Skip to content
Part 26 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Umma ta mike ta dauko rigar baccin dake ajiye can gefenta ta miko min.

“Karbi ki suturta jikinki.” Ta yi maganar ba tare da ta kalle ni ba.

Hannu biyu nasa na karbi rigar nayi yadda tace din, tana ganin nayi hakan ta nemi wuri ta zauna tana kallona cikin natsuwa ta ce “menene matsalar da ta hanaki zama wurin mijinki ku more darenku na farko?”

Nayi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda jin nauyin maganar tata, gaba daya mukayi shiru na dan wani lokaci zuwa can sai na kawar da shirun namu ta hanyar yi mata tambayar taimake ni mana Umma yau kam ki gaya mun gaskiyar al’amarina taimake ni ki gaya mun don in san ni wacece?” Kallon da naga tayi min shi ne ya firgita ni, nan da nan naji cikina ya bada sautin kululululu….

Cikin rawar jiki na tambaye ta “Da gaske ne Umma ni din shegiya ce?” Ta dan girgiza kai a hankali tare da fadin cewa “ko kadan ke ba shegiya ba ce Adawiyya.” Na dan samu ‘yar natsuwa kadan saboda jin abin da ta fadi, don haka sai na dan kara matsawa jikinta na ce, “Gaskiya Umma ke din ke kika haife ni?”

Na zuba mata ido ina kallonta tare da sauraron irin amsar da zata bani, sai na sake ganin ta motsa kanta.

Da hannu biyu na bugi kirjina cikin tsananin kuka na ce mata “Na shiga uku Umma, tunda ba ke kika haife ni ba?” Na kama kuka mai tsananin yawa ina fadin “Shi kenan Umma ta rasa ku dukanku na rasa Baba kema kuma a yau na rasa ki bani da kowa kenan a duniya?”

Umma ta jawo ni jikinta ta rungume itama taya ni kukan take yi tana fadin “Ba ki rasa kowa ba Adawiyya, ni da Alhaji mune iyayenki da kika sani mune kuma iyayenki na har abada, ban taba tunanin hali zai yi da zan bayyana wannan sirrin ba in banda tsananin son da nake yiwa Babangida, da ban bari akayi aurenku ba, don nasan yin auren naku yana nufin bayyanar asirin da na dade ina boye miki.

Na sake kallon Umma a kidime na ce mata “Umma amma ai dake nake takama, gashi kuma a baya kin taba ce min kin haifi Rabi’atu kin kuma gaya min cewar Umma amarya tazo gidan nan da yaro a goye to ina ce shine yaya Almu?”

Cikin natsuwa Umma ta kalle ni ta ce min, wancan yaro da na ba ki labari tuni dangin Ubanshi suka kar ba, duk da Alhaji yayi iyakar kokarinshi wajen ganin an bar mishi rikon shi amma basu yarda ba bisa uzurin da suka bayar na cewar shi kadai ne dan uwan nasu ya rasu ya bari maganar haihuwar Rabi’atu kuwa biyo ni kawai kisha labari, a baya na tsaya ne a inda na gama baki labarin isowar Maryam gidan nan to yanzu ma daga nan zan tashi.

“Isowar Maryam gidan ya saman min da saukin fitina ne, amma ba fita hanyata karama tayi ba, domin duk da amaryar da akayi mata kishinta yafi tsanani a kaina, don ita da bakinta sai da ta rinka gayawa mutane cewar da ta zauna dani a matsayin kishiyarta gara ta zauna da kishiyoyi guda uku duk da ita su zama hudu.”

Umma ta dan saki wani lallausan murmushi bayan fadin hakan da tayi. Sai kuma ta ci gaba da fadin “Babu abin da karama ta ki irin taga Alhaji a dakina koda kuwa nice dashi sai ta rasa kwanciyar hankali ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi muna cikin wannan zama ne mutancen gida suka gane ai Amarya ciki ne da ita, shi kenan ana gane hakan sai kuma kishin Karama ya kema can zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu fadan safe daban na yamma daban bayan kafin ta gane Maryam na da juna biyu duk kokarinta bai wuce na ace su biyun sun hade mun kai ba, ita Maryam din ce bata yarda ba rikici tsakaninsu yayi tsanani ‘yar magana ba magana ba kumą sai ta rarumeta da danbe sai da Baba ya gaji da hakan yasa baki yayı kashedi akan danben shine aka dan samu sauki.

Ni kam ina gefe kallonsu kawai nake yi ina kuma iya kokarina wajen boye halin na nake ciki saboda ban son a gane amma duk da yake sai da Alhaji da Baba suka gane ina zaune a kan tabarma a dakina rannam ina dama wa Alhaji furar da zai sha bayan dawowarshi daga kasuwa, sai ya kalle ni ya ce min “iko sai Allah, watakila kuma bana yan tagwaye zan samu a gidannan da kuma shekara da shekaru babu ko daya.” Na yi kamar ban ji shi ba, na mika mishi furarshi ya kama sha.

‘Yan kwanaki kadan bayan bayan nan kuwa ina tare da Baba muna hira sai ya ce min “to wai ni Zuwaira da kike ta faman wannan boye-boyen kin mance ne uwarki mai yi min lissafin cikinku yau bata nan? Na sunkuyar da kaina kasa cikin hawaye saboda na kasa daina kukan mutuwar Baba Rabi kullum cikin kewarta nake, anyi wannan zancen babu wani dadewa sai kawai na haifi ‘ya mace abin da ya baiwa kowa mamaki har Alhaji da Baban da suka gane akwai cikin balle kuma wadanda basu gane ba a wannan lokacin yaya Balki ce ta tsaya akan hidimar jegona don gaba dayan matan gida sun ce babu hannunsu tunda dai na boye musu cikin don ina tsoron kar suyi amfani da maitarsu su cinye abin da yake ciki to yanzu ma da ya fito ba za su taba shi ba don haka ita ce mai samun ruwa ta kwashe ta wanke yarinya ta gasa mata cibiya ita kuma Maryam tana yi mun wankin kayana da na yarinya dama duk wani aiki da ya dangance ni.

Ranar suna Baba ya sanyawa yarinya suna Rabiatu, a wannan loka cin ba karamin karamci yaya Balki tayi min ba don kuwa har nayi arbain ita ke sanya mun ruwan wanka ta kwashe ta yiwa yarinya wanka safe da yamma bata yarda ta bari ba kamar yanda Alhaji ya ce ta huta da ji da hidimar yaran dake dakin ta wajen su bakwai ga guda biyu da ta haifa a kurkusa wadanda basa yarda su rabu da jikinta ko ina take suna manne da ita uwa da kuma Junaidu.

Ba zai yiwu in tsaya kwatanta miki irin son da Alhaji da Baba suke wa yarinyar nan ba illa dai kawai in ce miki ba al’adar mazan gidan ba ne daukar ya’yansu amma shi kam daukarta yake yi ya fita da ita ya kaita wurinta Baba suyi hira in kuwa ya ganta a bayana tana kuka ko ya ji ta zai ce min ban ita nan, ko da kuwa a cikin mutane ne nayi-nayi ya daina don ina jiye mishi kunyar hakan da yake yi,amma ya ki dainawa

Sai ya ce “ke kyale ni kin hi shekara nawa nayi ban same ta ba?”

Mun samun wajen watanni uku a lokacin nan tafi wani jaririn mai wata biyar girma da kuzari gata da idanuwa dara-dara gashi ba na jin kunyar gyarata kullum cikin tsabtace ta nake sai kawai ta kamu da mura mai tsanani na wuni daya kawai sai kuma ta ce ga garinku nan.

Baba ya yi ta kuka ina bashi hakuri shima Alhaji ya shiga cikin damuwa mai tsanani kowane loka ci sai yayi ta fadin “oh ashe yarinyar nan ba zama tazo yi ba?” In dan yi murmushi in ce mishi “I, ba mai zama ba ce sai kayi hakuri ya ce to yaya zanyi? Ni kaina boye damuwa kawai nayi amma zuciyata takai matuka wajen zafi, don kuwa ina son da a wannan lokacin ban sani ba ko Baba ya gane hakanne sai ya ce min dakin nan naki zaiyi miki fili mai yawa na rashin Rabi, koda take yar karama kin riga kin sa rai da ita. Don haka ki dauki Uwa itama wata Rabin ce sai ta rufa miki gurbin da ta bar miki.” Nayi nurmushi na ce “To Baba daga wannan ranar kuwa sai na karbi rikon Uwa daga wurin Yaya Balki hakan kuma sai ya kara karfafa kauna mai yawa a tsakaninmu har muka zama tamfar ‘yan uwa.

Sati uku cif da rasuwar Rabi’atu sai Maryam ta haifi da namiji na kai wa Baba shi, bayan nayi mishi wanka ya kare mishi kallo ya ce “kamarshi, daya da ‘yar uwarshi da mace ne da sunanta na mayar mishi sai ki sa hannu biyu ki rike shi naki ne ki dauka shi da ‘yar uwarshi da ta tafi duk daya ne tunda ‘ya’yan Bello ne na ce “mishi to Baba na karbe shi na tafi na bar shi yana share hawaye da gefen rigarshi ni Baba ya taya ni fadi sunan da nake so a sanyawa jariri na ce’ yasa mishi sunaishi don haka ranar suna sar aka rada mishi Muhammadu Mustapha ni, nake kiranshi Babangida shi kuwa Baba yake ce mishi Lamido.

Hannu biyu na saka na karbi al’amarinshi tun yana dan jariri na kai kai shi gun Maryam ne kawai don yasha nono, tunda Junaidu yaga jariri a dakina kullum zai zo ya zauna kusa dashi dama kuma ga Uwa ta dawo dakin don haka sai ya zama dare ne kawai ke raba shi da dakin daren ma kuma sai an bari yayi bacci nake kai shi ko kuma ita ta turo a dauke shi. Rannan ma dai da Alhaji ya gaji da ganın hakan sai ya ce min to wai ke me zai sa ba za ki bar yaron nan a dakin nan ba ne kawai ki hada su ki rike? Ina amfanin kullum sai an sako shi a dauke shi?” Na ce mishi to.

Shi kenan sai gani da ‘ya’ya uku a daki ina kuma tafiyar da al’amarinmu gwanin sha’awa kowane lokaci muna cikin tsabta ko hira zani wurin Baba tasasu a gaba nake yi in tafi dasu, don nasan hakan yana faranta mishi rai.

Kullum naje gabanshi tare da su kuwa sai ya gaya mun cewar wadannan yaran da kike gani naki ne sun kuma ishe ki kar ki yarda ki daga hankalinki don ganin wai baki haifa ya rayu ba, kowa da kike ganin yana da irin jarrabawarshi in kuma kayi hakuri to da irin sakamakon da za’ayi maka in ce mishi to Baba.

A wannan lokacin ne Alhaji ya soma yi min magana kan sha’awar da yake da ita ta fara yin kasuwanci zuwa wasu garuruwa yana min bayani kan muhimmancin neman halal, na ce haka ne ko kuwa ba kya son hakan?” Nayi maza na ce “A’a ai ni ba zan ce kar ka nemi arziki ba.”

Ya ce”eh na sani Zuwairah, shi yasa na gaya miki don ki taimake ni wurin Baba ya barni in fara don nayi mishi magana bai amince ba, kuma ya ki amincewar ne a dalilin wai ba ki da kowa sai ni sai ko shi in na fara tafiye-tafiyen wai zaki yi kewata da yawa gara sauran matan su suna da dangi anan kusa. Bayani mai tsawo yayi min cikin rarrashi da kamun kafar in sa baki Baba ya amince mishi da bukatar tashi har yana yi min alkawarin wai ba zai rinka yin tafiyar yana dadewa ba, ban ce mishi komai ba ha rya yi ya gama yayi shiru ban tanka ba saboda nima can Cikin zuciyata nasan zanyi kewarshi amma kuma duk da haka nayi mishi yanda yake so din wato in rokar mishi Baba cikin natsuwa na same shi nayi mishi bayanin ya daga ido ya kalle ni cikin kulawa ya ce “tausayinki nake ji Zuwaira, in har ya dandani dadin neman kudi a nesa da gida zai yi wuya ya dawo gidan ya zauna, amma tunda kin ce a barshi yaje shi kenan.”

Alhaji ya soma tafiya Fatauci daga gida zuwa garuruwa daban-daban na kurkusa, wani lokaci yayi kwana biyu ko uku ya dawo gida.

Ana nan ana nan sai gashi in ya tafi sai ya kai har kwana ashirin bai dawo ba, in na zauna wurin Baba ina lissafin kwanakin tafiyar tashi sai ya ce, “a to, abin da na gudar miki kenan, kika ce a barshi ganewan da nayi shima Baba ba jin dadin dadewan nashi yake yi ba, sai na daina yi mishi zancen nayi kokarin kawar da damuwar kewarshi cikin raina, nayi matukar kokarina na maida hankalina kan al’amarin ‘ya’yana wadanda suka riga suka fara girma suka yi wayo, nake matukar jin dadin mu’amalla dasu saboda tsananin son juna da muke yi suna sona saboda suna daina buya in yi kukan kewar Alhaji saboda in har Uwa ta gane nayi kuka ta rinka kuka kenan saboda ita din tafi su wayo.

Ina cikin wannan zaman da yaran ne rannan Alhaji ya dawo gida a dakina ya sauka. Bayan al’amura masu yawa sun gudana a tsakaninmu, muna cikin hira sai ya sako mun wani zance da ya shafi harkokin kasuwancinshi irin alherin da yake samu da yanda kasuwa ta bude mishi, na taya shi murna har cikin zuciyata, sai kuma ya ci gaba da cewa “to kin san halina Zuwaira, babu wani al’amari nawa da yake boye a gare ki bana son zaman takura da kewa, don haka nace wannan karon in zan tafi tare dake zan táfi don na gaji da zaman kadaici.”

Maimakon in ji dadin wannan bayanin da yayi min tunda dama cikin kewarshi nake, sai na kasa yin farin ciki a dalilin ganin ya’ya uku dake kwance akan karamin gadona suna bacci, wadanda basu san kowa ba sai ni ko dawowa suka yi daga Makarantar allo basu ganni ba basa iya jirana in dawo sun rinka shiga sashi-sashi kenan suna nemana, ga kuma Baba wanda girma ya riga ya kama shi ni ce mai hidimarshi nice abokiyar hirarshi to tsallake su duka zanyi in tafi ko kuwa yaya zanyi?”

Da na kalli Alhaji sai kawai na kawar da fuskata gefe nace ‘mishi “ba zani ba.” Amsar da na bashin yayi matukar bashi mamaki, don ya saba yi ne ina ce mishi duk abin da ka gani.

Cikin natsuwa ya mike ya zauna yana kallona da fuska mai dauke da alamar mamaki cikin muryar da ya tausasa ya ce min “kin zartar wa kanki da hukuncin rashin bi na?

Ban tanka mishi ba ban kuma bashi hakuri kan hakan da nayi ba sai dai nan take naji babu abin da nake son yi irin in yi kuka kukan kuwa nayi tayi yayi rarrashi har ya gaji ya ce min “haba Zuwaira me nayi miki da zafi haka? Ina ta baki hakuri kin ki ki hakura ko so kike sai yaran nan sun farka sun ganki kina kuka sun ji zafina tunda zasu ga na batawa uwarsu, bayan ni ba ma samun zama cikinsu nake yi ba?” Yana fadin haka nayi shiru na bar kukan, sai dai kuma har gari ya waye ban sake tankawa wata maganarshi ba, abin da bai taba faruwa a tsakaninmu ba. Don haka sai hankalinshi yayi matukar tashi da abin da nayin.

Gari na wayewa na anmsa kiran Baba saboda ya kai maganar gabanshi. Ya gama baiyanawa Baba maganàr da ya ce ba a kara ba kan wannan ba, ba sai kawai naga ta kama kuka bayan ni da ta yiwa laifi ban nuna bacin rai ba.

Baba ya gyara zama yace, “to yaya zaka nuna bacin rai bayan abin da kake so tayi maka? Ai dole Zuwaira tayi kuka tunda ta gane duk abin da kake nufi bai wuce son ka kwashe matanka ka tafi dasu ka barta ba, tunda su biyun dai babu wadda zata yarda ka dauki ‘yar uwarta ka barta to kaje ka dauke su ka bar mu a nan.

Hannu biyu Alhaji yasa ya dafe kanshi saboda tsananin tashin hankali bai taba zaton abin da Baba zai gaya mishi kenan ba, nima kuma nayi mamaki yanda akayi ya gane abin da ya darsu mun cikin zuciyata.

<< Wace Ce Ni? 25Wace Ce Ni? 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×