Skip to content
Part 14 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

To shafa ka ji.”

Har ya miko hannun zai shafa, ban san tunanin me ya yi ba sai kuma na ga ya maida hannun nashi ya kalleni ya saki wani lalausan murmushi ya daga tafin hannun nasa yana kallo ya ce wannan hannun ba zai sake taba wani jiki ba sai na uwa, don haka ba zan iya shafa gefen fuskarki don jin marin da kike cewa Umma ta yi miki sai gobe in na je wurinta na nemi izinin yin hakan tukunna, kin san ni fa zan zamo mai gaskiya wajen matata, in yi ta sonta in manne mata ko’ina ta sa kafa ina biye da ita yanzu ni in ban da na ga Umma tana zarewa masu son yin magana ido ai ni da na nemi izini na fadi abin da ke cikina.”

Na juya kawai na kama hanya zan shiga sashin Umma, don dama kusan da wurin muke saboda na tsani jin kalaman Yaya Almu a kan matar shi.

A Zuciyata na ce, an tashi daga Aina’u an koma kan Uwa. Yana biye da ni yana cewa, To ni in da don tani ne ai da na tattara na koma dakin uwa na yi zamana in ya so in an daura sai kawai a je can a dauko mu tare.”

Na ce, ‘A’a haba abar musu kai dai kawai.

“A to su Ummna ne ba za su yarda ba, amma don tani ai a bar musu ni din kawai shi ne daidai in muka koma can inda za mu koma babu mai zuwa mana zirga-zirga a gida in muka ‘shige dakinmu muka maido, kofa muka rufe babu mai damun mu sai kawai mu yi ta kwasar amarci muna morewa in yi ta manne mata babu mai sa ido, balle ya ce don me? Kin kuma nasan duk gidan an babu wanda zai kai ki sa ido shi ya sa ma na yi nurna da na ji har da ke cikin auren ba za a barki a gida ba, balle ki samu damar yi mini zirga- zirga kina sa mana ido, kina ganin abin da nake yi kina zuwa kina bada labarin na zama ta ce.”

Na ce, ‘Uhun! Don tani yaya Almu sa ranka a inuwa… “

Kan in gama fidda abin da na gutsa sai ga Baba maigadi da gudu yana cewa yaya Almu, Yallabai ku nake nema ga fa Hajiya Karama can tana zuba akwatina a mota, kuma direba ya ce mini wai Alhaji ne ya taso shi ya ce mishi wai ya zo ya kai ta Katagun.

Da sauri Yaya Almu ya juya ya nufi waje yana cewa, Katagun da tsohon daren nan?

Nima na karasa falon Umma cikin faduwar gaba, don in gaya mata abin da ke faruwa. Ita ma ta je ta bai wa Baba hakuri. Ita da Umma Amarya na samu kuka take yi, Umma Amaryar tana ba ta hakuri.

“To ki tafi akan me?”

Umma ta ce “Zan tafi ai ya san duk abin da yake yi me ya yi tsanani a tsakaninsu yau da har zai ce ya saki Hajiyą Karama a kan shi? In ban da kawai yana nema ya jawo mini wani sabon al’amarin in ta ce ba ta yarda da auran Adawiyya ba, sai ya sake ta?”

Kuka mai tsanani Umma take yi ga ta cikin hijabi rike da jakarta a hannu, abin da na tabbatar shi ne in ban da Umma Amarya ta tare ta da ban same ta a dakin ba.

Waje na yi da gudu nima kukan nake yi mai tsanani, Umna tana shirin barin gidan Baba. Abin da bai taba faruwa ba, ban taba gani ba, ban taba ganin bacin ranta ba in dai na dangane da Baba ne sai yau.

Na nufi wurin Baba don in roke shi, yaya Junaidu na samu a durkushe a gabanshi yana cewa, Ni da Umma mu muka fi kowa kusa da Adawiyya a gidan nan baba mun roke ka ka janye wannan hukunci da ka zartar akan Umma Karama.”

Baba ya ce, To Junaidu ai abin da ta nemi a yi mata ne aka yi mata.”

Yaya Junaidu ya sake sunkuyar da kan shi kasa ya ce, “Baba ai kuwa kai ne ka ke yawan gaya mana cewar ita macc ba biyce mata ake yi ba. Sannan kullum a ce ita Umma Karama kowannc lokaci a kan Adawiyya nc ake zartar da irin wannan hukuncin a kan ta ina ganin kamar hakan bai yi dadi ba, don haka nake rokonka a madadina ni da Umma daga yanzu duk abin da ta ýi na laifi in dai akan Adawiyya ne to muna rokon arzikin a yafe mata, kar a sake yi ma ta wani hukunci.”

Kan Baba ya yi wata magana sai ga Yaya Zubairu ya shigo da saurin shi bai wani tsaya gaisuwa ba ya ce, “Baba Umma fa ta fito.”

Da sauri Baba ya tambayc shi, ‘Wacce?”

“Umman gidan nan.

Baba ya yi maza ya mike tsayc ban san me ya tuna ba sai kuma na ji ya ce, To ta fito mana, ta fito ita ma ta tafi ta tafi kar wanda ya hana ta tafiya.”

Yana fadin hakan ya yi waje da saurin shi gaba daya mu ma muka biyo bayanshi. Tuni Umma har ta kusa isa bakin gct ita kam da kafa za ta bar gidan ba ta kuma dauki komai ba. Da gudu na bi bayan ta zan bita mu tafi tare.

Baba ya daga murya kadan ya kirani, “Ke uwata zo nan.” Na yi maza na juyo zuwa gare shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, “In za ta tafi sai ki bi ta?

Ke ta ta ce, ko ta wace?” Ban yi magana ba kuka kawai nake yi.

Shiga gida ban son ganinki a nan.” Na yi maza na bar wurin ina tafiya ina jin Baba yana cewa “Kar wanda ya ce zai hanata tafiya ta je kawai ku bar ta ta tafi.”

Falon Ummana na dawo na zauna ni kadai ina ta kuka na rasa inda zan sa kaina in ji dadi. Me ya faru haka? Me ya yi tsanani da har zai zo ya tayar mana da hankalin gidanmu, mài dadi lokaci daya? Na dai ji Yaya Junaidu yana fadin shi da Umma su ne suka fi kusa da ni, to sun yafcwa Umma Karama komai ta yi mini, kar a sake cewa za a yi mata wani hukunci ban gane komai ba, ban gane abin da wannan bayanin nashi yake nufi ba, ko ba komai dai ba a gaya mini ba, dama na sani ni da Umma bab wani dasawa muke yi ba a bayyanc yake Umma ba ta iya kallona ta yi murmushi, in tana yi kuma ta ganni za ta tsuke fuska, kuma za ta yi shari’a tsakanina da wani to lallai ne ni ce mara gaskiya. To amma hakan ba yana nufin na san komai a game da tsakanin namu ba ne, in ban da yanzu da nake jin yaya Junaidu yana cewa ita Umma Karama kullum aurenta kan samu matsała ne a kaina.

Na daga ido na kalli hotona da Ummana wasu hawayen masu tsanani suka ci gaba da zubowa shar!

Shar!! Shar!!! Ina cikin haka ne kawai na ji an tura kofa in daga kai sai na ga Ummana, Yaya Almu da Yaya Junaidu suna iye da ita, tana shigowa ta nemi wuri ta zauna. Yaya Junaidu ya matsa kusa da ita ya zauna a kasa yana mata magana cikin nutsuwa, Umma tana sauraron shi. Sai da ta ji ya yi shiru sai ta ce mishi,

“Kafa san komai Junaidu ka san irin gwagwarmayar da na yi zan so Adawiyya ta yi irin wannan rayuwar ne? Ba ni fa da kowa sai ita, ita kadai ke gareni.” Muryarta ta ci gaba da rawa alamar a kowanne lokaci za ta iya sake fashewa da wani sabon kukan.

“Ko ba a yi wannan abin ba Rabi’atu ba farin jini za ta yi ba, tun ba laifinta ne kawai zai zamo matsala a gare a ba, za ta yi ta fuskantar matsaloli ne kawai ta ko’ina wadanda ba ta san dalilin zuwan su ba, saboda dai ni din ni ce uwarta. To irin rayuwar da ni na yi irinta ita ma Adawiyyah za ta yi?”

Yaya Junaidu ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata, ‘Eh Umma za ta yi rayuwar gwagwarmaya da kwaramni’ya irin wacce kike cewa kina jiye mata tsoro, sai dai kar ki manta kin yi rayuwar gwagwarmayar ne a karkashin shugabancin mutum mai adalci, mutumin da ya san karamci da amana, wanda ya sadaukar da rayuwarshi don samarwa kasa da shi ingantacciyar rayuwa, ba kuma sai na gaya miki ba kin fi sanin cewar bai hada ki da kowa ba a zaman da kika yi da shi, balle ya fifita wani a kan ki. To ki yi wa Adawiyyah addu’a ita ma ta samu irin na kin, amma ba ki, rinka gudar mata ba.

Na sha jin cewa Umma ina yi wa ‘yanmata nasiha da cewar lallai ne su zamo masu godiya bisa alherin mazajensu.”

Umma ta yi shiru ta sunkuyar da kanta kasa lana sauraron shi da ya yi shiru, sai ta ce mishi, “Na gode Junaidu.” Suma suka yi mata sallama suka fita suka tafi na dan bi su da kallo. Sai da na ga sun bace.

Sannan na matsa kusa da ita na ce mata; “Umma.” Ta dago ta kalleni. Na ce mata, “Wai me ya kawo Wadannan abubuwan Umma?”

Ta yi shiru tana kallona. Na ce,, “Kuma ga wasu maganganun ban mamaki da na ji Yaya Junaidu yana yi a gaban Baba da ban san me suke nufi ba.

Anya Umma ba kya yi mini wani boye-boye kuwa ko wani kunu-kunu…”

Kan in karasa sai kawai na ji ta kife ni da wani irin mari, sai da na dungura a kasa.

Tsoro gami da mamaki suka taru suka lullubeni. Yau kawai sau biyu Umma ta maren, mari kuma ba na wasa ba. A tsawon zamana da ita kuma kafin yau hakan bai taba faruwa ba. Lamo na yi na kwanta a kasa ina sauraron abin da zai biyo baya, ko za ta rufc ni da duka ne? Shiru ban ji wanr motsi ba, don haka na lallaba nan ja jikina na shige cikin daki na hau gado na kwanta, na bar ta nan zaune a kan kujera kuka take ta yi a zuciyata na ce “Watakila dai da ma dan kadan kike jira.”

Yadda Umma ta kwana a zaune tana kuka haka nima na kwana a kwance idona biyu. Al’amurán wunin ranar na ke tunawa, tun daga ji dana yi Baba yana anbaton hadani aure da Yaya Almu ko da yake dai ban samu wanda ya amsa cewar ya tayani jin wannan zancen ba. To amma kuma al’amura musu yawa sun biyo bayan hakan, masu tsanani da kuma na ban mamaki.

Gari na wayewa na yi komai da na saba a dakin tun daga wanka,, da alwala da sallah. Na yi kwalliyata ta hanyar gyaran jikina na kuma shafe shi da turaren Humra. Sannan na sanya doguwar rigata na yane kaina na fito don in gaida Umma. A falo inda tam kwana a zaune kasa kallon fuskarta na yi, saboda kunburin idanuwanta.

Ina gama gaishe ta na shuri takalmana na fita ba ta kirani ba, watakila ta yi zaton za ni gaida mutanen gidan nc, ko kuma wurin Baba, tun da yana nan, kuma dakinsu Yaya Almu na nufa za ni wurin Yaya Junaidu, don na gane akwai wani abu muhimmin abu tsakanina da shi. Sai da na ji ya amsa sallamar da na yi kafin na tura kofa na shiga dakin na su, yana kwance akan katifa yayin da Yaya Almu yake zaune kan kujera guda daya da ke dakin. Na durkusa na gaishe shi, yana amsawa cikin nutsuwa sosai watakila shi ma ya gane girmamawar da nake yi mishi ya karu.

Ya zuba mini ido cikin yanayin kulawa sosai kafin ya ce mini, “Me ya fito da ke yanzu a sanyin nan kuma da sassafe?”

Na ce mishi, “Yaya Junaidu wurinka na zo, don na gane akwai wani abu mai girma a tsakanina da kai nan gane kana da wani muhimmanci mai karfi a kaina, duk da ban san fa inda ya fito ba.

A hankali ya ce mini, “Amma ina fata ba abin da kika zo tambaya kenan yanzu ko?”

Na ce mishi, “Eh Yaya Junaidu zuwa na yi in tambayeka ka gaya mini gaskiya ka ji Baba ya ambaci sunana a wurin nan jiya?”

A nutse ya ce mini, “Na ji ya ambaci sunanki Adawiyya mene ne?”

So nake ka gaya mini dawa ka ji ya ce zai hada ni?”

Cikin nutsuwa ya ce mini, “Da Mustapha ne.”

Na sake kallonshi na tambaye shi, ‘Wane ne Mustaphan?”

Kan Yaya Junaidu ya amsa mini sai na ji Yaya Almu ya ce mini, “Mustaphan wurin aikin ku, ko ba sunan yallabai din office din ku kenan ba? Ai kin san na gaya miki cewar bayan kin gama aikin nan zuwan yallabai din ku biyu ya zo wurin baba, saboda an ce mishi ba zai yiwu ya zo ya kiraki ba sai ya nemi izini.

To shi ne daga baya ya turo iyaycnshi.”

Sanin da na yi an yi wadannan abubuwa da Yaya Almu ya fada duka ya sa na kidime nan da nan na shiga kokarin tunanin sunan yallabai na asali. Ina cikin haka Yaya Junaidu ya ce mini, “Saurare ni Adawiyyah.”

Na juya gare shi na maida hankalina wurin sauraron abin da zai gaya mini. Ya ce, Ki nutsu ki zama mai hankali, kin ji motsin wata yarinya a gidan nan tun da aka yi maganar nan?” Na ce mishi, “A’a.”

T kina nufin su duk sun gamsu da abin da aka yi musu ne?”

Ban amsa ba, sunkuyar da kaina kasa kawai na yi.

Ya ce, To ina tabbatar miki biyayya kawai suka yi, don haka ki tafi ke ma ki nutsu ki zauna wurin daya ki kudurwa ranki yi wa Baba biyayyar da tafi ta su yawa.”

Na ce mishi, ‘To.” Na mike zan fita da ni, “Daga nan kar ki je ko’ina ki wuce wurin Umman ki kawai.”

“Zan je in gaida Baba tukunna.” Na ce da shi.

“Baba yana Lagos yanzu Adawiyya sai da muka ga tashin shi a filin jirgi ni da Mustapha. Sannan muka biyo hanya muka dawo muka yi sallar Asuba a gidan nan Ya dauki Umma Amarya sun tafi ya bar Umma Karama, duk da da ita ya kamata ya koma ta karasa kwanakinta da ba ta gama ba, saboda bai huce ba kan laifinta da ta yi mishi ita ma Umma ya tafi bai yi mata sallama ba, saboda ran shi ya baci da abin da ta yi mishin, ko ni da Mustapha mun ji ana bude get din gida ne muka fita da sauri muka gan su za su tafi shi ne muka yi mishi rakiya, don haka ki nutsu ki shiga hankalinki kar ki bari shi ma ya yi fushi da ke.”

To Yaya Junaidu.” Na ce da shi.

<< Wace Ce Ni? 13Wace Ce Ni? 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×