Skip to content
Part 13 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

LITTAFI NA BIYU

Shirun da Umman ta ce in yi shi din na yi na ja bakina na tsuke na zuba ido ina kallo tare da sauraron abin mamakin dake afkuwa.

Gabadaya yadda na yi zaton Baba zai yi hadin auren nashi ba haka ya yi ba.

Na jinjina al’amarin amma cikin zuciyata tun da ban isa in furta komai ba, Umma ta ce inja bakina inyi gum sai dai hakan ba yana nufin har zuciyata ma za’a tilasta mata yin gum din ba ne don haka ita kam tana ta faman kai kawonta.

Aure zai a hada ki ke da wanki uba daya. Abin da na ji ta tana fadi kenan kafin in samu saurin yin nazarin da zan iya tayata jimamin lamarin sai na ji zuciyata tana cewa wannan zumincin da Baba yake shirin yi da yawa yake.

Na yi maza na dakile tunanin nata ta hanyar kara mai da hankalina wajen sauraron abin da ke faruwa a falon don kar ta yi share shirgi wajen gayawa Baba magana don kawai ta ji ina sauraron abin da ke fitowa daga cikinta.

Na daga ido na kalli Baba a inda yake zaune sai dai maimakon in jiwo abin da yake fadi a lokacin tun da ina ganin labbansa yana motsi alamar magana yake yi wai sai na sake jin kalmar daya furta ta hadani aure da yaya Alamun tana ta faman kai kawo cikin kunnuwan nawa, to menene tsakanina da yaya Alamu? Tambaya mai ma’ana kenan da ná ji ta fito daga cikin zuciyarta wanda ya ji dalilih sanyani na sake mai da natsuwata zuwa gareta don inji abin da zata sake yagar mun, amma ba ke bace ba ta wajen Baba ba? Zuciyata tasan bazan saurare ta ba kan wannan in dai har aure zai hadata tsakanina da Yaya Almu to kuwa ko shakka ni da shi din ba dukkan mune yayan Baba ba.

Gabana ya yanke yayi mummunan faduwa a lokacin da nayi kokarin yin tunanin to cikin mu wanne wanda ba nashin ba? Na maida kallona wurin Yaya Almu don ganin shi a wani hali yake ne jin wannan rikirkitacen bayani da Baba yayi, kanshi a sunkuye yake babu wata àlamata damuwa a tare da shi to yasan komai ne?

Tambayar da na yiwa kaina kenan, kai da wuya idan ya taba sanin wani abu, da ya gaya mun musamman da yake nasha gwaba mishi Kalmar yan ubanci da yake mini, kai to ko Ummana da ta taba taba gayamin, don tama fi Yaya Almu jin takaicin wanan kalmar da nake gaya mishi sai dai komai ta kalleni cikin bacin rai take ce mun wai ke kome gurin Babangida ya miki ‘yan ubancine?

In ce ehmana, idan ba shi ba mene ne? Na sake dawo da tunanin cikin dakin nace wata kila dai shima yaya Almu jira yake yi a gama yin magana.

Ya yi tambaya kamar yadda ni ma nake shirin yi, don haka sai nima nayi maza na sunkuyar da kaina kasa kamar yanda naga kowa yayi na kwaikwayi irin ladabin su don kar ni kadai a ganni ina zazzare ido a tsakanin Jama’a.

Kamar Yadda na fadi shi Junaidu Rahma zan ba shi, Kubra in hadata da Zubairu, Kabiru da Rashida, Aina’u da Mujibu shi ma dana ne nan gidan babu wanda bai san Mahaifinshi aminina ne.

Zan yi hakan ne don kara karfin zumunci sai kuma Basira da na ce zan bai wa Rabi’u, shi ma dan’uwanku ne ba sai na tsaya yi muku bayani a kan shi ba.”

Na kara karkade kunnuwana na bude su sosai don in ji da kyau, shi Yaya Almu da wa Baba zai ce zai hadi shi.

Ban ji an ambaci Lamido ba, sai kawai na ji ana fadin Ko da mai magana a cikin ku?

Na yi maza na daga yatsa don neman a b ani izinin yin magana, cikin zafin nama amma ta damke dan yatsan nawa tamkar zata balle shi daga jikin yan’ uwan nashi, na dago ido cikin razana da ganin abin da tayin, na kalle ta na sai muzurai take yi mun, don haka na hakura na sunkuyar da kaina na yi shiru.

Na ce ko akwai mai wata magana?” Baba ya sake yin wata tambayar, shiru babu wanda ya tanka.

Sai ya sake cewa, “Ina Jinaidu yake ko ba kwa jin maganar da nake yi ne da ku?” Yaya Junaidu ya gyara zama cikin karin nutsuwa ya ce, ‘Baba maganar ta mu ba ta wuce ta godiya ba bisa dinbin alherinka da tausayawarka a gare mu gaba dayanmu da mu da kannenmu mata da ka yi wannan hukunci akan mu mun karbe shi da hannu bibbiyu, mun kuma yarda mun amince cewar wannan zabi da ka yi mana shi ne abin da yafi dacewa da mu, don haka muna maka fatan Ubangiji ya kara maka lafiya da yawan rai mai albarka ya baka ikon aiwatar da wannan kuduri na ka.

Mun gode Allah ya kara maka imani.”

Gaba daya aka masa amin, amin.

Dadi ya kama Baba sai wani murmushi ya ke yi ya kalli ‘yan’uwanshi da abokanshi da ke zaunc ya ce, To kun ji jawabin Junaidu tun da gaba daya kowa ya gamsu, to in kun yarda ku ba ni izinin sallamar yaran, don su tafi.”

Kan wani ya yi magana sai Umma Karama ta yi maza ta ce, Ba fa an gamsu ba an dai yi shiru ba ga wasu nan suna kuka ba?”

Lokacin ne na san ba ni kadai ce nake jiwo kukan da ake yi kasa-kasa ba, cikin raina na ce, wato dai dama kowa yana jin kukan biris kawai aka yi da mai yin shi. Umma Karama tana fadin haka sai wurin ya yi tsit aka yi shiru aka daina kukan da aka jima ana yi.

Cikin nutsuwa Baba ya sake yin magana ya ce, “Ina Kubra take?

Ta yi maza ta ce, ‘Gani Baba.”

“Wace ce mai kuka a cikin ku? Wace ce ba ta gamsu da hukuncin da na yi a kanta ba? Ta yi magana zan ba ta ‘yancis in ba ta wanda take so.”

Gaba daya aka yi shiru ya ce mata, “Duba mini ki gani wace ce take da hawaye a idanuwanta?” Anti  Kubra ta yi ‘yan dube-dubenta ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce,

“Babu kowa Baba.”

Ya ce, “To na gode.”

Zai soma sanya mana albarka, Umma Karama ta ce, tunda an rasa mai cewa komai ni ina da maganar da zan yi.”

Ya ce, “To dan saurare ni kadan.”

Ya kalli Umma Amarya ya ce ma ta “Maryam kin ji duk bayanin da na yi.”

Ta ce mishi, “Eh na ji.”

“To kina da wata magana ne?”

“Babu babu, sai ta fatan Allah ya baka ikon aiwatarwa da kan ka.”

Ya ce, ‘To na gode, tashi ki taf.”

Umma ta yunkura ta kama hanyar fita ta yi waje abinta. Ya waiwaya wajen Ummana ya ce, “Ke fa kina da abin da kike son fadi ne?”

Ta ce mishi, “Babu.”

“To ke ma na sallame ki, gaba daya wanda ya san ba shi da wata magana na sallame shi ya tashi ya tafi, in kuwa yana da ita to ya zauna zan saurare shi zan kuma share mishi hawyenshi.”

Gaba daya aka tashi aka yi ta fita, sai ni da Umma Karama ne muka gyara zama za mu yi tambaya. Ban san yanda aka yi ba ina waige-waige masu wuce ni suna fita, sai kawai na ji an figo ni ta baya ana jana da karfi a kan dole ba akan na yarda da jan da ake mini ba na bi, saboda irin wawan shakar da aka yi mini. Har muka shiga falon Umma bi kawai nake y ba tare da na gane wanda ya yi mini irin wannan rikon ba, sai da muka shiga aka sake ni, na waiwaya na ga ashe ita ce da kanta.

Na tsaya ina kallonta cikin måmaki na ce, “Umma ke da kan ki ne kika yi mini irin wannan shakar kamar za ki kashe ni?”

Ba ta tanka mini ba, ta wuce na bi bayan ta ina yi mata magana.

“Umma saboda na ce zan tambayi Baba maganar da na ji ya fada na zai hada ni auren da ban san dalili ba ne ya sa kike mini muzurai har..

Ban samu karasawa ba saboda kidimamman marin da Umma ta kifa mini a fuskata. Bin Umma da kallo na yi cikin kaduwa da mamaki ban taba jin ta zagen ba, balle a kai ga zunguri, balle a kai ga irin wannan kidimamman mari da ta kifa mini, ban taba jin ta yi mini mai karfi ba.

Na sa hannu na kara shafa barin fuskata da ta mara tuni yatsunta sun riga sun kwanta a wurin.

A hankali na juya na fito na bar mata wurin na sake dawowa tsakar gidanmu mai yawan kai kawon jama’a, saboda yawan mutanen da ke cikin gidan.

A yau babu kowa na, biyo ta sashin mu wato sashin yan mata, saboda yawan cushewar da ake yi a cikin shi wuni ake yi ana saka sauti a cikin shi ‘yanmata suna taka rawa.

Kai wani lokacin ma har cikin dare za ka jiwo sautin yana tashi, har sai yaya Junaidu ya aiko ya ce yana rokon arzikin abar su haka nan su huta. Amma yau tsit wurin yake babu wani motsi alamar dai bulalar Baba yau ta fyadi kowa da kowa.

Na gama kwana-kwanar kaucewa idon mutane da nake yi, na yi sa’a babu maigadi baya da bakin get, don haka na yi maza na tura kofar na yi waje.

Sai kawai ga Yaya Junaidu da Yaya Kabiru suna tsaye su biyu sun jingina da jikin angon gidan. Wata kila wani abin suke tattaunawa, wata kila kuma suma bulalar ta Baba ce ta fito da su waje.

“Ina za ki yanzu da daddaren nan Adawiya?”

Fuskarshi cike da mamaki, ya yi mini tambayar.

Na ce mishi, “Ba ko ina.”

“Ba ko ina? Ni kike cewa ba ko’ ina? Dama kina fitar dare ne ba a sani ba? Za ki gaya mini inda za ki ko sai na kai ki gaban Baba?”

Nan da nan na tsorata na soma yi mishi kuka na ce, “Ka yi hakuri yaya Junaidu.”

In yi hakuri? In yi hakuri fa kika ce Adawiyah? wuce mu shiga cikin gida. Wuce mu shiga kar mutancn da ke wucewa su ganmu tare da ke a nan.

A gaba suka tasoni zuwa dakinsu. Muna shiga na durkusa a kasa ina kuka tare da basu hakurin kar su hadani da Baba.

“Ina za ki yanzu da kika fita?”

Tsoratar da na yi ya sa ban iya boyewa ba na ce, “Za ni gidan wata kawata ce in kwana.” Ya zuba mini ido cikin nutsuwa ga alama dai ya yi mamakin maganar tawa, amma dai sai ya shanyc ya ce, ‘Me ya sa za ki yi haka Adawiyya?”

Ina kuka na bashi labarin duk abin da ya faru tsakanina da Umma, har da marin da ta yi mini, ya haska wurin da kyau ya’ duba ya ce, “Ki yi hakuri kin kure hakurin ta ne Adawiyya ban ga dalilin da zai sa ki yi ta kokarin sai kin yi mata magana da kika san ba ta son ji ba:”

Na sake daga ido na kalle shi na ce mishi, “Yaya Junaidu me ka ji Baba ya fada a kaina?”

Ya ce, “A kan ki kuwa? An ya Baba ya ambaci sunan Adawiyya a wurin nan? Kai Kabiru ka ji abin.

da Baba ya fadi a kan ta?”

Yaya Kabiru ya dan ja tsaki dan kadan, ya ce, Ai ni ba na zaton na saurari wata magana, ambaton Rashida da na ji an yi ko kai ma abin da ya sa na ji na ka da na Zubairu don an fade ku ne kafin nawan ban da haka kuwa da ban ji komai ba. Yanzu dai ke Adawiyya shiga gida ki kwanta in ba haka ba kuma zan gayawa Baba abin da kika shirya yi.”

Na yi maza na mike na nufi cikin gida zan koma wurin Umma sai kawai muka yi kacibis da Yaya Almu a hanya, har na gota na wuce shi ban tanka mishi ba, saboda na yi kwanaki bana magana da shi. Sai na ji ya ce mini, “Ji mana ‘yanmata, zo mana.”

Ban kula shi ba na ci gaba da tafiyata sai na ji ya ce, “Au ko da yake ma bai kamata in tsaida ke haka kawai ba tun da na ji baba ya fadi wanda zai ba da ke gare shi ko?”

Da sauri na juyo na zo gare shi na kalle shi cikin kosawa na ce mishi, “Kai ma ka tayani jin Baba ya ambaci sunana a wurin nan ko?”

Bai motsa daga yanayin tsayuwarshi ba, hannayenshi zube cikin aljihunshi yana kuma kallona cikin nutsuwa babu kuma alamar wasa a tare da shi ya ce, “In dai ba jin kunne na yi ba kamar na ji hakan.”

Na yi maza na ce mishi, “To wa ka ji za a bai wa ni?”

Ya ce, “Aa to nan kuma daya yaushe tsaya ina sauraron sunan wani kato? Ai ana cewa uwa za a bai wa Lamido sai na yi maza na toshe kunnena  ban sake jin wani zance ba, cikin zuciyata dai ina tayin godiya, don kuwa ni dama ita na yi ta roko ina ta fatan a ba ni ita.”

Na daga ido na kalle shi, babu alamar wani abu a tare da shi, don haka ban yi tunanin komai ba na ce, “Wace ce ita uwa din Yaya Almu? Ya ce, “Wata ce gidan su yana can baya haka ko da kina zato ke uwar yake nufi?” Na yi maza na ce mishi, Eh yaya ą Almu ai na dauka. ni ce.”

‘A’a to ki yi zaton ke ce Rabi, ke kina sona ne?” Na yi maza na dago ido na kalle shi na ce, “So kuma yaya Almu? Wane irin so? Ya ce, ‘A’a to ai shi na gani, in ba haka ba ya ya za ki yi tunanin za a hada irin wannan kwamacalar? Ai ba zai yiwu ba, ai ba a yin haka. A ina kika taba ganin wa ya auri kanwarshi?”

Na ce, “To bayanin kawai da na so ji kenan daga wurin Umma shi ne ta je tana marina.” Wani sabutaccen murmushi ya saki, sai kuma ya yi maza ya tsuke fuska, wata kila saboda ganin irin kallon da na yi wa murmushin na shi.

“Kar ki yi wa Umma karya ita ba ta mari. Sai dai nasiha da rarrashi.”

Na ce mishi, “Yau ta maren kalli ma yadda wurin ya tashi.” Na juya mishi gefen fuskar tawa.

Ya ce, “Ni ba zan gani ba sai dai ko in shafa da hannuna.”

<< Wace Ce Ni? 12Wace Ce Ni? 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×