Yaya Zubairu ya yi maza ya ce mata, "A'a Adawiyya ba ta yi mata komai ba, Umma ke dai kawai ki yi hakuri."
"Ba komai." Umma ta ce da shi.
Da daddare rannan ina kwance a bayan Umma ita ta ce in zo in hau bayanta in kwanta. Ina kwance a bayan nata tana tambayata.
"Jikinki dumi Adawiyya ko ba kya jin dadi ne?" Na ce mata na yi kwance cikin ruwa mai zafi ne Umma.
A hankali ta soma yi mini hira cikin nutsuwa, "Sai kin zama jaruma kin zama mai hakuri kan zaman da za ki yi. . .