Skip to content
Part 15 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

A falon Umma na same ta zaune kan sallayarta na durkusa a gefenta duk da tsoron da nake ji na kar ta sake marina. Na ce mata, ‘Umma Baba ya tafi.” Ta gyada kai nuna alamar ta sani. Hawaye suka zubo shar! Daga idanuna loakcin da na buda baki na ce mata, ‘Saboda ni ya yi fushi da ke?” Ta dan saki fuskarta ta shafa fatiha ta miko hannu tana share mini hawaye a hankali ta ce, “Ba saboda ke ba ne Adawiyya laifi na yi mishi.”

Na sake kallon Umma cikin nutsuwa a kuma a tsorace na ce mata, ‘Umma.”

Ta zuba mini ido tana kallona cikin sauraro ni kuma ina tsoro fadin maganar, don ina tsoron marin da ta gane yi mini, ban sani ba ko ta gane haka ne sai ta miko mini hannunta alamar wai in kara matsawa jikinta, cikin sauri na yi hakan ta kwantar da kaina akan cinyarta ba tare da ta yi mini komai ba, nima kuma ban sake yin wata magana ba. Har baba Talatu ta shigo tana tambayar me za a shirya mata na abin karyawa?

Wajen karfe goma da rabi ne yaya Junaidu ya shigo ya gaida Umma, ya kuma shaida mata cewar za su bi bayan Baba za su je su bashi hakuri kan fushin da ya yi. Ta ce mishi yana da kyau hakan kai da waye? Ya ce dukkan mu ni da Zubairu da Kabiru da Mustapha. Ta ce to ku gaishe shi.

Bayan fitarshi su Yaya Kabiru duk suka shigo suka yi mata sallama, yaya Almu ne ya shigo a karshe yana ganina a zaune ya ce, Ya ya haka ba za ki shirya ba?” Na ce, ‘Ai ban da ni.” Ya ya maza ya ce, “Haba Rabi shirya mana mu je ki yi mini rakiya.” Na ce mishi to.

Kasancewar wurin Baba za a je ya sa na yi kwalliyar atamfa fara super ce tana da dan adon furanni bakake jefi-jefi. Takalmin da na yi amfani da shi shi ma baki da fari ne hakan nan jakar hannuna sai na yafa farin gyaie na yi matukar yin kyau, sai daukan ido nake yi, ga kuma kamshina na kowanne lokaci.

Na yi wa Umma sallama na fito na hangi yaya Almu yana fitowa daga wurin Umma karama lokacin ne na tuna yau ko gaisheta ban je na yi ba. Na same su a waje dukkansu sun shirya dukkansu kwalliyar ta zarce suka yi babu kuma wanda bai sanya hula ba a cikin su, sun yi matukar yin kyau, amma zan iya cewa yaya Almu daban yake kasancewar shi mai yawan amfani da fararen tufafi, saboda ganin shi a cikin su bai hanawa ka yi ta ganin kyan kwalliyar tashi ya yi kyau.

Yaya Junaidu da yaya Zubairu ne a gaba, yaya Zubairu yana tuki, yaya Kabiru yana santar bayan direba sai yaya Almu a tsakiya ni kuma ina gefen shi ta jikin kofa. Ana tafiya suna hirarsu mafi yawancin magangarta su akan aure ne da halaiyar mata na

tsananin kishi da rashin hakuri. Yaya Zubairu yana ba su labarin abin da Umma Karama ta yi wa Baba da yadda ita da kanta ta nemi ya ba ta saki da kuma ya ce ya ba ta sakin ta rude tana ta faman kuka.

To wannan wane irin abu ne naka? Yaya Kabiru ya ce, Eh ai su haka suke suna son abu suke nuna wai ba su son shi a dole su ga masu jan aji.

Su ka dan yi dariya cikin jinjina lamarin, shi kam Yaya Junaidu tsaki ya yi ya ce, “Ni fa ko dokin auren nan ba na yi saboda na san wani nauyi ne kawai zai hau kan mutum kuma ko daga kallon irin yadda al’amura suke tafiya ma ai kai ka san su Baba hakuri kawai suke yi.”

Yaya Almu ya karkato ya sunkuyar da bakinshi ta wurin kunnena ya ce, “Ki ji mun Junaidu wai baya dokin aure, saboda sai an yi hakuri da mace ake iya zama da ita, shi ke nan yake jin haka ni kam dokin nake yi ina zumudis cikin raina a kowanne lokaci kuma kallon agogo nake yi ina ganin tafiyar lokaci, ina kirga sauran awowin da suka rage a kawo mini Uwale, kin san irin son da nake yi mata kuwa?”

Na girgiza kai nuna alamar ban sani ba.

Ya ce, “Uhm! To ko yau din nan sai da na ganta wajen sau hudu, amma har yanzu ban gaji da ganin nata ba, ji nake tamkar a bar mu mu biyu kawai a daki mu yi ta maganarmu mai dadi in kuma na ji ina ra’ayi in dan shafe ta in ji dadi.”

Na ce, “To ai kai da zamanka ka yi a gidansu kawai ba ka yiwo wannan tafiyar ba.” Ya yi maza ya ce. ‘Eh kuwa to sai dai kuma na riga ai na fito, amma dai bari kawai ba zan yarda a kwana ba yau din nan za mu dawo, don in je in ganta da daddare.” Ya dago ido ya kalli Yaya Zubairu da ke ta faman tuki ya ce mishi, “Kai Zubairu wannan irin tafiya da kake yi ni fa sauri nake yi, don ba kwana zan yi ba, zan dawo in tafi tadi.”

Yaya Kabiru ya ce, To mu sauke ka mana ka bi ta nan.” Ya nuna mishi hanyar daji wai ya yi yanke.

Gaba daya suka kwashe da dariya, suka ci gaba da zancensu shi ma ya juyo wurina hannunshi ya miko yana taba makalallen dankunnen kunnena na asalin azurfa, ya ce, “Rabi kenan ke kam kin iya kwalliya har dan kunnen nan ma fari ne da ratsin baki ga abin wuyan shi ma.”

Ya mika hannu zai ciro abin wuyan daga cikin gyalena wai ya kara gani, karo, na farko da na ji ba na son hakan na yi maza na hana shi. Cikin hanzari ya daga hannun nashi daga jikina yana cewa, “Uh! Gara in yi maza in koyi daina taba jikinki kar wata rana Uwa ta ganni, don na san kishi za ta yi, daga ganinta. To wannan fa na gamu da daidai da ni ni kishi-kishi ya ya kenan?” Ya zuba mini ido yana kallona cikin sauraro ban tanka mishi ba.

Ke kin san kishin Uwa kuwa?” Ya sake tambayata, ,nima na sake yin kamar ba da ni yake maganar ba, ya dan yi murmushi ya ce, “To ko da yake dai babu komai tun da ina son ta kin san shi namiji kan matar da yake so kamar bawa yake.” A Zuciyata na ce, kai ne dai hakan.

“Ai ni babu abin da Uwa za ta yi mini in ce bana dokin aurenta, ko in rinka maganganu irin na Junaidu ji shi ji abin da yake fadi.” Lokacin ne na Jiwo hirar da Yaya Junaidu yake yi na wani abokin shi da wai saboda halaiyar matar shi, shi din ya daina Zuwa gidansu. Yaya Almu ya kalleni ya ce, “Ni don irin su Junaidu sun daina zuwa gidana ni da Uwale ina ruwana? Ban da kawai mu rufe kofa mu yi ta sha’aninmu.” Na kalle shi kawai cikin zuciyata na ce, ‘Ai kai kam sai addu’a don ka riga ka tafi.”

Jirgin sha biyu da rabi muka hau, don haka a gida muka yi sallar Azahar. Bayan mun idar ne muka sami Baba a falo shi da Umma Amarya, ta sha kwalliya riga da siket wai Umma ta sanya tamkar wata ‘yar yarinya.

Baba yana cin abincin da Umma Amarya ta gama shirya mishi a gaban shi ya kalle mu ya ce, “Wannan wane irin zuwa kuka yi babu sanarwa, babu komai ko kuma kin zo ne don ku cinye mini abin dadin da Amaryata ta shirya mini?”

Gaba daya aka dan yi murmushi, sai yaya Junaidu ya ce mishi, “Baba mun zo ne don mu baka hakuri kan laifin…. “Kan ya karasa Baba ya katse shi.

“Kar wanda ya ce zai yi mini wata magana ko ya ce zai ba ni hakuri, ba zan saurare shi ba tun da dai ita uwarku ta ga abin da ya dace ta rinka yi mini kenan, to mu je zubawa ni da ita.”

Gaba daya aka sake shiga wata nutsuwar ni kam kuka a kama yi. Yaya Zubairu ya kara rage murya ya ce, “Baba, Umma kuwa mai gudun bacin ranka ce, ko wani ta hango zai bata ma hankalinta tashi yake yi.”

Ya ce, Eh, amma kuma tafi kowa yi mini abu cikin gadara ina abin da ya shigar da ita cikin maganata ni da matata, ita auro mini ita? Ko ba kwanan nan ne ta yi mini irin wannan abin ba na ce mata kar ta sake shi ne yanzu ma ta sake? Saboda ta raina ni, to hana ta tafiyar da kuka yi ni zan bar mata gidan na shekara guda ko daurin auren ku ba zani ba, su Yayan Tudu sa daura.”

Kukan da nake yi ya tsananta sosai, na ce, “Baba ka yi hakuri.” Ya kalleni cikin bacin rai ya ce, Haba Uwata a ce har yanzu ni ban wuce Umman ku ta dauko hijabinta ta ce za ta bar mini gida ba, saboda wani abin bacin ran da na mata ba?

Na ce, “Ka yi hakuri Baba ta san ta yi maka laifi, ta ce mini ta yi maka laifi.” Ya zuba mini ido ya ce, Ta gaya miki?” Na yi maza na ce mishi, ‘Eh Baba, ta ce mini ta yi maka laifi na kuma San ba ta ji dadin abin da ta yin ba.”

Ya ce, ‘A’a ta ji dadin hakan da ta yi Uwata tana sane da abin da take in ba haka ba ai kwanan nan ne na ce mata kar ta sake yin hakan, ta ce ba za te sake ba.”

Yaya Almu ya dan gyara zama ya ce, Baba ba fa kwanan nan ba ne tun Rabi tana da shekaru hudu ne abin ya faru.”

Baba ya ce, ‘Af! To yaushe ne? Yaushe ne aka haifi Uwata? Ba kwanan nan ba ne aka haifeta, anan gidan ne fa aka yi renonta. Aurena kuwa da ita uwar taku ai ba na shekaru arba’in ne daidai, amma saboda rikicin auren da ba a daura ba ta fito za ta tafi ana ba ta hakuri, babu kuma abin da yafi komai kona mini zuciya irin ‘wuce ni da ta yi ina tsaye ai na fito ne don ta ganni ta koma, amma ta wuce ba ta fasa ba, wato bari ta nuna mini ni din me?

Yaya Kabiru ya ce, Ka yi hakuri Baba, Umma ba za ta fadi haka ba ta dai yi maka ba daidai ba in mun je gida kuma za mu gaya mata duk da ta sani ta san ta yi maka laifi, kuma na san ta fi mu rashin jin dadi.”

Baba ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce, “Abin da take gadara da shi kenan ta san komai ta yi ba za ku bar ni in yi mata abin da ya dace da ita ba, ai ya dace ta shekara ba ta ganni ba, in Maryam ta gama kwanakinta ita Hajiya Karama ta zo ita kuwa ta yi ta zamanta anan.”

Yaya Junaidu ya sake gyara zama cikin nutsuwa ya kalle shi ya ce mishi, “Baba ka taba ce mana ba a biyewa mata.”

Baba ya yi murmushi ya ce, “Gaskiya ne Junaidu ba a biye musu ku yi, ta hakuri da su, don kuwa su din manyansu da yaran su halinsu duk daya ne, yanzu ka duba ka gani irin gudun bacin ran yarinyar nan da nake yi, amma ko a jiknta, ita in tayi nishadi sai ta bata mini.”

Jikina ya yi sanyi na yi zaton ko da ni baba yake maganar. Na yi maza na kalle shi na ce, Ni Baba?”

Ya ce, “Uwar ki dai ke kam me za ki yi ki bata mini rai uwata?” Na dan sake kallon shi na ce, “Baba yanzu ka ce auren ku shekaru arba’in kuma kana ce mata yarinya? “

Ya ce, Yarinya ce uwata na mafi ganin kuruciyar ta kan kowa, don kuwa an daura man aure ne tana da shekaru bakwai. Wani irin aure da mutunci da amana ya bani, amma wai kullum aka dan yi wani abu sai ta zaro gyale wai ita za ta bar ni a ce ba ta ci mutuncina ba?”

Na ce, ‘Gaskiya Baba ba ta kyauta ba ka yi hakuri.”

Ya ce, ‘To ya ya zan yi? Ya wuce.”

Muka shiga hira sosai. Baba ya ce, “Za ku tafi ne ko kuwa kwana za ku yi?” Na yi maza na ce, “Ni dai kwana zan yi Baba.”

Yaya Zubairu ya ce, “Mu zamu koma don mun fito dukanmu ba mu bar kowa ba a gidan.”

Baba ya yi maza ya kalle shi ya ce, “Abin da nake yawan tunawa kenan, dukan ku za ku bar gidan ko da yake dai ga wasu samarin nan su Hamza, amma me kuke ganí?”

Yaya Kabiru ya ce, “Za su iya yin komai baba ai shi Hamza da Musa masu tsayawa ne kan al’amura za su daidaita komai.”

Ana waunan maganar yaya Almu ya yi mini magana a hankali, “Ki dai san wannan zuwan na ki rakiya kika yi mini, don haka ba wani kwanan da za ki yi tafiya za mu yi, don ni ba zan kwana ba zan je gida in je tadi, zan kuma gayawa Baba.”

Na yi maza na ce, “A’a ina ruwana?” Baba ya kalleni ya ce, “Mene ne Uwata?”

Na ce, “Baba Yaya Almu ne wai ba zan kwana ba.”

Ya ce, ‘A’a a kan me? Shi ma ya kwana mana in yana so, mene ne na sai ya sa ki kin tafi? Ai ni ma ina son kwanan na ki sai mu yi hira ko?

Na ce, “Eh Baba.”

Jin da na yi Baba ya ce yana son kwanan ya sa na yi niyyar yi mishi girki, don ya kara jin dadi. Ana idar da sallar La’asar na shiga kicin na samu Umma Amarya a ciki na shiga tayata aikin da take shirin yi. Muna ‘yar hira sai ga Yaya Almu ya iso kofar kicin din. “Rabi zo mana.” Ban kalle shi ba, na ce, Girki zan yi wa Baba.”

<< Wace Ce Ni? 14Wace Ce Ni? 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×