Skip to content
Part 11 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Muna tafiya a motar Yaya Almu hirar auren shi da matar shi yake yi mini ni da da kike kallona zan so matata Rabi, zan so mu’ammala mai dadi tare da ita, zan so a ce muna da cikakkiyar fahimtar juna ni da ita, ba zan yarda wasu can su shiga cikin mu’amallar mu ba.

Zuciya ta raya mini wato ni ce wasu can, ya ci gaba da cewar;

‘Shi aure da kike ganin shi karfin shi yafi Karfin komai, kusancin shi kuma yafi karfin kowanne irin kusnaci mu’amallar da ke tsakaninka da matarka mu’amalla ce ta kut-da-kut ta rufin asiri ta taimakekeniya da kuma nunawa juna kauna, don haka ai ina ganin bai kamata ka bar wasu su shiga cikin lamarin ka har su zo suna kawo muku matsala ba.”

Na ce, “Uh haka ne.” Na tsuke fuska ta don dani in samu ya yi shiru cikin raina kuwa sai tunani nake yi.

Ashe dai shi ma yaya Almu irin sullutayen mazan nan zai zama wadanda daga an yi aure sai kuma su mance da iyaye da ‘yanuwa sai a koma gindin mata a tare sai kuma yanda ta yi.

Ina cikin tunanin nawa ya katse mini shi ta hanyar cewa, “Ni fa na dade ina tunanin hikimomin da kc cikin aure Rabi, ni fa ina ganin duk abin da ka yi wa matarka ba ka fadi ba, to wake maka irin abin da take maka? Wurinta fa kake sauke dukkan lalurornka, to balle kuma a ce ka yi sa’a ta haifar maka da, caf ai ni kam sai in bar komai in zauna in yi ta tarairayarta ina tayata son abin da take so, in tayata kin wanda ba ta so, in ta kalle farin abu ta ce mishi baki ne in yi maza in ce mata kirin kuwa, don dai kar ranta ya baci.”

Na kalli Yaya Almu na ce mishi, to amma haka aka ce ayi zaman aure ya yi máza ya ce Yaya aka ce a yi? Kin sanni ban sani ba, tun da ban taba yi ba.

Ba tare dana gane abin da yake nufi da fadin hakan ba sai na ce mishi ina ce cewa aka yi, ku kare kan ku da iyalanku daga shiga wata irin wuta wacce makamashinta yake mutane ne da duwarwatsu.

Ya yi maza ya ce haka ne Rabi na ce to amma a yanda kake cewa za ka yin nan za ká ya yin wannan aikin? A maida fari baki, ka ce mishi bakikkirin? Kenan in aka maida gaskiya karya za ka yarda? Gaskiya ni ba haka na ga Iyayen mu suna auren su ba.”

Ina fadin haka na soma kuka ina fadin, “Kenan zan rasa ka zan rasaka Yaya Almu, na gane matarka za ta kwace mini kai, dama kuma ba ni da kowa sai kai. Kai ne dan’uwana da uban mu ya haife mu tare muka kuma taso a daki daya. Kai ne nafi shakuwa da kai, kai na fi so kai ne nake damuwa da duk wani al’amarinka tun inan ganin abubuwan da kake yi mini ‘yan ubanci ne da takura a dalilin ba ka son ganina a cikin gida har sai na fahimci cewar kana yi mini abubuwan da kake yin ne don kana nufin gyara a kaina, to amma yanzu wadannan kalaman naka me suke nufi?”

Ya yi maza ya kauce hanya ya nemi wuri yaa yi parking a cikin jeji ya fita ya je ya bude but idin motar ya dauko jakaar ruwa ya zo ya bude wurin zamana ya miko mini jarkar.

“Bar kuka Rabi ki wanke fuskar ki kar mu isa su ga hawaye a idon ki, ai tun da na gane kin damu da ni haka ba zan bari ta raba mu gaba daya ba, zan rinka yi miki waya a kai a kai duk sati biyu zan yi kokarin in kiraki.” Na sa hannu na karbi jarkar ina wanke fuskata cikin zuciyata kuwa fadi nake yi, lalle wannan ya gama tafiya ba zan sake kuka a kan shi ko.damuwa da shi ba, in kuma ya kira n1 a waya bayan sati biyu da kiran farko to ba zan taba dauka ba, gara mu yanke kawai gaba daya.

A Katagun a gidansu Umma karba sosai aka yi mana dama yaya Almu ba bako ba ne a gidan yama fini sanin ‘yan’uwan Umma da mu’amalla da su, don haka ban sake komawa ta kan shi ba, kowa harkar gaban shi yake yi, ko wani wuri za ni ba na neman shi sai kawai in kira yaran gidan su rakani, shi ne ma in zai je wani wuri yake aikowa in zo mu tafi tare, sai in ce mishi ya je kawai ni na riga na je.

Wani abin takaicin dai kawai da ya kara kular da ni a tafiyar shi ne yanda duk inda na je sai a rinka nuna ni a matsayin wai ni ma a amaryar ce, har suna tambayata to in ban da sakarci irin na ki me ya hanan ki biyo sauran yanmatan ku yi tahowarku tare gwanin sha’awa sai ki wani coge sai Lamido ya kawo ki don ba ki da kuny? Na yi ta kokarin yi musu bayani ni fa rako Yaya Almu na yi ya zo ne ya yi muku sallama armma ni ai ba yanzu zai a yi mini aure ba Umma ta ce bikina ni kadai za a yi ba za a hadani da wadannan kartin ba, wajen shekara hurhuda fa suka ba ni sai a ce mini ke tafi can ko shekara nawa-nawa suka baki ai kin kamo su har ma kin dara su tun da duk cikin su waccce ba ki kereta tsayi ba?

Na ce to shi kenan ku tambayi Yaya Almu kan wannan dalilin nema har na nemi Yaya Almu don ya bayar da shida kan cewar babu ni cikin wadanda za a aurar din ya ce musu eh ita yanzu ita ce za a bar wa rikon gidan, in an hada  har da ita ai zai zama babu wata mai kula da sashin ‘yan matan kuma ba ta karasa karatun ta ba, ga shi tun da tana faduwa jarrabawa to ba bana nema za ta fita ba, sai badi za ta gama diploma, sannan ta yi H.N.D. kamar na su Aina’u kenan don haka ina ganin auren Rabi kam da saura tukunna.

Gaba daya suka shagala kan cewar kai amma kuwa da abin bai yi dadi a irin wannan girma da ta yia ce kuma sai an kara wasu shekaru nan gaba? Ya yi murmushi ya ce yarinya ce fa kwanakin baya ne ai ta cika shekara goma sha tara, suka ce au to in ban da nan wurin ku ina ake yin haka ka bar ‘ya tana ta yi maka wanki a gida? Ai mu nan shekaru sha biyu, sha uku in ta yi tsauri sha hudu sai a gabatar da yarinya.

Kwana biyu muka yi muka kamo hanyar dawowa a wannan lokacin ba wani dasawa muke yi da Yaya Almu ba, don sau uku yana subutar baki yana kirana da sunan Aina’u sai ya kiranin sai ya ce mini wai sorry please na riga na sanya ta ne a raina a dalilin ke ma ita kika zaban mini sai na ke ganin to watakila dai ita din za a ba ni bari in koyi sonta tun kafin a ba ni itan, doon komai ya tafi mana daidai, ko kuwa? Kin san ni ba zan taba yin musu da Baba kan wacce zai ba ni ba, to balle kuma in yi sa’a a ce ita din na samu ga ta mai kyau, ga ta gwanar iya kwalliya, ga 1ya taku.

Na yi maza na ce a’a nan kuma daya. Ya ce au to ashe kwalliya kawai ta iya ban da takun tafiya? Uh to amma ai na samu mace gwanar kwalliya ai dadi ne da ita za ta fidda ka kunya duk inda kuka shiga ni ko ba ta iya girki ba babu komai zan nemo mai yi mata girkin, ta yi kwalliya kawai ta yi zamanta in na dawo gida ta yi ta tarairayata tana ina taka saka da ni, tana mini tausa tana mini abin nan. Ai ni kuma shi kenan ta tafi da komai nawa ta. gama da ni ta tafi da ruhin rayuwata. Na tsuke fuska cikin jin takaici na ce,  “Kai Yaya Almu dai wani abu ya same shi tir!” Na ja tsaki.

Ya dan waiwayo ya kallen ya ce, “Ba dai ni kike wa tsaki ba ko?” Na yi shiru ban ce mishi komai ba.

‘Rashin kunyar taki har ta kai ga yi mini tsaki?”

Shiru na yi ban kula shi ba, da na ji zai yi magana sai na katse.shi na ce mishi, to wai ni yaya Almu me ya sa duk inda muka tsugunna muna magana sai ka gaya musu faduwa jarrabawa nake yi? Ya ce ban san ba kya so a sani ba ba zan sake gayawa kowa ba, tun da ma ai kin san in na yi aure zan dauki matata in yi tafiya ta da ita, ba zama ki rinka ganina a kai a kai ba, balle in je ina fadin abin da ba kya so a sani.

Tun da na gane duk wata magana da za a yi shi sai ya ciko ta da maganar auren shi ko da farkonta ba ta auren na shi ba ne, sai kawai na kame bakina na daina yin maganar da shi har muka isa gida ni da shi ba mai magana da wani.

Tun daga rannan kuma na daina shiga harkar shi, ko abinci na yi ba na zuba mishi. Yana zaune a falon Umma hira suke yi tare na shigo na same su na ce mishi sannu yaya Almu, ya ce yauwa Aina’u. Umma ta kwashe da dariya ta ce, ‘Adawiyya ce yau ta zamc maka Aina’u Babangida?” Ya ce au yi hakuri Rabi. Ya ci gaba da zancen shi a zuciyata na ce ba laifinka ba ne laifina ne da na gaisheka.

Ban sake tsinkewa da lamarin Yaya Almu ba na kara tsoraa da shi sa a ranar da Umma ta aike ni wurin shi wai in kai mishi sinasir da miya, wanda ni na yi mata ta dibar mishi. Samun shi na yi a kwance a dakin shi ya yi rigingine kan katifar shi yana kallon dama wasu baitoci yake rerowa cikin labarci masu dadin ji, duk da ban san abin da suke nufi ba, don in ka debe gaisuwa ban san komai ba cikin wannan harshen mai daraja cikin kowane karshen baiti daya kai sai in ji shi yana fadin Ainau.

A zatona haka amshin wakar yake. Ina tsugunne ina sauraron shi ina jiran ya gama in gaya mishi abin da ta ce in gaya mishi, sal da ya gaman sai ya kalleni ya yi murmushi ya ce, “Wannan wakar wani mawaki ne na lokacin jahiliya’ da ya ta6a yin nasara aka rubuta wakar shi da ruwan zinare a kasuwar mawaka, shi ne ya zauna ya yi wa masoyiyar shi wakar nan da kika ji ina yi ya siffaintata da kyau, ya bayyana ta a matsayin mai cikakkiyar sura, da darararan idanuwa.

Ya dan kalle ni ya ce, ‘Ashe ke kanwata ce bai kamata in tsaya ina gaya miki siffofinta ba, ke dai kawai.”

Ya sake yi mini wani murmushin, sannan ya ce, “Ta yi mini kama ne da antin ki Aina’u shi ya sa na cire sunan budurwar ta shi na sa na tawa budurwar don tafi tashin cancantar wadancan baitocin, ko ya ya kika gani?”

Na yi kamar in ce mishi ai da kirkiro baitocin ka yi da taka hikimar sai na kasa saboda har yanzu na kasa daina ganin girman shi, illa dai kawai tausayinsa da kan kamani in ce oho mutum har mutum kamar yaya Almu dai wai tun ba a fara zama ba ya zama ta ce, to n an fara zaman ya ya zai zama? Oho. Ina cikin wannan tunanin ne ban kai karshe ba ya katse i ta hanyar cewa ina son aure Rabi, ina so in ga mace a kusa da ni mai kyau a ce ita din kuma ta wace. Ya dan shinfida hannu kan faffadan kirjin shi yana shafawa tare da yin ajiyar zuciya, sannan ya ce “Kin ji dadi in na sanmu hakan? Kin sanni ina son mace.”

Ya dan lumshe ido a hankali ya sake bude su  cikin nutsuwa ya sake kallona ya ce, “Ke ‘yaruwata ce ba zan iya boye miki ba Rabi ina son aba ni mata zaman nawa haka ya ishe ni, wani lokaci na kan kasa barci in bukatar hakan ya taso mini, sai dai babu yanda zan yi dole in yi hakuri shi ya sa nake gaya miki tun da ke kina hira da Umma ko za ki rokar mini ita ne ta yi wa Baba magana ya taimake ni bana kar ya bar ni in wuce damunar nan mai zuwa ina tuzuru, ya yi mini aure, zaman nawa haka ya isa’yan watanni kadan masu zuwa ne fa zan cika shekaru talatin a duniya, to ko ban fada ba ai ya kamata a ce ita Umma ta san na girma.

Za ki taimaka ki yi mata magana?”

Na 6ata fuşka na ce, ‘Ai ka fini kusa da ita.”

Ya ce to ai kunya nake ji ko ke din ma in za ki yi mata maganar ai za ki yi ne a matsayin ki na kanwata kina tausayin zamana haka, tun da kin san zaman nawa a haka ya ishe ni ba cewa za ki yi ni na aiko ki ba, kin ga nima da na gane kin isa aure kinmfara bukatar wami mutum kusa da ke sai in yi maza in ce a gabatar da ke.”

Yaya Junaidu ya leko dakin ya gan mu, “Ya ya na ga Adawiyya tana durkushe kamar mai neman gafara?

Ya dago ido ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, Wai sinasir ta kawo mini, ni kuma ina da abin da nake bukata fiye da wannan shi ne nake rokonta ta  taimaka ta sa a yi mini aure.”

Yaya Junaidu ya galla mishi harara tare da jan tsaki ya ce mini, Ke Adawiyyah tashi ki yi tafiyarki in ya matsu shi zai san yanda zai yi tun da ai ba fin shi bakin magana kika yi ba.”

Ina jin haka na yi maza na mike dama zaman nawa a wurin ya ishe ni, don ba jin dadin hirar nake ji ba.

Ina shiga falon Umma na kalleta na ce mata, “Daga yau Umma kar ki sake aike na wurin Yaya Almu.”

A hankali ta daga ido ta kallen ta ce, “Me ya yi zafi haka ke da dan’uwanki?” Na ce kai ina ganin kamar zan yafe shi kin san wai zuwa na yi na same shi yana yi wa Anti Aina’u wakar larabci? Wai har yana kwacewa Baralabe baitocin shi yana cewa wai da ita suka da ce?”

Maimakon Umma ta taya ni jin takaici sai kawai na ga ta kyalkyale da dariya mai karfi har tana tambayarta wai me kika y1 wa Baangida ne yake miki irin wannan sakarcin?

Na ce me na mishi Umma in ban da kawai idona shi da ya rufe? Kin ma san wai dame, yake kwatanta ta? Ta ce, ‘A’a.”

Na taba baki na ce to wai da cikkakiyar sura da daradaran idanuwa.

Tana da su Umma?” Na zuba mata ido ina kallonta ta sake sakin wani lallausan murmushin kafin ta ce, To tana da su din kenan tun da ya gani?” Na ce, “Haba Umma ni da ke muke magana kuma dukkan mu mun san gaskiya Aina’u fa ba wata mai cikakkiyar sura ba ce. Sannan kuma ko Anti Basira ai sun fita manyan  idanuwan.””

Na lura maganar da nake yin dariya take Sanya Umma sai na mike zan shiga cikin kicin in debo kunun aya in sha na ce gaya mini Umma sun fini kyau ne ya kidime har a kanta? Ta yi maza ta ce, “Wane su.” Ina jin ta fadi haka na yi maza na dawo kusa da ita na zauna. Ta ce, ‘Ai ko baiwar tsayin da aka yi miki ya ishe ki Adawiyya. A ce dai ba ki da komai sai tsayin nan na ki ya isa ki gamsu. ki yi godiya kan ni’imar da aka yi miki, balle ga ki mai daradaran idanuwa farare tas, gaki da dogon gashi mai matukar kyau, gaki da cikkakkiyar sura. Ai ni inda Lamido zai yi karfin halin yin wannan shin kunyar a gabana to da kuwa na yi karfin karyata shi in ce mishi kul daina irin wadannan kalaman naka na karya da kake yi kai ma ka san ba Aina’u ce mai wannan siffar ba.”

<< Wace Ce Ni? 10Wace Ce Ni? 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×