A haka muka kasance har ranar zuwan baba ta zo na zamo cike da zumudi fiye da kullum a dalilin ranar ce kuma za ta zamo ranar dawowar Ummana.
Tun dare nake ta faman shirye-shiryen abincin saukar da nake shirya mata.
Gari na wayewa na gama kintsa komai na tsabtace wurin ta tsab, ko’ina sai kamshi kake ji yana tashi. Na yi wanka na zauna na tsala kwalliya cikin wata doguwar riga mai ruwan kasa, gaban rigar ya sha ado da wasu duwatsu masu daraja na yane kaina da gyalanta, sannan na dauko warawaran Yaya Almu na sanya a hannuna tare da wasu zobuna guda biyu da Yaya Junaidu ya ba ni kyautar cika shekara na farin gold na yi matukar yin kyau ga kwarjini na fito cikin wani sansanyan kamshi na iso wurin yaya Almu na samu wai lokaci ne zai yi wanka na ce mishi;
“To ni gaskiya zan bi Yaya Junaidu sai ka zo.”
Ya kalleni cikin murmushi ya ce, “Haba Rabi dan jiran da za ki yi mini na mintina da ba su fi talatin ba.
Na yi maza na ce mishi, ‘A’a ni kam ba zan iya ba.” Ya ce, “To shi kenan sai na zo.”
Da gudu na fito don gudun kar Yaya Junaidu ya tafi ya bar ni, ina shiga motar na zauna wacce take ledusc Jeep ce. Yaya Junaidu ya kallcni cikin murmushi ya ce kar dai ki ce mini doki ba zai barki jiran Mustapha ba?”
Na ce uh gaskiya ba zan iya ba ya yi dariya ya ce Adawiyya kenan, yau za ki ga Umma ai dole ki yi zumudi.
A Airport mun isa babu dadewa sai ga jirgi ya sauka ana bude kofar jirgin sai ga Ummana ta bayyana cikin kwalliyar da ta saba yi in har za ta tafi wani wuri, tare da Baba ko kuma za su dawo tare wato kwalliyar lafaya.
Suna fitowa daga cikin filin suka shige motar nima na shige gaba tare da Yaya Junaidu.
Tun ba mu gama gaisawa ba Baba ya kalleni cikin fara’a da murmushin da ke bayyanar da farın cikin shi ya ce, “Lalle na yarda har da zaman ki kusa da Ummanki yake kara maida ke yar kankanuwar yarinya, ‘uwata kin ga irin giriman da kika yi kuwa a dan tsakanin nan kin kara girma kin kara kyau kin kara hankali, domin gashi yau na ganki cikin suturar da ta kara miki kwarjini. “
Na ji dadin kalaman Baba cikin ladabi na ce mishi, “Ai na kara shekara baka nan Baba shi ya sa ba ka sani ba.” Ya ce na sani ban mance ba, ya ya ma za a yi in mance da ranar haihuwar uwata?
Sannan ma ai ga Ummanki tare da ni kin kuma sani ita ma ba za ta taba mancewa ba.” Na yi maza na ce haka ne Baba.
Na tanadar miki kyautar ki tana nan zan baki, na kuma san anan ma ba za ki rasa mai baki ba, tun da ga su Junaidu nan a gidan.” Na yi murmushi na ce kowa ya yi mini kyauta Baba.
Yaya Junaidu ya yankana mini cake din birthday ya kuma ba ni kyautar wadannan zobunan.” Na daga yan yatsuna na nuna mishi zobunan ya ce,
‘A’a lalle Junaidu ya burge ki.”
Na ce eh Baba shi kuwa Yaya Almu ya bani wadannan warawaran tare da kyautar dogayen riga ya kuma roken in maida su suturar da zan rinka yawaita amfani da Su.
Da sauri baba ya ce,”Ya yi daidai uwata, don kuwa nima ba akan son raina nake ganinki da Kananan kayan nan ba, barin ki dai kawai na yi don in gane yaushe ne za ki girma ki daina, don kan ki? To ga shi girman ya zo.”
Muna ta hirar mu da Baba ita kam Ummana Shiru ta yi, don dama in tana cikin mota da wuya kwarai ka ganta tana magana.
Muna isa gida Yaya Almu ya sa hannu ya budewa Umma kofar motar ta fito Cikin girmamawa ya ce mata, Sannu da zuwa Umma.
Ta kalle shi cikin nutsuwa a hankali ta bude baki ta tambaye shi,
“Lafiya na ganka a gida?” Ya sake shiga wata nutsuwar kafin ya ce mata,
“Rabi ce ta ki jirana sai na ji kasalar yin tafiyar babu ita don haka na ce bari in jira isowar ku kawai a gida.”
A falon Umma tana zaunc ana ta yi mata sannu da zuwa, ni kuwa ina kwance a jikinta ita ma sai shafani take yi, cikin fara’a tana fadin,
“Adawiyyata ta girma a bayana.”
Rannan kusan kwana aka yi ana hira a falon Umma wajen karfe goma ta dawo daga falon Baba ta zo ta same mu ni da su yaya Almu da sauran yan matan gidan muna zaman jiranta ta zo a yi hira.
Tana shigowa anti Basira ta sake ce mata, ‘Sannu da zuwa Umma, gaskiya daga yanzu in za ki yi tafiya sosai-sosai za ki rinka sallamar mu don in bakya nan bushewa yake yi gaba daya aka dauka eh Umma.
Umma ta yi murmushi ta ce, To ni ban da ku Basira kwana nawa ma za ku kara ai ina ganin ko zan sake yın wata tafiyar kuma zai zamo sai bayan bikin ku, don abin da Babanku ya gaya mini kenan zan tsaya in kula mishi da hidimar shirye-shiryen bakin ku.”
“Yan mata suna jin haka kunya ta kama su suka rinka mikewa suna sallama da Umma suna tafiya dakin su ni kuwa ina ganin sun gama fita na kara mimmikewa a jikin Umma cikin murna da farin ciki na ce mata, “Umma ba karamin farin ciki zan yi ba in aka sallami kartin yan matan nan suka kama hanya suka tafi gidan mazajen su.”
Umma ta yi dariya ta ce, “Ke kuwa Adawiyya me suka tsare miki haka?”
Na yi murmushi kawai na ce, “Uhum Umma kenan ke dai tun da sun riga sun kusa tafiya to mu bar zancen kawai ba zan kawo miki karar su.
Ba don kar su je suna cewa na hada ki da su, amma in ban da haka ai ba dadin su nake ji ba.”
Yaya Almu ya ja tsaki mai karfi, nuna jin takaicin a fili, ya kalleni ya ce mini, “In an salami kowa ya tafi an bar ki a gidan nan Rabi na roke ki arziki kar ki ci duniya da tsinke, ki rinka cinta da bakin allura.”
Yaya Junaidu da Umma suka kyalkyale da dariya, Umma ta ce mishi, “Ba dai fushi ka yi ba Babangida?”
Ya ce, “A’a Umma wai dai ta ji dadi ne sosai shi ne nake kara ba ta shawara.”
Ina kwance jikin Umma suna ta hirar su har dai barci ya daukeni na farka cikin dare sosai na samu duk kowa ya watse daga Yaya Almu sai Umma su biyun suke ta hirar su, alamar za su tashi na gyara kwanciya na juya ta daya gefen Umma ta kara mikewa sosai wai don in kara jin dadin barcina.
Sai wajen karfe hudun Asuba na ji tana yi mini gyara kwanciyar ki da kyau Adawiyya, ko ki tashi ki shiga daki ki kwanta, ni zani in yi alwala. Na ji muryar Yaya Almu yana
ccwa, “Ta gyara kwanciya Umma? Ai gwara ta tashi ta yi wa Junaidu girkin da ya ce sammako fa zai yi.”
Ina in haka na yi maza na watstsake don na riga na san da maganar tafiyar tashi na kuma riga na sabar mishi da yi mishi guzurin abin da zai rinka karyawa da shi a duk lokacin da zai yi tafiya.
Baba yana gama kwanakın shi guda biyu ya dauki Umma Karama suka yi tafiyar su, gida ya saura daga Ummana sai Umma Amarya.
Sati guda da tafiyar Baba Ummana ta bayar da umarnin yan mata su yi shiri za a kai su su je su yi gaisuwar sallama a cikin dangıi, alama dai kenan lalle biki ya matso.
Suna gama shiryawa suka zo suka yi sallama ta kawo kudi masu auki ta ba su ta ce su zuba a jakunkunan su, suka yi mata godiya suka tafi, ni kuwa sai na tashi na na nufi sashin ‘yan mata.
Ina kara duba fasalin sashin namu da irin gyare-gyaren da zan yi a cikin shi kafin in dawo zaman cikin shi na sosai da sosai, don ina son wurin suna fita nan zan dawo ko yanzu abin da ya sa ba na zama wurin sosai takura mini ne da su ke yi da yawan aiki ko aika komai za a yi in dai ina wurin to Adawiyya za su ce.
Adawiyya ban kawo abu kaza, Adawiyya ban abu kaza, Adawiyya dauko mini wannan, Adawiyya share nan, goge can, waya ce miki ki yi haka? Aikin su kenan shi ya sa nake gudu in bar musu wurin,, don haka suna fita zan shiga, don babu mai mini wannan takurar kuma na gama nazarın wurin na dawo na zauna ina rubuce-rubuce na tsare-tsaren abubuwan da zan gudanar, Yaya Almu ya shigo ya same ni.
“Aiken me yau kike yi haka Rabi? Kin kuwa san ban taba ganin ki kina rike da biro kina aikin makaranta ba?”
Na ce, “Ai ba aikin makaranta ba ne, ina tsare-tsaren yadda zan gudanar da al’amurana ne in kun tafi.”
Ya nemi wuri ya zauna cikin nutsuwa ya mika hannu a hankali ya karbi takardar ya zuba mata ido yana kallonta cikin nutsuwa tsawon lokaci kafin ya dago ido ya kalleni ya ce mini, “Wato ke dai Rabi ina jin kin yin karatu kawa kika yi yanzu ki duba ki ga abin da kika zauna kika tsara da yake wannan yin kan ki ne da a makaranta ne aka ce ku yi wani abu makamancin wannan dä kin ce ba ki gane ba.”
Ya miko mini takardar tare da cewar tsarin ya yi kyau.
“Saura kawai lokacin aiwatarwar, kuma jiya mun shiga makarantar ta ku ni da Zubairu sun manna sakamakon ku carryover ki biyu.”
Na yi maza na daure fuska na ce, ‘Ai na sani kawayena sun yi waya sun gaya mini.”
Ya ce, “Okey ai ban sani ba.”
Umma ta shigo ta zauna tana yi mishi magana alamar ta san da shigowar na shi da suka gama wannan magnar sai ya ce mata, “Ni zan iya yin tafiya ne yanzu Umma ko dole sai na jira yan matan sun dawo?”
Ya yi murmushi ta ce mishi, “Me ye gamin tafiyar ká da ta su?”
Ya ce, “Babu.”
Ta ce, “To ai sai ka yi ta ka kawai suma suna yin ta sun, ko da yake ban san in da kake son zuwa ba.”
Ya ce mata, “Katagun.”
Ina jin haka na yi maza na ce mishi, “Nima za ni.” Dan na san wurin dangin Umma za shi. Ya ce, “Me za ki je ki yi wo ki bari sai za a yi miki na ki auren kya je nima yanzu za ni yi musu sallama ne su yi mini ganin karshe ina saurayi daga yanzu kuma za su sake ganina ina matsayin mai iyali.”
Umma ta yi kamar ba ta jin abin da yake fadi ta hanyar kawar da kanta can gefe ni kuwa sai na shiga marairaice mishi ina cewa;
“Haba yaya Almu in na yi maka rakiya ai ba laifi ba ne, tun da dama ka saba zuwa da ni ba sai nima in yi maka rakiyar karshe kana saurayin ba.
Daga yanzu kuma ai zan rinka rakaka ne kana matsayin mai iyali.”
Ya yi maza ya ce, ‘A’a yanzu dai shirya yau mu je ki raka nin, amma ana ba ni iyali ai kuma na yi sallama da rakiyar ki kenan, iyakaci na ce za ta rinka raka ni nan da nan.”
Na ji wani abu ya dan mintsinen a zuciyata, har sai da ya bayyana a fuskata, na kasa boye bacin raina.
Shi kuwa yaya Almu tamfar bai gane hakan ba, sai cewa ya yi, “Ai ni in na yi aure Rabi matata zan ba ta matsayi mai karfi a rayuwata, komai zan yi da ita zan rinka yi”
Na ce, “Uh hakan yana da kyau.”
Na tashi na shige daki na yi kwanciyata.
Wajen karfe goma sha biyu ya shigo cikin shiri, kwalliyar doguwar rigar tazarce ya yi na yadin farin koil ya yi matukar yin kyau.
Ya ya yi sallama da Umma, sannan ya tambayeta ina Rabin take? Ta mishi ga ta can a cikin dakinta.
Ya dan daga murya ya ce, “To fito mu tafi mana Rabi”
Na ce mishi. ‘Ai na riga na fasa zuwa sai ka dawo ka gaishe su.”
Da sauri Umma ta ce, “Kar ki fara wannan maganar fito ku tafi sai da kika sashi ya bata lokaci yana jiranki shi ne za ki ce kin fasa? In da don tashi kadai ne ai da da wuri ya tafi ya dawwo yau ba, saboda kin cc za kin ba ne ya sa ya ce to bari ku je ku kwana don ki gaisa da mutane sosai.”
Na ce, “Uh, uh! Ya je kawai.”
Umma da Yaya Almu suka yi rarrashi har suka gaji na cc babu inda za ni har Umma ta tunzura ta shiga balbaleni da fadi abin da ba ta taba yi ba.
Ni kuwa sai na fashe mata da kuka ina cewa, “Ni Umma ni ban san abin da nake yi miki ba, kin fi son Yaya Almu a kaina, komai ya yi shi daidai ne a wurinki, dazu kina Jin shi yana ccwa daga ya yi auren shi shi kenan ya daina yin mu’amalla da ni, amma ba ki ce mishi komai ba, ba ki kwabe shi kan maganganun da yake ta fada ba, sai ni kawai don na ce na daina bin shi daga yau ba sai ya yi aure ya daina ba, shi ne za ki lullubeni da fadi?”
Yaya Almu ya ce, “To yi hakuri Rabi ai ban san zancen ba zai yi miki dadi ba, da ban gaya miki ba, sai in bar abin kawai a cikin zuciyata.”
Na yi maza na ce, “Kin ji shi ko Umma kin ji shi yana nan akan bakan shi na cewar in ya yi aure ya samu mata to ya daina mu’amalla da ‘yar uwar shi, kuma kin yi shiru ba za ki kwabe shi ba, ai in ya rabu da ni saboda ita kema zai rabu da kc don haka ba zani ba ya je ta fara yi mishi rakiyar daga, yau.”
Ya ce, “A’a yau kam ai ba a nuna mini ita ba tukunna.”
Umma ta daure fuska ta ce, “Kai Babangida daina wadannan maganganu naka marasa dadin ji.” Ya ce to Umma a yi hakuri.
Duk da hakurin da ya yi ta bani bayan fitar Umma daga falon ba mu bar gida ha sai wajen karfe ukun yamma a dalilin tuburcwar da na yi na ce babu inda za ni.