Skip to content
Part 12 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Kalaman Umma suka sanya ni jin sanyi cikin raina na ce, ‘Umma.

Ta dago ido tana kallona na ce da sannu zan kawo miki suruki wanda zai so ni fiye da son da Yaya Almu yake yi wa Aina’u, don in ba hakan aka yi ba zan rinka tunanin ta kware ni, don ta riga ta kwace mini yaya Almu ta raba ni da dan’uwana, bai tunanin kowa a yanzu sai ita.”

Hawaye suka zubo mini sharr! Nan take kuma  na kasa shanye kukan, saboda nauyin da zuciyata ta yi, a dalilin tsananin kuncin da ta samu kanta a ciki.

Kuka na yi ta yi, Umma tana ba ni hakuri, ina jaddada mata cewar babu dama wata a ce ta shiga tsakanina da dan’uwana hakan ba zai yiwu ba.

Ba mu tashi daga wurin ba sai ga shi ya shigo.

“Aina’u da sauran sinasir din nan ne?”

Umma ta yi banza ta bata fuska ta ce kai Babangida shiga hankalinka kar in sake jin ka kira mini Adawiyyata da sunan da ba nan ta ba, ranka zai baci.”

Ya nemi wuri ya zauna Cikin nutsuwa ya ce, yi hakuri Umma subutar ba ki na yi.” Ta sake cewa, “Kar ka sake don ba zan lamunci ganin Adawiyya cikin bacin rai ba, sannan bacin ran ma a ce daga gareka ne.”

Ya ce, ‘A ba ta hakuri kuma in ta yarda ta shirya mu je in kai ta ta shah iska, don bacin ran da na sanyata.”

Na ce, “Bab inda za ni.” Umma ta ce tun da ta ce ba za ta ba, to ba za ta ba.

Bayan fitar shi ne na kalle ta na ce mata share shi zan yi ta gyada kai nuna alamar yarda.

Tuni na yi watsi da yaya Almu da duk wata harka tashi, ita ma anti A ina’un na daina kulata don sai na rinka ganin tanfar wani gani-gani take yi mini.

Komai zan yi sai in je wurin Yaya Junaidu in ma unguwa za ni can wurin shi na ke zuwa ya kai ni a kowannc lokaci kuma in muna hira in dai na kawo mishi zancen auren su ya kan gaya mini shi zai aure ne kawai don yin shi din ibada ne, shi ya sa yake addu’ar idan baba ya tashi ya zabar mishi mace to ya zabar mishi mai hankali da nutsuwa, wacce za su yi zaman fahimta shi da ita, saboda shi a fahimtar da ya yi wa auren da kuma lura da al’amuran iyayen mu ya gane babu komai a cikin shi, illa hakuri da juriya, shi ana shi fahimtar in ma har da akwai wani Jin dadi to bai wuce na kare mutunci ba, don haka shi kyan mace da iya kwalliyarta yana dashe shi, to amma ba shi ne abin da yafi bukata a wurinta ba.

zai fi son ta zama mai hakuri da juriya,, saboda ta ya rungumar al’amuran shi da na yan uwan shi in ya so sai kyau da kwalliyar su biyo baya.

Cikin Zuciyata na ce waiyo ni Ina ma dai yaya Junaidu ne yake da matsayin yaya Almu a wurina, da ban samu matsala ko shiga barazanar rasa dan’uwana ba, amma shi tun ba a yi auren ba har ya fara yi mini kashedin babu mai shiga tsakanin shi da matar shi, karewa ma har ya fara mancewa da sunana.

Na kalle shi Cikin nutsuwa na ce mishi “Amma kuna hira da yaya Almu.

Yaya Junaidu kana gaya mishi irin wadannan abubuwan?”

Ya dan yi ajiyar zuciya a hankali, sannan ya ce  mini, “Ba na iya yin hirar auren da Mustapha a yan kwanakin nan saboda zukata sun yi nauyi

Adawiyyah, duk lokacin da na yi tunanin dauko hirar sai in ga to me za mu tattauna? Farin cikin rabuwa da 1yayenmu ko kuwa tausayin zaman mu da su ya zo karshe?

Zaman da muka yi da su mai dadi? Zaman da muka yi da su suna dawainiya da mu suna kokarin ganin mun zama mutanen kirki?

Kullum burin su bai wucc son ganin sun kyautata mana ba, ni kam tausayi kan kama ni in na dubi shekarun Baba na ga wai har yanzu bai daina dawainiya da mu ba, ba ni kuma da wani abin da zan yi mishi wanda shi bai taba yi mini ba, komai za ka yi tunanin yi mishi to shi din ya yi maka, wanda yafi shi kafin ka yi, don haka ni ko kadan ba na zumudin auren ba na kuma kin yin shi, ni dai gani nan ne kawai ina dai addu’ar samun dacewa ne kawai.”

A wannan dan tsakanin sai na kara son yaya Junaidu na kara girmama shi, na kara ganin darajar shi saboda na gane shi din babu abin da yake so da kauna irin iyayen shi, musamman ma kuma Baba.

Kullum na kan samu Yaya Junaidu a waje ko a falon Ummana mu yi hira sai dai ban zuwa dakin su na daina ya yi, ya yi in gaya mishi dalilin hakan na ki, saboda na riga na kudurawa zuciyata ba zan taba yi wa wani hirar kalaman da yaya Almu ya gaya mini ba, akan auren shi da matar shi ko da kuwa Umma ce, wadanda ya yi a gabanta sun isa su zama shaida in ma wani abu ya taso a tsakanina da shi a can gaba.

Ita kuwa Umma hidimarta kawai take yi na shirin auren ‘ya’yanta maza da mata, dama kuma haka ne a duk lokacin da za a yi hidima irin wannan, ita mai tsayuwa kan komai don haka tuni ta yi nisa da shirye-shiryenta a yanzu jiran isowar Baba kawai take yi, ta ji lokacin da zai sanya ranar auren.

Ina zaune muna hira da ita Yaya Junaidu ya shigo ya same ta cikin nutsuwa ya ce mata, Wurinki na zo Umma.”

Bayan sun gama gaisawa ta ce mishi, “To Junaidu ke Adawiyya tashi ki ba mu wuri.”

Ya ce, ‘A’a Umma ta yi zamanta kawai.”

Sabanin yaya Almu da ya fito mini dá wani sabon wulakanci na in ya zo wurin Umma zai mata magana sai ya ce mata wai sirri za mu yi Umma, Rabi ta ba mu wuri, ita kuma sai ta ce wai in fita takaici ya kama ni in ce in dai haka ‘yan’uwan suke zama in za su yi aure to ba za a rinka zumud n auren na su ba.

Umma ta ce to ina jin ka Junaidu ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “In har baba ba zai yi fushi ba to ki rokar mana shi ya ba mu izinin yi wa matan mu kayan aure, maimakon yadda ya saba yi in zai yi irin wannan hidimar ya yi wa mata kayan daki, ya kuma yi wa  maza kayan aure, matan su ba wai mun girma ba ne, Umma amma mun duba ne muka ga mu din dukkan mu ma’aikata ne wannan ra’ayin na mu ne dukkan mu don Kabiru ne ya fara kawo shawarar don haka da yawun su dukkan su na zo ki rokar mana shi ki kuma ba shi hakuri don kar ya dauka hakan da wani tunani.

Umma ta ce to ban san abin da zai ce ba, tun da auren nan ba duk zai bayar a cikin gidan nan ba, ya ce haka ne mun sani, amma duk da haka nan na Cikin gidan muna rokon a yi mana wannan alfarmar ta ce to bari ya zo mu ji, yau ai bai fi kwana goma ba watan zai kare. Ya ce haka ne.

Ya dan zauna ya yi hira kafin ya tashi ya fita. Na kalli Umma na ce mata, “Shi kam yana son Baba.”

Ta ce mini, dukkan su ai shi Alhaji yana da wata baiwa bai taba rike’ mutumin da bai son shi ba.”

Na ce, ‘Ai Baba dole a so shi.”

Umma ta yi murmushi, “Wannan fadi ki kara Adawiyyah Alhaji mutum ne.”

Ban fara sanin auren zumudin shi sosai ake yi ba, sai da na ga irin shirye-shiryen ‘yan matan da kuma yadda kullum sai an kwashe su an kai su wurin gyaran jiki kuma wai wurin Ummana ake zuwa karbar kudin gyaran, sannan ko nawa aka zo  aka ce mata sai kawai in ga ta zaro kudi ta bayar na kalleta na ce, “Umma mene nc haka, ya ya kamar a Kasa kike debo kudi? Komai suka ce sai ki ce musu ga shi”

Ta yi murmushi ta ce, ‘Aure fa za su yi kin kuwa san menc ne auren? Ai dole amarya ta gyara jiki ta yi kyau ta burge angonta.” Na ce to ni fa Umma? Ta ce ai ke ba yanzu za a yi auren ki ba, in na ki auren ya zo ni da kaina zan gyara ki ba sai na tura ki kin je wani wuri ba, sanin da na yi Umma gwanar gyaran jiki ce, don wani lokaci ta kan yi ini ina kuma ganinta tana yawan yi wa kanta, musamman a ce ga Baba nan zuwa ya sa na yarda da maganar ta.

Washe gari Juma’a babu zato babu tsammani don ba ranar zuwan Baba ba ne, ko dama karshen wata ne, balle ma watan sauran kwana takwas ya kare.

Ana cikin aikace-aikacen gida ni kam ma a kwance nake yayin da Umma take jan carbinta a inda ta idar da sallar Walaha, sai kawai muka ji gida ya kaure da hayanıyar oyoyo mai karfi ga kuma dirar motoci, suna ta shigowa gida.

Da sauri na fito falo ina tambayar Umma mene ne? Sai ta yi maza ta shafa fatiha ta ce mini.

“Alhaji ya iso.”

Da gudu na fita tuni har jama’a sun fara cika gidan mu. Yaya Junaidu kuwa yana ta kokarin  bubbude mishi wuraren da yake amfani da su a zuciyata na ce an yi saa dama kullum wurin a tsabtace yake.

Akan dole na dawo sashin Ummana ba tare da gaishe shi ba, saboda mutane ina shigowa na samu yaya Almu yana tambayar Umma abin da za a fitar musu tana gaya mishi na sake fita, don na daina zama inda yaya Almu yake, na je na gaida Umma Karama da suka iso tare, sannan na shiga kicin na samu Umma Karama da ta riga Umma shiga kicin, don fara shirye-shiryen aikin da za su yi na kwatsam da ya same su, su Baba Talatu ma duk sun hallaro aka kama aiki gadan-gadan ita ma Umma ta iso suna shawara ita da Umma Amarya kan abin da za su yi.

Ina ganin abincin rana za mu shirya don Babangida ya fita da abin da za su karya da shi ya kuma ce zai isa don haka ba ma bukatar saurin mai yawa.

Umma Amarya ta ce, To haka ne bari in koma daki don ban yi sallar Wahala ba.”

Umma ta ce mata to.

Umma da su Baba Maigyada suna shirin abin da za su girka ni kuwa na ja gefe na shiga shiryawa baba miyoyi kala daban-daban tare da abin sha.

Miyar koda na soma shirya mishi. Ga abubuwan da na yi amfani da su.

Koda

Albasa

Butter

Flour kadan

Maggc 2

Ganyen Pcrsley

Kayan kamshi

Na yanka kodar kananan yanka na soyata tare da albasa cikin butter na zuba flour tare da maggi na dan gauraya kafin na zuba mishi ruwan tafashe na rufe ya yi ta tafasa sai da ya yi laushi sannan na zuba ganyen persley da kayan kamshi na rufe ya yi ta tafasa yana nuna har sai da na gamsu da nunar shi nan sauke na kuma dafa farar shinkafar da zai ci da shi.

Daga nan kuma sai na yi mishi Miyar Hanta Da Tumatur ita kuma na yi amfani da:

Hanta.               Kayan kamshi

Flour.                 Nikakken bawon lemon tsami

Maggi.               Tumatur manya

Albasa.              Mangyada

Butter

Na yi wa, hantar yankan shan kwabo guda goma sha biyu suka zamo da kadan suka dara fadin gongonin madara. Na hada kayan kamshi da maggi da bawon lemon tsami da flour na gauraya sannan na barbade hantar nan da shi gaba daya, na yanka albasa ita ma shan kwabo na yi guda shida na soyata cikin butter ta dan fara laushi na yanka tumatir shi ma shan kwabo na dan soya kadan duka  na tsame su na ajiye, sannan na dauko hantar nan da na rige na bade da hadadden garin fulawa na soya shi ya soyu da kyau sai in sa round tumatir kafin in dora faifin hanta sannan in shinfida faifan albasa sai in dora wani faifan hanta a kai sai in kawo na tumatir. A haka har na gama shirya su suka yi matukar yin kyau sai da na gama shirya wannan duka na kammala su wuri daya.

Sannan na yi maza na shirya mishi juice cikin sauri in da na yi amfani da lemon zaki, manya sosai guda hudu na tsami guda daya, abarba rabi, matse ruwan lemon na yi duka da na abarbar na hada su wuri daya ban wani tsaya kara suga ba, saboda an yi dace da lemon da abarbar dukkan su masu zaki ne sosai, sannan shi Baba ma ba ma’abocin shan suga ba ne.

Da kaina na je na kai mishi na yi sa’a sun hallara wurin cin abincin tare da mutane da yawa, amma ba su fara ci ba, na je na ajiye kusa da shi, na kuma bude mishi ya gani ya zuba ido yana kallo cikin sha’awa na dan kara matsawa kusa da shi na yi mishi rada a kunne na ce mishi,

“Baba wannan ni na girka maka da kaina.”

Ya yi murmushi ya ce, To zauna ki zuba mini Uwata.” Yana fadin haka na fara zuba mishi shinkafa da miyar Kazar na ajiye mishi, shi kuwa sai ya kalli jama’ar da ke wurin ya ce musu, A fara Cin abinci jama’a ni yau girkin uwa ta zan ci.”

Suna jin haka suka fara murmushi suna cafko naman kajin da aka kawo, shi kuwa Baba ya sunkuya ya ci shinkafar nan yana ci yana gaya mini dadinta, yana kuma daga ido yana hango hantar nan yana gaya mini.

“To ai na kosa ki ba ni wannan Mamana.

Na yi maza na jawo na fara yanyanka mishi ina murmushin jin dadi.

“Amma kin iya girki haka uwata me ya sa tuntuni ba ki rinka yi mini ba?

Na ce mishi, ‘Ka yi hakuri Baba daga yanzu kullum ka zo zan rinka yi maka girki.”

Ya gama shan ruwan lemon ya ce maza a sake yi mini wani saboda wannan zakin shi ya yi mini daidai. Na ce mishi to.

Na shigo dakin Umma ina ta tsalle na murna, ina gaya inata abincina Baba ya ci sai da na gama tsallen nawa, da na juya na ga yaya Almu a zaune, don haka na yi maza na tsuke fuskata na wuce zan shiga daki ta ce ina sauran da kika rage? Saboda na san in na kawo mata tare Za su ci, na ce mata na kai wa Umma Amarya.

Ina fadin hakan kuma na je na kwashe na kaiwa Umma Amarya.

Na zauna na-yanyanka mata tana ci muna yin hira, tana yi mini nasiha akan muhimmancin hakuri da mutanen da zama ya hada ku tare da su.

ita mace da kike gan1 ita ce jagora ta duk wani al’amari, a gidan mijinta in ta zama ta kirki sai gaba daya gidan ya zama haka, in kuwa ta lalace to gidan ne yake lalacewa, domin namiji shi kadai bai iya wadatarwa. Na ce mata to Umma.

Da yamma na sake komawa kicin na shiryawa Baba miyar kuka da naman kaza, sai da ta yi ta nuna ta farfashe sannan na tsame kasusuwan na burga miyar.

Tuwon dawa na yi mishi, saboda na san tuwon da Umma ke yi mishi kenan idan tana son burge shi.

Da daddaren ma nina kai mishi tuwon ya sake kallon ya ce mini.

To wai ni uwata kin iya abinci haka me ya sa ba ki rinka yi mini ba. Ni Junaidu ya taba ba ni labarin iya girkinki, anmma ban taba dauka ya kai haka ba.”

Na ce. ‘Ai yanzu na ce kullum zan rinka yi maka Baba.”

Ya kalleni a hankali cikin nutsuwa ya ce mini, To na kwana nawa za ki yi mini?”

Da daddare ne bayan sallar Isha’i aka kira mu gaba daya muka hallara a dakin Baba tuni kuwa su Umma sun shiga sun hallara, ganin su Baba Malle da na yi da Baba Maishanu ya kara tabbatar mini da cewar lalle akwai wani muhimmin abin da ya kawo Baba gida.

Gaba daya an taru an zauna a kasa har su Umma a kasan suke zaune. Can gefe sai yayyan Baba guda biyu tare da Baba da abokan shi ne akan kujera. Nima na raba na tafi sai da na je kusa da  Ummana na makure wurin ya yi tsif tanfar ba mutane a ciki kowa ka gani a nutse yake kai a sunkuye cikin nutsuwa.

“Bude mana zaman da addu’a.”

Maganar da Baba ya yi kenan yana Kallon Baba Mai shanu.

Nan da nan kuma Baba Mai shanu ya fara karanto addu’o’i masu matukar karfi yana gamawa Baba ya soma yn magana cikin nutsuwa.

Tun shekaru kusan uku ko hudu da suka wuce ne ya kamata a ce na tara mutane an yi wannan zaman saboda tun a wancan lokacin ku din nan da kuke zaune anan wurin a gabana duk kun isa auren in banda mutum daya. Sha’awa ia tason in hada ku gaba daya ban bar kowa a baya ba shi ne dalilin da ya sa na yi ta jan wannan lokacin bar aka kawo yanzu ina fata wannan rikewa da na yi muku ba ku dauketa a matsayin takura ko rashin adalci ba?”

Gaba daya su yaya Junaidu suka kara  sunkuyar da kawunan su kasa, don mafi karfin maganar tashi Su yake fuskanta. Sai ya ci gaba da cewa;

‘A yau, na gaiyato yan uwana ne da aminaina, kamar yanda na sabab yi kullum a irin wannan lokacin kan al’amari irin wannan, don su taya ni shaidawa da abin da na yi niyya kan ya’yana, saboda halin rayuwa, ko ban kai lokacin da na anbatan ba su tsaya wajen ganin sun cika mini burin da na yi.

Mun yi irin wadannan bure-buren a baya mun kuma yi dace da samun ikon cika su, to a yau ma za mu sake sanya wani lokacin don cika wani burin muna fata mu sake samun damar cikawar in kuma hakan bai samu ba to ina fata wani cikin ‘yan’uwana ko abokaina ya tsaya wajen ganin an cika mini shi.”

Baba Malle ya yi addu’ar Baba ya samu damar cika burin na shi, gaba daya aka amsa da amin, amin.

Da Baba ya sake gyara zama sai ya nisa ya ce, “Zuwa na yi a yau don in shaida muku cewar na sanya ranar bikinku ta zamo ranar 7 ga sabon wata mai kamawa shi ya sa ban iya jira sai karshen wata in zo ba, don bai dace in dibawa bikin wa’adin  

<< Wace Ce Ni? 11Wace Ce Ni? 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×