Skip to content
Part 17 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Har muka iso gida ban yi shiru ba yana tsayawa na bude kofa na fito ban saurari maganar da yake yi mun na nufi falon Baba ina ihu gashi na yi sa’a labban nawa sun kukkubura shi kadai na smau a ciki na durkusa gabanshi ina ihu ya zubawa bakin na wa ido yana kallo.

“Yi hakuri uwata ai kin wuce irin wannan kukan mai karfi yi shiru ki gaya mun me ya fasa miki bakin naki haka?”

Na bar kuka na ce mishi Yaya Almu da kanshi ya lcka ya kirashi ya shigo, ya kalleshi ya ce me ta yi maka haka? Ya ce rashin kunya ne da ita Baba ba zaka gane rashin kunyarta ba sai na ce maka Baba daga shekaran jiya zuwa yau sau biyu Umma ta bugeta.

Fuskar Baba ta yamutsc alamar ranshi ya baci da jin bayanin na Yaya ALmu ya kalleshi cikin bacin rai ya ce lallai ne ka gaya mun abinda ta yi maka mai tsananni wadda ya sa ka yi mata wannan abin bayan ta yi kwalliyarta mai kyau dubi abinda ka yi, na ce ka

duba waiwaya ka gani me ta yi maka?

Yaya Almu bai boye ba ya ce maganar mutumin wurin aikinsu take yi mun.

Baba ya kalleni cikin nutsuwa ya cc me yasa haka uwata? Na kalli Baba cikin nustuwa na ce Baba dama ana aure  tsaknin wa da kanwa ne? Ya yi maza ya ce Babu na ce to to shi Baba sai ya rinka yi mun wata magana na ce mishi ni da shi ai kaine ka haifemu, ya ki. Baba ya ce to kai me ya sa ka ki Lamido? Yaya Almu ya sake maida bayanir shawarar daya bayar, Baba ya yi murmushi ya ce to amma uwata ai ina ganin kamar lallai Lamido yana sonki tunda har zai iya kawo wannan shawarar a tsakaninku ban ga abinda zai sa ki ki yarda ba, na ce msihi a’a baba ni na fi so ace Yaya Almu dani dukanmu ‘ya’yanka ne bana so ka rasa kowa a cikinmu bana so ace ba kai ka haifi Yaya Almu ba haka nan zan yi bakin ciki in har aka ce mun ba kaine mahaifina ba nan da nan na soma yi mishi kuka baba ya shigå rarrashina har na yi shiru na share hawyaena na kalleshi cikin nustuwa, bayan fitar Yaya Almu na ce mishi Baba waye Mustaphan da aka ce za ka baiwa ni? Ya zuba mun ido ya ce Lamido ne na sake buda baki cikin karfin hali na ce mishi Baba su waye suka haifeni? Da gudu hawaye suka rinka zuba daga idona, Baba ya sake kallona ya ce mini, “Kina tuhumar Ummar ki ne?

Na yi maza na ce mishi, ‘A’a.”

To don me ni za ki yi mini wannan tambayar kin taba ji an ce miki ga dan’uwanki ya zo?

Na yi maza na ce mishi, ‘A’a Baba.”

“To don me shi Lamido ba za ki hada shi da su Junaidu ba, me ya fi su? Me ye bambancin shi da su?

Da Lamido da Junaidu da su Zubairu duk daya ne kar ki damu kan ki da cewar shi yaya yake, muhimmin abin shi ne ke tawa ce wani muhimmin abin kuma shi ne Ummanki ce uwarki al’amarinki mai girma ne a wurina, don haka jna fata za ki karbi mijin da na zabar miki da hannu bibiyu in dai ba ba kya son shi ba ne.”

Na durkusa gabanshi na ce mishi, “Zan bi umarninka da hannu bibiyu Baba ko da ba Yaya Almu ka zaba mini ba, balle Yaya Aimu sanin halin shi d alherinshi da na yi ne ya sa na ke tsoro kar a ce shi ma ba na ka ba ne?”

Ya ce, “To kar ki ji komai ni kowa nawa ne.”

Na ce mishi, “To Baba.”

Shigowar Umma Amarya ya katse hirarmu don kuwa dare ya yi nisa hakán nan shigowa ta yi da shirin kwanciya.

Washe gari kuma fitowa na yi ban ga Yaya Almu ba. Wajen karfe goma na shiga falon Baba, saboda na yi barcin safe, na gaishe shi na zauna nan muna karyawa. Ya ce mini, ‘Ai Lamido ya zo zai tashe ki wai ku tafi na ce mishi ai ko don dukan da ya yi miki jiya ba zan barki ki bishi ba kin ga kuma har yanzu labban naki a kumbure suke, ki rinka kiyayye maganar da za ki rinka gaya mishi, kin ji ko?”

Na ce mishi, ‘To Baba.”

Da La’asar sakaliya sai ga Yaya Almu ya dawo alamar dai yana-fitowaa daga kotu, arport ya je ya dawo

Lagos. Na kalle shi na yi murmushi, Baba ya taya ni murmushin, shi kuwa ya kule.

“Ai dariya ma kike yi mini?”

Baba ya ce, Za ta yi mana ai ba ka da jarumtaka ne na dauka fushin da ka yi da safe ba za ka dawo ba sai kwanaki bakwai din da nan diba sun cika.”

Yaya Almu ya sunkuya ya ce, ‘Baba sauran yan matan fa suna can suna ta shirye-shiryensu.”

Baba ya ce, ‘Haka ne to gobe in Allah ya kai mu sai ku tafi tare.”

Hankalina a kwance yake lokacin da na dawo gida, ba ni da wata damuwa cikin raina, sabdoa tsoron da nake ji din an kawar mini da shi, ni ce dai yar Baba ta asali ta cikinshi shi kenan bukatata ta biya. Yaya Almu kuwa na san shi ne mijin da ya dace da ni, zabin da Baba ya yi mini din zabi ne na tsananin kauna, zaton da nake ji cewar shi din uba daya mu ke shi ya hana ni yi wa kaina sha’awarshi, ko a hakan kuma ina kishin kalaman shi kan matar da zai aura. A yanzu kuwa son shi nake yi da iyakacin raina, illa iyaka dai na ki yarda in nuna mishi hakan.

A falon Umma muka fara sauka mun same ta da baki sosai, kawayanta ne da na dade da sanin su a duk lokacin da hidima ta taso mata, kuma sune farkon masu zuwa kan lamarin nata, don kuwa aminanta ne na kut da kut.

‘Ashe bikin Adawiyya ya tashi? Abin da sabbin shigowa falon suke gaya mata kenan.

“To wai ni Furera Adawiyya ce kawai za a yi bikin ta ne?

“Har da su Junaidu fa cikin masu aure nan.

“Amma bakwa ambaton kowa sai Adawiyyah.”

Umma ce mai, gayawa wata kawar tata haka.

Ta ce, ‘A’a to wannan ai ke ya shafa mu kam ai auran yar mu muka sani za mu yi bikin ‘yar fari kuma yar auta.”

Gaba daya suka kwashe da dariya.

“Kin fara tsuma mana ita kuwa? Don na san halin ki.” Umma Hauwa’u ce mai wannan maganar.

Irin wadannan kalaman sune suka yi sanadiyar fitata daga wurin Umma na ce bari in je in gaida Umma Karama da sauran mutanen da aka wajabta mini gaishe su a gidan. Sai dai ina shiga sashin Umma Karama na soma jiwo abin da ya birkitani ya fiddani cikin hayyacina, ya katse mini farin cikina, ya sani na Ji tamkar yawo nake yi a sama.

“Wai a kan wannan shegiyar ‘yartata.

To shegiya mana wane ne ubanta? Nan gidan ubanta ne?

Shi Lamido dama a mallake yake a hannunta, don abin da yake mata ya wuce biyayyaya tasan ma bauta daga kawai na ce ban yarda hadin da ya ce zai yi tsakanin Lamido da yarta ba, don hakan tamkar neman mallaka mata komai na shi ne tun da za ta mallaki Lamido shi kuma kamata ya yi a ce kowa na shi ne a gidan don haka Aina’u ce ta dace da shi, ita ce yar dangi ba wannan yarinyar da ba a san asalinta ba.

To ba a san asalinta ba mana, mene ne asalin na su da  Uwarta?”

Rantsuwa mai tsammanin karfi na ji Umma Karama ta yi kafin ta sake jaddadawa wanda take magana da shi din cewar ni şhegiya ce daka kawai tafi karfin Alhaji.

Dafe kirjina na yi da hannu biyu ina fadin, “Na shiga uku.” Na juyo da sauri na fita na nufi dakinmu zan je in dan kwanta in huta, saboda kai tsaye ba zan iya fuskantar Umma da wannan zancen ba. Ina tafiya inan kara jaddada mamakina game da hadani aure da yaya Almu da aka ce za a yi.

Ina shiga dakin mu na wuce Aina’u da Basira, na fada kan gadonmu na kwanta na dafe kaina, saboda sarawar da yake yi. Bayan na dan nutsa ne na ji hirar da suke yi sosai, ashe wai zancen Umman suke zai shi ya sa ba su samu damar amsa gaisuwar da na yi musu ba.

“Cikin shiege ina jin ta yi ta haife ta, tun da shi kam Baba ai kowa ya san yaya Aimu dan shi ne.” Maganar Basira ne wannan da ta yi matukar kashe mini jiki.

Tabbas in har za a cire mutum daya tsakanın ni da Yaya Almu a ce wane ne wanda ba Baba ne ya haife shi ba? To ina ganin kamar ni ce za a cire. Son kai ne kawai ya hana ni yin wannan hukuncin, to amma kuma zai yiwu a ce ni shegiya ce a ce ba a san asalina ba? Ina cikin wannan kidmane na ji Aina’u ta fige zanin gadon da nake kwance a kai tana tambayata.

“Kin shimfida gadon ne da kika zo kika hau kai?”

Na ce, ‘A’a amma ko ban yi shimfida yau ba ai akwai ranakun da nan ke yi, ban zo na kwanta akai ba. “

Ta ce, Ke kar ki kawo mini iskanci kin ji?” Ni uwarki ma yanzu ba girmanta nake gani ba, balle in ji tsoronta. Kan mu rabu kuma zan nuna mata asirin da ta yi wa Baba da Umma Amarya da su yaya Almu, ni bai kama ni ba, don haka daina nuna mana wata gadara, don an riga an yi iska abin kasa ya riga ya bayyana, mun riga mun gane nan ba gidan ubanki ba ne cikin she…”

Kan ta kai karshen maganar tata ban san yanda aka yi ba ganí na kawai na yi a tsakar gidanmu muna cin uban dambe ni da Aina’u. Na kuma san danben ne ya fito da mu daga dakin na mu. Damben mai tsanani ne sosai, don kusan su biyu ne a kaina.

Yaya Zubairu ne ya turo kofar wurin namu da saurin shi ya zo ya raba mu, na kalli Aina’u na ce, “Karya kike yi ki ce ba kya jin tsoron Umma don kuwa ko ni zan yi mata maganinki ba kuma ke ba na gaba da ke ma tafi karfin su.

Ke Adawiyya ku wuce mu je.”

Umarnin da yaya Zubairu ya bayar kenan.

Muna fitowa muka gamu da Umma Karama za ta shigo wurin namu, cikin sauri watakila labarin damben namu aka kai mata, shi ya sa ta zo da kanta.

Can wurimta yaya Zubairu ya kai mu. Muna shiga wurinta ta kalle su cikin takaici ta ce musu, “Ku biyu ita kadai amma ji abin da ta yi muku? Ji ki Basira, ji fuskar ki tabarya ta kwada miki ko?”

Ganin yaya Zubairu a bayanta ya sa ta yi maza ta yi shiru cikin jin kunya. Sai kuma ta shiga yin tada wai za ta ji abin da ya hada mu. Aina’u ta ce mata ji kawai ta yi kawai ta yi na rufe ta da duka. Ta ce, “Eh. to dole mana samun wuri ne kansa bako ya fi dan gida iko a gida.” Ta kalleni ta ce, “Amma ai kin san su Aina’u ko Sa’a sune sun fi karfin duka a wurinki, don su nan gidan ubansu ne, ke kuwa fa kina tambayar uwarki asalinki? “

Ban ji kunyarta ba na ce, Ba na tambaya ba kuma zan tambaya ba, don girmanta yafi gaban a tuhume ta, na kuma san inda duk ta samo ni ni ‘yar halak ce, don Umma ba ta yi kama da mai yin halin banza.” Ina maganar ina kuka sai na ji yaya Zubairu ya yi mini tsawa,

“Ke Adawiyyah kar in sake jin kin yi wata magana.”

Ta ce, ‘A’a kar ka ce za ka ce mata komai ni uwarta ce daidai da ni.” Tana fadin haka ta figi gyalenta ta wuce wai wurin Umma za ta.

Yaya Zubairu ya bi bayanta yana cewa, ‘Umma kar ki jc mata wuri ki yi hakuri ki dawo wurin ki.” Ba ta kula shi ba. Da gudu na wuce na tafi wurin Umma na yi sa’a duk bakin nata sun tafi kan ma in ce zan ce mata komai sai ga Umma Karama ta shigo. Wadansu irin maganganu take yi masu tsananin zafi da gore- gore wai tana rama zagin da na yi mata. Umma tana jinta ba ta daga ido ta kalleta ba, balle ta buda baki ta tanka mata, in banda da ta ga za ta nufo falonta na farko ta shigo inda take zaune ne ta ce mata, “Kar ki karaso nan, saboda ba na so ranki ya kara baci, in dai kika tsaya anan to za ki yi ki gama lafiya.”

“Me za ki yi?” Ta shiga dura ashar. Ana cikin haka sai ga su yaya Junaidu dukkansu sun shigo ga alama yaya Zubairu ne ya kira su.

Yaya Almu ya ce, ‘Amma Umma wannan abin ai shi ne abin da ba zai yiwu ba ko? A ce wata zata tashi ta je wurin wata ba don mu’amular arziki ba sai don ta je ta ci mutuncin ta, yanda babu mai yi miki haka. Hakan nan ba zai yiwu ki yi wa wata ba in Rabi ta yi miki rashin kunya, sai ki gaya mini don ba ki taba kawo kararta na kyaleta ba.”

A fusace Umma Karama ta ce mishi, ‘Ai lokacin ba ta gama da kai ba ne, amma yanzu da ta fara tura maka ita kuna kwana me za ka iya? Me zan ce maka jiya da shekaranjiya duk a ina ku ke? Ina ce kuna can küna holewarku.”

Ban san lokacin da yaya Almu ya sulale ya bar wurin ba, ya bar Umma Karar1a tana ta faman fadin maganganunta har ta yi ta gaji ta juya ta fita, saboda ta gaji da zage-zagen da take yi. Ba wanda ya tanka mata. Bayan fitar ta ne yaya Kabiru ya kalleta cikin sanyin jiki.ya ce mata, “Ki kara hakuri Umma.” Ta yi murmushi ta ce To ya ya zan yi? Ina na kula ta muka yi kuma ai ni ce a kasa, Adawiyya ce ai ta jawo jta ta yi mata rashin kunya.”

<< Wace Ce Ni? 16Wace Ce Ni? 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×