Skip to content
Part 28 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Har na soma jin sauki ina fitowa tsakar gida ina dan taimakon yaya Balki da ‘yan ayyuka tun tana hana ni har dai ta hakura ta barni.

Rannan ina kwance a daki da ‘yan yara guda uku da suke ta bacci yayin da ni kuma nake kwance idona biyu saboda tunanin rayuwa.

Baba nake tunawa da kalmominshi da yayi tayi min musamman na karshen rayuwarshi wani tunani yazo min cikin raina da wannan zaman kadaici da nake yi ga wulakanci daga wurin mutanen gida gore-gore da habaice-habaice wuni nake yi a cikinsu, ga Alhajin ma yanzu rabon da in sa shi a idona har na mance lissafi me zan hana kawai in yazo in ce mishi ya kaini wurin dangina sai kuma na tuna maganar Baba nayi kuka har na gaji daga karshe dai na yankewa kaina hukuncin zama Jaruma da kuma bin dukkan shawarwarin da Baba yayi ta bani. Don haka washe gari da sassafe naje na gaida Yayan tudu na shaida mishi cewar tunda naji sauki ina so zan koma wajena, ya ce kin ji sauki tunda kin mike daga kwanaya, amma ai ba ki warware ba kin ganki kuwa kinga irin karewar da kika yi?

Na ce ba komai ina so in koma can din ya ce to babu laifi.

Ina gayawa yara zamu koma wurin mu suka yi ta murna nan da nan muka gyarashi muka koma ciki na kawar da kaina kan abin da ake yi a gida ko ina ji ana magana ta ban nuna nasan dani ake yi balle in tanka, na maida hankalina wajen saye da sayarwa wanda dama na fara tun Baba yana da rai, mutanen unguwa ma in zasu sayar sai su kawo min in suna bukata ma su zo wurina nema na maida dakin Baba da.dama ya bani wajen tara kayayyakin da nake sayarwa ina dan harkokina ga kuma ‘yan dabbo bina da nake kiwatawa wadanda suma babanne ya kafa min tushensu sai dai kuma duk da hakan bana cikin jin dadi zuciya ta a kuntace take kewa da kadaici sun ishe ni.

Ana cikin haka rannan sai muka wayi gari da safe Uwa ta dauki dusar shanu taje zata share musu wurin ta zuba musu sai gata ta dawo da gudu tana kuka tana fadin Umma zo ki gani, da sauri nabi bayanta sai kawai na hango bijimina babban a kwance an yanka shi daga nesa na kare mishi kallo tausayinshi ya kama ni na juyo kawai na dawo nazo naci gaba da aikina, ita kuwa Uwa taje sashin yayan tudu ta fada, ya shigo yayi min jaje ya kuma tambaye ni saidawa za’ayi don a rage asara ko? Na ce mishi a’a a rabar dashi kawai sadaka, su kuwa sauran dabbobin a tasa su a gaba akai su kasuwa a sayar, ya ce eh to kin yi dabara ba zan ce ki barsu ba, don kar abin da ya samu sauran ma ya same su, in banda yaya Balki ba wanda yayi min jajen abin da ya faru, an dai basu sadakan nama sun cinye, sai da aka fitar da dabbobin nan daga wurin nan sai kuma na kara gane ashe suma suna debe kewa ashe ba karamin sabo dasu nayi ba a yanzu sai inga tamkar bani da aikin koma ga kuma yara kullum maganar su ba ta wuce Allah sarki shanunmu da yanzu suna nan da munyi kaza da kaza.

Ba’a kwana talatin da faruwar wannan al’amarin ba, rannan sai na farka cikin dare firgice saboda ihun da nake jiwowa na gobara-gobara, da sauri na dauki Babangida na goya na daure shi tamau a bayana, na dauki Junaidu na kankame sannan na kama hannun Uwa na rike don ban san ta inda wutar take ba, sai da muka fito ne naga ashe dakin Baba ne yake cin wuta, dakin da nake tara dukiyata. Muna tsaye muna kallo dakin yayi kurmus sai dai maimakon wutar ta tsaya anan abinka da jinkan ciyawa sai da ta lamushe kusan rabin gidan, da kyar aka samu aka tsaida ita.

Washe gari bayan an dan natsa yaya Balki tazo min hira tana kara jajanta min abin da ya farun, tana bani hakuri na ce mata ai ni tun bayan mutuwar Baba ban sake ganin wani abin da ya bata min rai ba, komai aka yi sai inga wasa ne, wannan bai kai ayi bakin ciki dominshi ba. Allah ya jikanshi ya saka mishi bisa rikon amanarshi tace min amin.

Tun daga wannan lokacin na bar komai na bar kowace irin sana’a don kuwa na gane hakan zai iya jawo min kowane irin abu, shi kenan na zama bana komai in na gama ‘yan ayukana sai in dauko ‘yan littattafaina guda biyu da dama Baba yake koyar dani na Kawa’idi da Ahlari, inyi ta karantawa in na kamo daga farko na kai karshe inyi ta maimaitawa daga baya ma na shiga koyawa yara. Wasa-wasa sai gashi mun sauke kawa’idin da su min shiga Ahlari.

Muna nan a wurinmu rannan da daddarc sai kawai naji muryar yayan tudu yana tashina, jikina yana rawa na fito ya ce min taso yaran nan ku dawo nan ku rinka kwana, na ce to na kwaso yara nabi bayanshi zuwa dakin yaya Balki, can ya maida mu. Washe gari da safe kwaso yayi min magana da cowar in yi hakuri in zauna a nan don hankalinshi ya kasa kwanciya da zaman nawa a can, na ce mishi to. Wannan lokaci na zama wata irin abin tausayi ban san menenc matsayina ba, babu Alhaji babu dalinshi, matanshi ma Sun daina zuwa gida a shekara biyu da rasuwar baba ganin da nayi mishi tunda akayi arba’in bai fi sau uku ba, ga abubuwan da suke kewaye dani a gida irin mutanen da nake zaune dasu ga aiken da yake yi min ma ya daina ga abin hannuna babu ya kare don ma dai yayan tudu yana yi min kokari to shima kuma ba mar shi bane ga kuma iyali har mata uku da ya ya.

Muna wannan zama rannan kwatsam sai ga Alhaji ya iso da yamma, cikin wata irin kwalliya ta ban mamaki da burgewa, ana tayi mishi oyoyo ni kuwa nayi maza na shige wani dan daki na buya in ban da Uwa ta biyo ni ta kira ni da ban san yanda za ayi in fito ba, na same shi a dakin da aka sauke shi saboda umurnin da yayan tudu yayi min inje mu gaisa, na ce mishi to, na tali tare da yaran dukansu ya daga ido ya kallc ni ya rage fara’a ya ce yaya zaki zo min da yara kuma bayan su na riga na gansu Ban yi magana ba ya ce musu kuje gun yara kuyi wasa, suka ce to suka fita. Na sassauta murya na gaishe shi cikin ladabi ya amsa na tambaye shi iyalinshi ban kara ba akan wannan naja bakina nayi shiru, ya ce min yaya akwai mas’ ala ne haka naga gaba daya kin canza? Na hadiye bacin ran da tambayar ta sanya ni na ce mishi babu komai, ya ce to in babu komai ni gobe zan koma dama zuwa nayi in ganku na ce mishi to Allah ya kaimu na tashi na dawo daki na zauna ina tunanin irin canjin da na gani a tare da Alhaji, ya yi kyau yayi kwarjini bai bukatar cewa ya samu daula don jikinshi ma ya riga ya bayyana na kalli kaina naga yanda na zama na fige nayi muzai-muzai in ba wanda yayi min kyakkyawan sani ba sai yayi zaton shekaruna sun zarce yanda suke bai bukatar komai a tare dani bai sona ba ma zai lya nuna ni a yanzu ya ce nima matarshi ce ba, to me zai hana ya kaini wurin’yan uwana? Nayi kamar inyi mishi tuni kan ina da ‘yan uwa me zai hana ya kai musu ni maimakon barina cikin nashi ‘yan uwan da yake yi, sai kuma na tuna kalaman na tuno shi a hirarmu ta karshe yana cewa mahaifinki yana sane da danginshi ya bani amanarki, don haka ke din tawa ce kiyi hakurin zama a cikin ‘yan uwanki in hali ya samu sai kije ki gano su, don sadar da zumunci. Hawaye suka zubo min a ido, saboda tuna Baba da irin son da yake yi min da nayi.

Uwa ta shigo dakin da sauri tana murma, “Umma wai kizo in ji Baba.” Tamfar dai in ce mata ba zani ba, sai kuma naga ba zan iya ba na tashi na bi bayanta na sake shiga dakin da yake cikin na durkusa na ce mishi, gani ya zuba min ido yana kallona ya ce so nake in tambaye ki Zuwaira, kin daina sona ne? Lokaci mai tsawo baki ganni ba amma ki nuna min baki da wata bukata game dani, na kuma tambaye ki damuwa kin ce baki da ita, me kike nufi dani ko kuwa kin zuba min ido ne kina jiran ganin sakamakon da Baba ya ce miki zai same ni in har na zaluncee ki?”

Na ce mishi a’a, bana neman sakamako a kanka ba ma kai ba da kake da matsayi mai girma a kaina, duk wani wanda ya danganci zuriyar baba bana neman sakamako a kanshi ko da kuwa me yayi min, na yafe mishi zan kuma ci gaba da yafe wa bayanin nawa yayi mishi dadi ya ce to amma in haka ne me yasa ba ki tambaye ni dalilin rashin zuwana ba? Na ce nasan ba zaka yi hakan da gangan ba.

Yayi murmushi ya ce na gode miki Zuwaira da ba ki kullace ni ba, kika kuma zama ma yafiya kan duk abin da ya same ki, bayan haka ina so in tabbatar miki da cewar ban taba yin wani abu da nufin in zalunce ki ba, ina kuma son ki fiye da duk yanda kike zato ina son hakurinki, ina son dabi’arki ta girmama wanda yake gaba dake duk abin da kika ga nayi to na yi shi ne bisa hakan ya zama min dole in har akwai wani abin da yake bani tsoro a yanzu bai wuce zaluntarki ba, don kullum ina tuna kalaman

Baba na įaddada min amanarki da zai bar min wannan dadewa da kike gani ina yi bana zuwa ba na kusa ne na tafi nema bana cikin kasa a yanzu kuwa na gama shirya miki wurinki ke da ‘ya’yanki don haka nazo ne in tafi dake.

Ban ce mishi komai ba har yayi zancen shi ya gama na tashi na tafi nayi, kwanciyata washegari nazo zan gaishe sh1 sai na same su da yayan tudu bayan na gaishe su zan tafi sai Alhaji ya ce min ke Zuwaira! Na ce mishi na’am, sai ya ce ga dukiyarki yaya ya kawo min kudin shanunki da ya sayar ya kuma juya miki su sun karu shi ne na ce maimakon in karba ko zan bar mishi ne ya ci gaba da juya miki ko? Na ce mishi to, na tashi na tafi.

Washegari ne kawai muka kamo hanya don ban tsaya kintsa komai ba, Alhaji ya ce ni da yara ne kawai zamu taho bai bukatar mu dauki komai yaya Balki da wasu mata biyu cikin matan yayan Alhaji suka yi mana rakiya.

Kai tsaye sabon gida Alhaji ya kaimu, tabkeken gida mai manya-manyan dakuna ciki da falo da akayi matukar kawatawa da kaya shi ne nawa ga wani dakin a kusa da nawan shi ne na Uwa can gefe wasu dakuna guda biyu daya wai na Junaidu da Babangida, dayan kuwa na yaran da zai debo mun, daya kuma wani wuri da aka kawata da kuma biyu da falo da bayan gidan nan ne wai nashi, ni da kaina mamaki ne ya kama ni baile kuma wadanda suka yi min rakiya.

Kwana uku ‘yan rakiyata suka yi suka tafi, da za su tafi sai na ce wa yaya Balki in sun koma ta bude dakina ta kwashe duk kayan da suke cikina bata tayi ta murna.

Bayan tafiyarsu ina zaune a falo na tasa ‘yan yara a gaba zuciyata cike da tunani iri-iri sai ga Alhaji ya shigo, Karama da Maryam suna biye dashi sunyi kitika-kitika sai wani juyi suke yi suna sheki na karbe su hannu bibiyu muka gaisa muka shiga hira sai dai da Maryam kawai don kuwa ita Karama bata iya hadiye bacin ranta ba nan take a gabana ta ce mishi dama ita kadaice zata zauna anan’? Ya ce mata eh, zata ai tayi hiru da zasu tafi na diban musu daddawa da kukar da nazo da su daga gida, na basu tafiyarsu da kwana uku sai ga Maryam tazo min wuni, ta taya ni muka kara kintsa wuri, yayi kyau sosai sai da na gama abincin dare taci sannan aka zo aka dauke ta ta tafi.

Matan abokan Alhaji suka yi ta zuwa yi min sannu da zuwa saboda ya basu labarin uwargidanshi tazo a wannan lokacin ne muka so juna ni da Hajiya Hauwa, alhalin da can tana mu’amallah da su Karama, a wannan lokacin Karama tayi matukar tayar da hankalinta kan dawowa na da kuma ware ni da Alhaji yayi ni kadai ga kuma irin kawatuwan da yayi wa gidan da ya sanya min kan wannan abin har sau biyu tayi yaji ta tafi gida, zuwan farko yaje sai dai bai yarda da cewar da akayi ya hadamu wuri daya ba ya ce ai shi ba wannan lokacin ne ya fara raba mu ba tunda ya dade da debo su mu kuma ya bar mu a kauye me yasa tun wannan lokacin bata yi maganar ya hadamu a wancan lokacin ba sai yanzu? Karama bata gama wastsakewa daga wannan lamarin ba sai labari yaje mata cewar zan tafi aikin hajji ni da yayan tudu Alhaji ya biya mana in na tsaya cewa Alhaji ya jiyar dani dadi a wannan lokacin ya nuna min gata ya karrama ni to na bata bakina ne kawai don ba zai yiwu in fadi komai ba, abu daya dai da zan gaya miki shine, nan da nan na goge nayi fes na zama matar birni nayi kyau irin wanda ban taba yi ba, gani dai dama mai tsabta ce kwarai to gani kuma na shiga daula na kuma yi dace na gamu da mata ma’abuta ado da iya kwalliya, irin su Hauwa. Kuruciyata ta dawo danya sharaf, fatata tayi matukar yin kyau har mutane da yawa ke zaton wai su Karama sun gime ni.

Ina nan zaune da su Uwa da su gwanin sha’awa babu wanda yasan bani na haife su ba, saboda babu alamar da zata nuna hakan.

Tunda aka fadi zan tafi aikin hajji Maryam tazo min murna, Karama kuwa sai da Alhaji ya taso ta a dalilin kawo su dukansu da yayi shine tazo.

<< Wace Ce Ni? 27Wace Ce Ni? 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×