Skip to content
Part 16 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Umma tana jin haka ta fice daga ciki, shi kuma ya shigo, “Ke yarinyar nan kina so ki raina ni fa kwanan nan in kinra ki ki ce ba za ki zo ba?”

Na ce, ‘A’a to mene ne in na fadi haka kai da kake murnar za ka samu matar da za ta raba ka da yan’uwa duka? Ai har da haka zai kara sawa in kwana, don in gayawa baba komai da komai, in yana da abin yi tun wuri ya yi.”

Yaya Almu ya zuba mini ido ya ce, “Ke ki ce za ki zauna ne don ki kulla mini sharri, yaushe na gaya miki haka? ta uwa ma wannan salihar yarinyar yaushe za ta ce za ta raba ni da ku?”

Na ce, Ai ba ita ce mai raba kan ba, ra’ayin ka ne hakan kana samun mata za ka rabu da ‘yan’uwa.”

Yay ce, “Tabdijam! To ai gara da na biyo ki kicin din nan kin ga ai na ji irin kullalliyar da kike neman ki kulla mini.”

Na yi shiru na soma shirye-shiryen girkin da zan yi ina harhada kayayyakin da zan yi amfani da su ya matso kusa.da ni a hankali ya rada mini.

“Da gaske aure nake so Rabi, kamar in yi ya ya? Yanzu na riga na girma son mace na ke kamar me? Da kuma ba ta damen ba, don ni ko ‘yan mata a ban cika yi ba sai dai kawaye, amma a dan tsakanin nan ni ka ina a tsorace da kaina nake, shi ya sa kusan

kullum ki ke ganina ina Azumi.”

Na ce, “Uh! Yana da kyau.”

Na ci gaba da aikina, shi kuma ya kara matsowa jikina.

“In ban da sha’anin kima Rabi ai da na yi miki wata magana.”

Na ce, “Kamar wacce iri kenan?”

Ya ce, “A’a na gane kamar kin tsorata sosai kan cewar da kika ce kin ji kamar baba ya yi na cewar Zai hadani da ke aure.

Na yi maza na kalleshi na ce, Zan tsorata manan hakan fa yana nufin tsakanin ni da kai akwai wanda ba baba ne ya haife shi ba.”

Hankalin Yaya Almu a kwance ya ce mini, “To sai me in an yi haka? Ni inda na san wannan kawai matsalarki ai da sai in ce miki ke ki rike baban kawai na ki ne, ke kadai tun da kin fi ni tabbacin zama yar shi ko ba komai ke Umma ce uwarki, yanzun nan ne kuma Baba ya gama cewa tun tana da shekaru bakwai aka bashi ita, bayan haka ke kadai ce mai kama da ita a gidan nan.

Ni kuwa muan da yawa ni ina kama da Baba, Junaidu yana yi, Zubairu yana yi, Musa yana yi, kin ga da sai duk ki maida mu ‘ya’yan dangi kawai, in ya so ni sai in zama surukin shi.’

Na ce, ‘A’a ai kai ma Umma Amarya ce ta haifeka.”

Ya ce, “Ai wannan ba komai ba ne tun da ita Umma Amarya ba budurwa ba ce, lokacin da Baban ya aureta.”

Sai da plate din hannuna ya subuce kasa ya tamutse, jin maganar da Yaya Almu ya yi mini.

Bai ku kara kaduwar da na yi ba sai kawai ya sunkuya ya tsine fasassun tangaran din ya zuba su cikin dosbin ya tawo ya tsaya kusa da ni, bayan ya wanke hannunshi.

‘Ashe Umma ba ta taba gaya miki ba? Ai ita Umma Amarya ta auri Baba ne bayan ta fita takabar mijinta na farko kin ga kenan in dai dan’uwanshi ta aura ta can na samo kamannina da shi, kamar dai su Junaidu kenan ko ya ya kika gani? Hakan bai yi ba?”

Nan da nan zuciyata ta shiga kai kawo cikin tunani mai tsananin rudarwa a ce Yaya Almu ba dan Baba ba ne na cikin shi? Kai zan ji tausayin shi in har hakan ya faru baki ne komai ba rabi nace kai yaya Almu ace zaune kaima badin Baba bane na cikin shi zanji tausayin shi in har hakan ya zai sance Baba yana bakarar da hanziri jarumi mutumin kirki kamar ka wanda zai yi alfahari dani wanda zai rinka daga ido yana kallonshi yana ganin shi a matsayin wani alheri da Ubangiji yayi yarda in kore shi in har zan iya yara in kore shi daga jikinshi ince kai din ba nashi bane don komai aure ya halatta a tsakaninna da kai to na zamo mai son kaina da yawa in kuwa zane kaina akan Baba to banayiwa kaina adalci ba don haka muyi zamanmu kawai ni da kai dukkan mu ya’yan shi ne.

Yaya Almu ya ce “Uhun Rabi ke nan ni a wurina da ace dukkanmu na shi ne gara a yi in wannan din, ke tashi ni surukinshi ai ya mallakarmu dukanmu. Ke ‘yarshi ta cikinsa wacce matar da ke so ya ke girmamawa fiye da kowacce ta haifar rooshi, ga ki mai kyau, Rabi don kawai kin yi sa’a kin dauko kyau irin na Umma ke har ma kin so ki fita don kuwa ke kam ai ko namiji ya yi tsayinki ya more ina jin dai wurin Baba ki ka samo wannan tsayin naki, ga ki mai kirki da kuwa kin gaji kirki Rabi kin san yawa kirkin Umma da laherinta kuwa? Dubi irin shugabancin da take yiwa Baba a gida yanzu ke a ganink ace ke matata ce, za ki zama mun uwargida a gidana ki yi mun irin shugabancin da ki ka ga Umma ta na yi bai fi mun ace ubanmu ne daya za a daukeki a baiwa wani ina kallo ba?”

Na ce “Kai Yaya Almu mu bar maganar nan kawai, tana sawa gabana yana faduwa, zuciyata tana harbawa da sauri.”

Ya yi maza ya ce “Uhm to gara mu bar ta, bari mu yi wata me sunan wannan abincin da za ki yi mana? Na cc mishi “Stuffed chickcn onc” Na yi mishi lakabi da “one” din ne don zan iya yi maka su kala- kala don haka ran da zan sake yi maka wani zance maka stuffed chicken No 2, don in bambance maka su, ya saki wani irin lallausan murmushi ya ce ai na yarda da ke Rabi na san ke gwanar girki ce na kuma san za ki iya tattalin mijinki za ki iya tarairayarshi ki reneshi in na zauna na yi tunani na tuna tsananin kwadayina game da shimfidata sai in ga to ina ma dai ke ce wacce zan rinka shimfidewar? Kin sanni ina son mace mai sura irin taki, ina son komai naki Rabi ina Son duk wani yanayi naki in da za ki yarda da shawarar da na kawo da kin yi mamakina da kin ga irin tarairayar da na yiwa shagwabarki.”

Na yi ajiyar zuciya mai karfi na ce Yaya Almu ka yi hakuri ka san ban saba yin irin wannan maganar da kai ba.”

Ya ce “Gaskiya ne Rabi gaskiya ne, to koya mun girki in mutum zai yi stuffed chickcn one, me zai bukata? Na soma yi mishi bayani cikin sauri don ban son ya sake kawo wancan hirar tashi na ce mishi dankwalcliyar kaza katuwa kamar wannan ya ce na ganta, na ce to ga nama cikin cup madaidaici, butter cokali shi da na ture wadannan gefe na sake jawo wani hadin na shiga nuna mishi na ce sai kuma wannan naman saniya cup daya da Rabi ferarreen dankalin turawan da aka yanyanka shima cup daya madaidaici ga butter cokali takwas, murmushi biredi cup daya, kwat guda biyar sai albasa guda biyu suma.

Ya ce To amma Rabi wannan irin girki naki ba zai saki kiba ba?”

Na yi murmushi na ce “Ai kuma na iya abincin rage kibar iri-iri.”

Ya cefo mu yi magana gaskiya Rabi kin san ba zai yiwu ina kallon alheri da idona kuru-kuru in barshi ya wuceni ba, ni fa gaskiya na fi so ki zama matata ni bana son yin kanwar da ke in kima bukatar yayu ga su Zubairu nan ga su Junaidu da su Kabiru ke har su Hamza da su Musa sun gimeki ki yi dasu, ni ki bar ni kawia in zama mijinki uban ‘ya’yanki, ki haifar musu masu yawa, ki yi musu tarbiyya su zama mutanen kirki na cc a’a.ba za a yi haka ba kai, dai ka je ka auri Uwalenka, nima in auri Mustaphan wurin aikinmu, yallabai dama ni ina son shi don ina sha’awar tebarshi tana ba ni sha’ awa ka sanni ina cikin mutane masu girmama teba da ganin darajarta be zan iya zama da wanda ba shi da ita ba.

Nan da nan na ga Yaya Almu ya tsuke fuska alamar zuciyarshi ta so su shi kuwa na yi maza na koma kan aikina na kamashi gadan-gadan na dauko turmin karfen da na riga na wanke na kife don ya bushe shi da tabaryarshi na zuba naman nan na soma dakashi tare da ferarren dankalin nan sai da ya yi laushi tukuna na kwasheshi cikin wani kwanon silba mai dan fadi na juyre murmushen biredi akai da kayan yaji da yankakken albasa na sa kwai da ruwa cokalin cin abinci guda biyu na cakudasu da kyau sannan a dauko dankwaleliyar kazar nan da ba a cire komai a jikinta ba sai kai da kafafuwa na yi ta cusa kwababben naman nan a cikinta sai da na cikata tam ta yi matukar yin nauyi sannan na kawo zaren lilo na daurcta da kyau Yaya Almu yana bayani ta hanyar rike mun ita sannan na kawo blucband na yi ta mulketa da shi kafin na bude 0ven na sakata a ciki ta soma gasuwa na ce mishi minti arba’in da biyar za ta yi a wannan wutar don haka bari in yi wannan hadin ka gani ya ce mun to.

Na dora wancan naman cup daya na yi mishi hadin farfesu mai ruwa sosai na zuba kayan hadi su kayan kamshi shima na rufe sannan na koma na sake shiryawa Baba abincin darenshi na ka’ida tawon laushi miyar yauki na tuka mishi tuwon alkama miyar busasshiyar kubewa, na dawo kan kazar nan na cewa Yaya Almu ai ka ga bayan minti arba’in da biyar din nan na sake rage wuta ta yi kasa sosai na tsawon minti talatin ya ce Eh na gani na ce to yanzu komai ya kammala bari in cirota ta gani na ciro kazar ta yi shar gwamin sha’awa sai wani kamshi ke tashi daga cikinta na juye farfesu a kanta cikin kwanon dana sanyata mai kyau na’ kawo murfi na rufe. Yaya Almu ya ce bari in kai mana wannan ke kya taho da sauran.

Na ce mishi to.

Na shiga falon, na samu Baba yana tambayar Yaya Almu kai ka yi sallar Magariba kuwa Lamido?”

Ya ce “Eh Baba itama mai girkin ai ta yi balle ni na bi ku sallah ana idarwa ne dai na fito ban tsayya ba.” Na isa wurin ajiye abinci na ajiye kwanukan da na zo da su kamshi ya gauraya ko ina Baba ya kalleni cikin murmushi ya ceUwata in kina mun irin wannan liyafar a za ki sa in fasa yin bikinki a bana ba kuwa?”

An zauna gaba daya ana cin abincin rana cikin raha, Baba ya sakc cewa da can duk tsawon lokaci uwata ta iya irin wadannan girke-girken amma ba ta ciyar da danta da su ba ta boye abinta sai ta je gidan mijinta ta yi ta shirya mishi gara, miji ya fi uba ne uwata?

Na kalleshi cikin ladabi na ce mishi “A’a Baba, ya yi maza ya ce “A’a ya fi miji ya fi uba daraja uwata don kuwa shi ta dalilin biyayyar da ki ka yi mishi ne za ki shiga aljanna, uwarki ba ta taba gaya miki haka ba?”

Na ce Ta taba.” Ya ce “Yauwa to ita ai mai girmama aurenta ne.”

Na idar da sallar isha’i, bayan na yi wanka sai na zauna na yi kwalliya bayan na gama shafe jikina, na gyarashi yanda ya kamata, doguwar riga har kasa na sanya na wani yadin material bluc, Umma ce ta zo mun da yadin daga Dubai tsawon rigar ta sanya har ba a iya hangen siket dinta dake jikina, wuyan rigar an yi adon zare dan kadan na daura dankwalin a kaina sannan nakawo sarka da ‘yan kunne bluc da warwaro da zobe mahadinsu na sanya, farin zaren da aka ratsa da blue wajen yiwa wuyan rigar ado ya sa na yi amfani da farin gyale dan siriri sosai na sanya farin takalmi da jaka na kara fesa wani turen na yi matukar yin kyau na fito na shiga dakin Baba inda duk aka hadu ana ta hira na je na zauna kusa da Baba a kasa sai dai ban tsoma baki cikin hirar tasu ba, ian dai ji ne kawai don ta yi mun kama da hirar manya da suka gama ne yaya Junaidu ya yi wa Baba sallama ya ce mishi za su tafi, za su bi Jirgin karfe goma.

Baba ya yi musu addu’a, suka yiwa Umma Amarya sallama suka fita. Yaya Almu ya ce mun zo mu je ki rakani mu kaisu airport mu dawo.

Baba ya kalleshi ya ce “Kai Lamido ba ka ce gobe kana case a court ba ne, ya ce eh zan yi Sammako in tafi ya ce to shi kenan ke uwata tashi ki rakashi, na bi bayan Yaya Almu wanda shima ya sha kwalliya cikin farin boyel.

A hanya muna dawowa ya dan wiawayo kadan ya kalleni ya ce mun “Ina son ki fa Rabi kin san ai ba zai yiwu in yi ta yi miki haka-haka ba, ko? Na ce “E to haka ne amma ai ka san ni kuma da wuya in yarda ka san mene ne so?”

Da sauri ya tambayeni don me? Ina da shekaru talatin a duniya ki ce mun ban san so ba? Na ce kwanan nan ka gama son Aina’u har kana zama kana rera mata wakoki kana siffantata da siffofin ban mamaki kace wai kai a haka kake ganinta a irin son da na san kana yi mata, ni na dauka in ba a baka ita ba suma za ka yi ta yi sai na ga ka shanye kemadagas ko a jikinka sai ka koma son Uwalen da aka ce za baka ko yau da safen nan akan sonta ka ke shi ne nima yanzu za ka ce kana sona?

Ya ce “E ai ina sonki din ne.”

Na ce “To kar ka sake gaya min haka abin da na sani shi ne kai wana ne ubanmu daya don haka ni ban taba yin wani tunani game da kai ba, yallabai kadai nake so shi ne yake bani sha’awa tebarshi kuma tana burgeni tun ba in naga ta turo cikin babbar rigar nan tashi ba.”

Yaya Almu ya buge mun bakina da karfi da bayan hannunshi na sa hannu na taba labban nawa na ga jini don haka da karfi na rinka kurma mishi ihu.

<< Wace Ce Ni? 15Wace Ce Ni? 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×