Tausayin Alhaji ya kamatá ta yi ta fadin magana, shị kuwa ko a jikin shi.
“Ginin nan fa kai kake bayarwa a yi. Sannan shi ga kasuwar da yake zuwa, yaushe ya je ya dawo ya zo ya yi aikin nan?” Duk bayanan da take yi Baba baya tankawa, sai dai ta yi ta gama ta yi shiru.
Ba a dauki wani lokacin da ya wuce sati biyu ba rannan da daddare sai Alhaji ya zo ya cewa Baba Rabi a gayawa Baba in ya yarda yana son fara aikin nan. Ta ce mi shi to. An bashi izinin farawa kuwa ya kama ranar da ya shata ginin, rannan Baba Rabi ba karamin fada ta yi mishi ba, akan me zai shata daki biyu? Wato ciki da falo, ana gane mishi wahalar aiki yana karawa kan shi.
Baba ya yi murmushi ya ce, ‘Dadina da ke ba kya iya ganin abu ki yi shiru, ai ba a kwacewa yaro garma, yi abin ka Bello ai kana da lokaci mai tsawo na yin aikin, ni dai na yi maka alkawari kana gama gininka zan ba ka matarka.”
Alhaji ya ce mishi, ‘To Baba.”
A haka Alhaji ya kama aikin nan. Ya kan kama aiki ne da sassafe daga fitowarshi daga sallar Asuba in rana ta yi kuwa sai ya bari ya yi wanka, ya tafi kasuwa. A haka cikin watanni biyu sai gashi har ya yi rufe, ya yi shafe da dabe, har ya sa rumfa a kofar dakin, ga Kuma dabe ko’ina, ga kuma wurin kewayawar shi can gefe shi kadai. Ya kuma kawayata wurin da shafen farar kasa.
Rannan da daddare Baba Rabi da Baba sunan hira ta ce mishi, ‘Ni mallam ba ka ga yaron nan ya gama aikin da ka bashi ba ne, ban ji ka ce komai ba?”
Baba ya ce, ‘Eh na gani ya yi kokari.”
Ta yi dariya ta ce, “In mutum ya yi dace yana da zuciya ai ya more, babu wani abin takaicin da zai dame shi, don haka sai ka cika mishi alfawarin da ka yi na bashi matarshi da zarar ya gama aikin da ka bashi.”
Baba ya ce,”Yanzu da damunar nan yaushe zan yi hidimar biki? Ai kuma sai da kaka.”
Baba Rabi ta ce, “Malam jiya ne fa aka yi ruwan farko. Habá malam kar ka yi wa yaron nan haka ka yi hakuri.” Tana fadin haka ta kama kuka.
Baba Rabi ta tasa Baba a gaba ya yi bikina a tsakiyar damuna, saboda mita kowanne lokaci, damunar nan ba ta hana babu komai ba, hidima sosai ya yi har da yanka saniya ya gayyaci ‘yan’uwa da abokan arziki sosai, duk da ni kadai ce za a yi bikin nawa, sauran yan matan da da za a hada mu da su gidajen mazansu sun ce su a yi musu hakuri sai kaka, ba za su yi biki da tsululun damuna ba.
Hidima sosai Baba ya yi tamkar dai bai taba aurar da wata ya ba sai a kaina. Dattawa abokanshi suka yi ta- zuwa mishi murna, shi kuwa sai cewa yake yi, “Ba na shekaru hudu kenan da kwanciyar malam Ali nima yawan rai ne ya sa na gani ban yi zaton hakan ba, gashi lokaci ya yi zan dankata ga mijinta ko da dai shekaru goma shadaya ne da ita. Cikin zuciyata tausayinta nake ji ba ta yi kwari ba, amma dai na sauke nauyin dake kaina.”
Su kuwa sai sukan ce mishi malam wannan yar taka ma ai babu mai cewa shekarunta kenan, in ba ka fadi ba, saurin girma ne da ita.
Daki biyun nan tam baba ya cika mini su da kaya. Gado biyu ya yi mini, a lokacin nan kuwa gado biyu sai ‘yar gata sosai. Aka yi mini jeren tasa mai Kadangare, a kanta daya-daya kantar kuam jeren kwanuka. Abin dai gwanin sha’awa.
A haka aka kaini dakina hankalina akwance ban san yaya auren yake ba. Na yi zaton canza mini daki kawai aka yi aka kai ni kayatacce. Haka nan ganin shigowar Alhaji bai tayar mini da hankali ba, saboda ya riga ya yi dabarar da ya ja hankalina zuwa gare shi. Sannan bayanin da baba Rabi ta yi mini kenan cewar canza mini daki kawai aka yi, amma gani ga ta ga kumababana, don haka kar in damu.
Na ce mata to. Kasa hakuri da ni da Alhai ya yi ne ya firgitani na tsorata kwai da shi na rinka gudun dakin, ina zuwa wurin Baba Rabi muna kwana tare. Tun tana cewa hau gado ki yi kwanciyarki ja’irin yaro kawai, wanda bai san bin al’amaria hakali ba, har ta gaji da kanta take korata ta ce ke tafi dakin ki bana son sakarci. Da ta fara korata sai na koma kwana cikin yaran gida sa’o’i na, ita da Alhaji su kwana suna nemana, sai da safe su ganni ba su san ta inda na fito ba.
Rannan ban san tunanin da ta yi ba sai ga ta ta shigo tana haska fuskokin mu da yar fitilarta tasa hannu ta kamo ni ta fito da ni su kuwa yaran ta bi su da sanda ta kwakkwada musu, wai gobe ma su sake barina na kwana a cikin su. Na dawo kwana a dakina kamar abin arziki, Alhaji ya fita harkata, gashi kuma kullum zai kawo mini abuuwa masu dadi iri-iri zai kuma zauna yana yi mini hira mai dadi, in ma na ce mishi zan je wurin yara mu yi tatsuniya sai ya ce mini, ai shi yafi su iya tatsuniya, in zauna ya yi mini. In na ce to bari in kira su ya yi mana tare sai ya ce wai a’a ni kadai zai yi wa su in suka zo tatsuniyar za ta bace. In ce mishi to ya zaunar da ni ya yi ta yi mini tatsuniyoyi masu dadi a duk lokacin da ya yi mini guda biyu zai ce nima, in yi mishi, sai kuma in yi mishin.
Irin wannan mua’amallar sai ta sa na sake sakin jiki da shi, sai dai bai, a je ko’ina ba ya sake tsoratani na koma guduwa, ina buya a bayan rumbu a yi ta nemana ba a gannina. Rannan da daddare Baba ya fito daga waje, rannan neman ya yi tsananí, shi ma da kan shi ya fito. Walkiya ce ta haskani ya ganni tsugunne a tsakanin rumbu ya tsaya yana kallona ya ce mini,
“Zo nan Zuwaira.”
Na fara kuka ya ce, “Ki yi hakuri ki fito nan ni kam ai ba zan ganki in mayar mishi da ke ba, ita ma Rabi da take yin hakan son rai ne ya sa ta take yin shi.” Ya shige da ni đakin shi yana fadin, “Wannan fitina ai tana da yawa duk dai laifina ne da na biye mata na bada ke inda na ki yarda ai da kina nan zaune cikin rufin a sirinki, hau gadon can ki kwanta.”
Na yi maza na yi hakan, shi ma ya bau na shi gadon ya kwanta. Bayan ya gyara wutar kaskon shi, saboda saukar ruwan sama, har dakin ya yi sanyi yana kwance yana fadin,
Ai wauta na yi na ba su ke da ban bayar ba da wanda ya isa ya yi mini wannan shakiyancin ban ci mutuncinshi ba?”
Kwana da kwanaki kowa ya san a dakin Baba nake kwana, babu wanda ya yi magana, saboda tsoro.
Rannan dai Baba Rabi ta zo ta mishi, “Ni malam wannan yarinyar ba za ta dakinta ba ne?”
Ya yi maza ya ce mata, “Eh ba za ta ba.”
Ta ce, to ai sai ta yi ta zama tun da ita daban ce da kowa, ita ba za ta iya hakuri da al’amarin mijinta ba, tun da tana da daurin gindin da za ta rinka, tona mishi asiri sauran matan da suke rufe kofa da nasu mazan me ya same su? Haka kawai za ta maida yaro ya zame mata abin tsoro kamar wani dodo.”
Baba ya ce, Dodo ne mana tun da bai da hakuri.”
Tun daga rannan kullum baba Rabi za ta sani a gaba tana yi mini nasiha.
“Haba Zuwaira ba za ki yi hakuri ki dauki lalurar mijinki ba? Yaro yana sonki kamar ya ya, amma kina ta faman wahalar da shi? Ina amfanin wannan abin da kike yi? Ina amfanin a ce in zai taba ki gabanshi ya ringa faduwa kenan, saboda ya san za ki yi mishi kwakwazo a cikin jama’a? Mutanc suna ji sun san halin da yake ciki ke ba za ki rufá mishi asiri ba ne? To ba na so kar in sake ji ai ke matar rufin asirin shi ce, kar ki yarda a rinka jin tsakaninki da mijinki kin ji ko?” In yi ta kuka don na san karshen maganar tata dai maida ni za ta sake yi.
Shekaru biyu kacal da zaman mu sai na yi wani irin girma na bam mamaki, babu mai cewa shekaru goma sha uku ne kaca da ni a duniya. Na yi kyau, na yi fari, ga mijina jarumi kowanne lokaci a cikin sai mini kayan ado yake; man shafawa kuwa bana shafa bude da kwabo, sai mai gurguwa shi ma sai ya kwaba mini shi da zaitun da habbatus-sauda ga turaruka na almiski nima kuma gani da tsafta kullum zan yi kitso in yi lalle, kafa da hannu gwanin sha’awa.
Tun a lokacin nan na soma samun matsala tsakanina da matan yayyen Alhaji, wadanda suka yi matukar sanya ido kan al’amarina da mjina in ji su wai bai yin komai sai da yardata da magana ta kai kunnen Baba Rabi sai ta ce da su, “Ku ma ku je ku yi wa na ku mazan haka ai ba hanaku a ka yi ba; yarinyar da aka rena a gabanku shi’ ne har kun fara maganarta in ban da abin da alkunya? “
Rannan Alhaji ya dawo da yamma muna daki tare da shi, ina kwance a jikin shi don ya riga ya sabar mini da irin wadannan abubuwan. Ya kalle ni ya ce mini, “Ni fa Zuwaira ina son fita daga girkin gidan nan, ba na son shi in na fita za ki iya daukar dawainiyar mu ko?”
Na ce mishi, “To.”
Ina soma yin girki na soma shirya wa su Baba gara kullum cefanen Alhaji mai kyau ne, gashi dama na riga na saba da aiki na kuma iya girkin ko da yake baba Rabi tana cewa wai bai war girkin ne da ni, don komai na yi mai dadi ne. Kullum zan gama girkina da wuri in na gama in kai wa kowa na shi, na su Alhaji a dauka a kai sashin yaya babba, don a can suke haduwa su ci. Nima in je mu ci da matan gida bayan na kai wa su baba na su. Muna gama cin abincin, zan dawo in zo in juye ruwan wankana in yi, in yi kwalliya saboda Alhaji ya hanani zama hira a cikinsu, In ji shi wai duk sun haife ni bai yarda in rinka wani hira da su ba, tun da dai sun ce mu ci abinci tare, to muna gamawa in kwashe kwanuka in tashi. Hakan nan kullum na gama girki in yi wanka don bai son warin hayaki, na ce mishi to.
Wadannan abubuwa biyu sai suka kara tsananta bakin jini na a wurinsu, wai ba na zama a cikinsu na dauki kaina daban, gani nake tamkar na fi su, bayan ni din ba komai ba ce in ban da daure mini gindi da baba ya yi, ya fifitani akan kowa, ya sa nake raina mutanc. Kuma wai’ni na cika son miji fitina ce da ni, ba na barin shi ya huta kullum ina makale da shi, don fitina ma wai kullum sai na yi wanka da daddare. Kan wadannan maganganun na su sai na rinka kin yin wankan dare, nan abin ya rinka hadani rikici da Alhaji har rannan ya kai ni kara wurin Baba.
Na je wurin baban hira kamar yanda na saba yim kullum, don ban taba fasa zuwa mishi hira ba. Kullum zani mu yi hirar mu ni da shi da Baba Rabi, shi ma Alhaji yana yin tashi hirar wurin yayanshi sai dai bai dadewa in ya dawo ya dade yana jirana ban dawo ba, in na shiga ya yi ta mita yana fadin zai dauki matakin hanani barci a duk ranar da na je na dade wurin hirar tun da ban san ya kamata ba.
Ina zaune muna hira da baba ita kuwa Baba Rabi tana sude kwanon romon kaji da na kawo musu, ta lashe hannunta ta mutstsuke su tare tana cewa, To Alhamdulillahi Allah ka yi wa Bello albarka ka yalwata mishi arzikinshi ka bashi ikon ciyar da jama’a.”
Baba ya yi murmushi ya ce, ‘Ita kuma mai girkawar fa?”
Baba Rabi ta ce, ‘In Bello ya yi albarka ai ta yi”
Ya yi maza ya ce, ‘A’a ban yarda ba, rinka yi mata tata addu’ar daban.”
Ta yi dariya ta ce, ‘To Allah ya wadata ta da hakuri ta zame mishi uwar iyali.”
Ya ce, To amin.” Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, “Mijinki ya kawo mini maganarki ko da yake bai gaya mini laifin da kika yi mjshin ba, nima kuma ban tambaye shi ba, amma ya ce mini ba kya jin maganar shi kin fi jin tsoron matan gida akan gudun bacin ranshi, haka ne?”
Na soma yin kuka. Baba Rabi ta ce, “Tana nema ne ta zama sakarya tana nema ta biye wa kazantarsu, kwanannan ba ka ga ba ta wanka ba?
Saboda suna cewa son miji ne yake sata wankan dare.”
Baba ya ce, ‘Ashsha! To ina ruwanki da su Zuwaira? Mijinki kuwa ai shi kika sani abin da ya ke so kuma shi ne abin yin ki, ki kuma guji bacin ranshi, tun da shi ma yana kiyaye kan shi, ya kode a jikinki kar kuam in sake jin ya ce mini ba kya jin maganarshi, yanzun nan ma ki tashi ki je ki yi wanka, kar kuma ki dawo mini hirar sai gobe da safe, don nima kwanciya zan yi in ban da sakaran namiji wa zai yarda da mace tana dankon kazanta? Me mijinki ya rage miki da ba za ki yi mishi yanda yake so ba?
Na dawo dakina na yi yanda Baba ya ce mini.
Na gama shafa ina kokarin sanya sabbin kayan da na fito da su, sai ga Alhaji ya shigo cikin murmushi ya ce, To sa kayan me kuma za ki yi yanzu da daddaren nan?” Ban kula shi ba, zan ci gaba da sanya rigata ya yi maza ya kulle kofa ya iso gare ni.
A wannan lokacin ne na samu kaina cikin wan yanayi na rashin jin dadi, kowanne lokaci ina kwance ba ni da kuzari ga barci komai ban iya har salla ma.
Kowanne lokaci Alhaji cikin mita yake.
‘Wai ke me ya same ki ne?
Kullum tambayar shi kenan In ce mishi ban sani ba, ba na dai jin dadi kawai. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, To ko dai kina yawan tunawa da Baban e tun da dai ni ban ga alamar rashin lafiya a tare da ke ba, kin ga yanda kika kara kyau kike wani sheki kuwa?” Na ce mishi ba na zaton tunawa da Baba ne tun da dai ai ban taba ma mantawa da shi ba, kullum ina yi mishi addu’a. Ya ce, To bari nan da kwana biyuu in bai daina yi miki ba zan san abin da zan yi a kai, ni in banda tsoron su Baba ma ai da asibiti na kai ki. To sai su ce mene ne dalilin zuwa asibitin?” Na ce haka ne.