Skip to content
Part 30 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

An dawo babu dadewa aka yi bikinsu, biki na gata don babu abin da Alhaji bai yi musu ba na gata nima nayi gayya har daga Senegal yan uwa sun zo biki, taro ya tashi lafiya aka watse, kowa ya koma gidanshi aka bar ango da amarya dani kuma da na rinka ganin tamfar ni na fi kowa jin dadin zamani na hada aure tsakanin kanina uwa daya uba daya da ‘yar da nake so yar da na rike ‘yar da nake ganin ‘ya ce.

Auren Uwa da Muntaka ba karamin al’amari ba ne a wurina, don sai da na rinka ganin tamfar sune dangina gaba daya da nake ganin na rasa a baya, na rinka jin tamfa r duk wani bakin ciki da na gamu da shi a baya ya wuce, ya zama mun tarihi.

Gidan su ya zame min wurin zuwa in naji zani unguwa sai in cewa Alhaji zani gidan su Uwa in dubo su wata rana ya ce min a gaishe su wata rana kuma ya ce bai yarda ba, wai na fitini yara da zirga-zirga a gida itama Uwa in taga kwana biyu bata ganni ba zata shirya tazo wuni, in zata zo kuwa zata yiwo min girke-girke iri-iri tazo min dashi, Uwa da Muntaka suka maida ni ‘yar gata sai ji dani suke yi nima ma ji dasu komai Alhaji ya shigo dashi gidan zan raba biyu in dorawa Babangida ko Junaidu in ce maza kai wa Uwa.

Ana nan a haka rannan muna hira da Alhaji sai ya ce min, ni Zuwaira in nace ki bani dava cikin ‘ya’yanki in kaishi Turai yayi karatu wa za ki ba ni? Na zuba mishi ido cikin kaduwa ina kallonshi na ce ban fa wattsake daga kewar rabuwa da Uwa ba shine har ka fara tunanin sake raba ni da wani kuma? Ya ce to yaya zaki yi ai dukansu ma kwashe su zanyi in kaisu karatu ke dai mutum daya zan fitar daya zai yi ne a nan a gida amma ba zan bar miki gidan babu yara ba, zan kawo kanana in sa su suyi karatu manya kuma su taya ni harkokin kasuwanci na ce mishi to, na kuma yi mishi addu’a.

Kwana biyu ya bani inyi tunani don haka da kwanakin biyu suka cika sai na gaya mishi akai Babangida Turai shi kuwa Junaidu a barshi yayi anan bai nemi sanin dalilina na fadin hakan ba nima ban tsaya yi mishi dogon bayani ba tunda naji ya ce to shi kenan sai nima nayi shiru.

Tun daga nan bai sake ce min komai ba nima ban sake komawa kan maganar karatun nasu ba, don ba son tafiyar tasu nake yi ba rannan kawai sai Alhaji ya ce mun shirye-shiryen tafiyar yaran nan sai ta kammala ina ganin tatiyar ta matso,  nayi maza na ce au a haka suna yan kanana ne za’a tafi dasu, ai na dauka sai sun girma tukuna? Gaskiya in dai yanzu ne na fasa a bar mun su kawai sai sun kara hankali tukuna ya ce min to.

Kwana hudu bayan nan daga fita sallar asuba sai kawai naga yara shiru basu dawo ba sai da na gaji da jiran shigowarsu bayan na kamala abin karyawa na ce aje a kira mun su su zo mu karya sai kawai Alhaji yace mun ai an riga an tafi dasu za’a kai Junaidu wata makaranta a Akure shi kuwa Lamido za’a wuce dashi.

Ihu na rinkayi da iyakacin karfina yana ba ni hakuri daga baya ma naga hakan ba zai mun ba na kama hanya na nufi katagan naje na bude dakin Baba da aka riga aka gyara tas na zauna a ciki zuwan Alhaji biyu naki binshi na ce ya barni anan kawai ai ya riga yasan ba zan iya zaman gidan babu yaran ba yarbani dasu ba tare da ya gaya min tafiyar tasu ba.

Satina biyu a Katagun in ban da bacin rai babu abin da nake yi naja na tsaya kan lalle Alhaji ya dawo mun dasu kafin in dawo ko kuma ya bar nil in yi zamana anan.

 Rannan dai ya sake zuwa na ce a na riga na ce ba zan koma ba, ya ce ai na kawe wasu yaran nace to ina ruwana dasu? Ni nawa nake so in gani.

Rannar dai yayan tudu yayi min fada irin wanda aka dade ba ayi min ba abin da ya tuna min da Baba nayi ta kuka a haka na biyo Alhaji muka dawo gida na same shi cike da yara da ya kawo gaba daya ya’yan yan uwa ne da na sani nasan lokacin da aka haife su amma basu debe min kewar Junaidu da Babangida ba, basu hana ni kukan tafiyar su ba. Ban taba samun kaina cikin kuiyan yin girkjin gida ba sai a wannan lokacin duk abin da nayi niyyar girkawa in na tuna Junaidu da Babangida ba za su ci ba sai inga to wa zan girkawa akan dole Alhaji yasa Hajiya Hauwa ta nemo mishi mai girki inda ta kawo mishi wata daga baya kuma ta kawo mishi mai gyada don ita mai gyada tafi wancan tsabta da iya girki akan dole na bar wa mai gyada girkin gidan saboda na kasa, kasala ta kamani bani da wani aiki sai na tunanin yaran in kuwa rufe ido nayi da sunan barci in yi ta mafarkinsu a wannan lokacin kullum daga gidan Uwa ake kawo min abincin dare kowane kwana biyu kuma sai tazo gida wai tazo duba ni.

Ana cikin haka ne na gane Uwa ciki ne da ita wai ban iya fadin farin cikina na hakura na kwantar da hankalina na koma kan lissafin cikin da Uwa ke dashi da kuma zumudin ganin abinda zata haifa, Uwa ta kanma zazzabin laulayi, kullum sai naje dubata in girka mata wannan in girka mata wancan sai dai bata iva ci saboda kurarrajin baki sun dame ta amma dai an samu taji sauki sai dai kurarrajin kam sunki jin magani, dole aka hakura aka barta sai dai kullum zan dama mata kunun gyada na shinkafa da na tsamiya in hada da kindirmon dana sa mai nono tana kawo min in aike mata dashi shi ne ya zamo mata abinci.

Duk da kurarrajin baki sun takurawa Uwa basu hanata murmurewa tayi kyau tayi fari sol ba duk da ita din ba fara sol ba ce, asalin kalar jikinta yana tsakanin fari da baki ne, wato a inda babu farare ita fara ce a inda kuwa suke da yawa to ita baka ce, tayi matukar yin kwarjini don kuwa dama doguwa ce sambal a mike take gata da idanuwa dara-dara wadanda a wannan lokacin suka kara fitowa suka kuma yi fari tas, bakin kuma ya kara baza ba mijin uwa ba da yake matukar sonta yake ganin tanfar ita ce komai dinshi, don kuwa na taba zuwa gidan na gane Uwa tana kokarin boye min bacin ranta, dana koma gida na neme shi na nuna mishi rashin jin dadi kan bata mata ran da yayi sai ya sunkuyar da kanshi kasa ya ce min ita ce mafi darajar abin da nake dashi, ita ce mafi soyuwar abin da nake so amma hakan ba zai hana in tayi kuskure in mata fada ba nace mishi haka ne amma maimakon fada rinka yi mata nasiha da abin da na raine ta bishi kenan zata bar duk wani abin da baka so in ka gaya mata cikin natsuwa ya ce mun to, to ba mijinta dake yi mata irin wannan son ba ni da kaina bana gajiya da kallonta.

A wannan lokacin duk wata hidima ta gidan Muntaka ya dauke mata ita sbaoda zuwan da nake yi in same shi yana aikace-aikacen gida yasa na daina yin sammakon zuw agidan sai na daidaici ya gama zai fita kasuwa ni kuma in dani mata hira. Muntaka da kanshi ya gano hikimar yi mata farfesun kanta yayi laushi sannan yayi amfani da turmin karfe mai tsabta ya dan daka shi don sauwake mata tauna.

Ganewar da nayi cewar uwa da Muntaka so mai tsanani suke yiwa juna sai dadi ya kamani na kara sonsu wani irin son da ba zai yiwu in iya kwatantashi ba.

Ana cikin wannan hali ne rannan Alhaji ya dawo dagga sallar Asuba naji shi yana kwalawa daya daga cikin yaran da suke gidan kira, yana fitowa bai ma saurari gaisuwar da yake yi mishi ba ya ce mishi maza tafi ka dubo min Muntaka me ya hana shi zuwa masallaci yau? Yaron ya fita da gudu ni kuma na fito ina ce mishi ko sun makarane?  Ya ce to ban sani ba amma shi ba mai makara bane ni dashi mukanyi rige-rigen zuwan Masallacin ne watarana in riga shi wata rana ya riga ni, muna tsaye a wurin har yaron ya dawo ya nemi wuri ya tsuguna ya shaidawa Alhaji bai jin dadi ne ciwon ciki na damunshi.

Da sauri Alhaji ya fita ni kuma na tsaya ina fadin ikon Allah, yau kuma cikin nashi ya dan motsa kenan, ganin da nayi Alhaji bai dawo ba sai nayi zaton asibiti suka tafi gashi ya fita ban tambaye shi ba balle in je can gidan don haka sai na tura maigyada na ce mata taje tazo min da Uwa.

Isowarsu ne na gane Ciwon bana wasa ba ne saboda ganin yanda Uwa ta rude in ban da kuka babu abin da take yi na shiga rarrashinta ina fadin haba Uwa, in mijinki yana ciwo sai kiyi ta kuka haka? Tana kukan ta ce min ba kukan ciwo nake yi ba mu..bata karasa ba saboda ganin da tayi na zuba mata ido ina kallonta kiyi hakuri Umma kiyi hakuri ta koma kuka tana ba ni hakuri, hankalina yayi matukar tashi na rasa inda zanyi na surn gyalena na yafa na tasa Uwa a gaba muka nufi asibitin don muga halin da suke ciki muna isa. Alhaji da Maibindiga muka fara gani da sauri ya ce mun me ya fito dake? Wa ya ce miki ki zo nan? Maza koma kiyi hakuri muna zuwa, muka dawo gida. Ba mu wani dade ba sai gasu sun dawo sai gashi ana ta shigowa gida ana diban butoci ina tsaye tsakar gida ina sauraron Alhaji ya shigo ko wani wanda zai gaya min abin da ke faruwa ji nake tamfar inyi wajen in ganewa idona saboda tsananin bugun da zuciyata ke yi, a cikin tsayuwar sai ga Hajiya Hauwa ta shigo kuka take yi sai ga Karama da Maryam sai ga matan abokan Alhaji da  makwabta suna ta shigowa ashe wai Muntaka ya rasu ne, a wannan lokacin bata kaina nake yi basaboda halin da Uwa take ciki suma take yi ana shafa mata ruwa inta yi kamar ta farfado sai kuma ta koma suman gata da ciki don haka akayi maza aka nufi asibiti da ita aka kwantar da  ita ni kuma ina gida wai ina karbar gaisuwa daga baya naga zama ba nawa ba ne nasa aka je aka rokar min Alhaji ya barni inje asibiti wurin Uwa don tunda akayi mutuwar ya ki shigowa gida sai turowa yake yi wai a bani hakuri, bai hana ni zuwa asibitin ba don haka can na tafi naje wurin Uwa. Tsayuwa nayi na zama Jaruma nayi ta rarrashi ina bada hakuri ina kuma tuna mata da cewar mu din dukanmu zamanta muke yi sai dai in wa’adi bai cika ba, in nayi ta rarrashi sai kuma in koma kwadaitar da ita game da rayuwar da mai lmani ke sa ran samu bayan mutuwa, shi kuma imanin ba zai cika ba sai in za ka karbi kaddara a yanda tazo maka, don haka kiyi hakuri saboda ki samu ladan musibar da ta same ki da irin wannan ban bakin da irin wadannan kalaman na samu Uwa ta dawo cikin natsuwarta ta koma ambaton Ubangiji maimakon tsananin tashin hankali na neme sallama muka dawo gida.

Ranar da aka cika uku ne nayi sammako tunda asuba na shiga wurin Alhaji tun bai fita sallah ba yana kan sallaya yana addu’a na jira shi ya shafa fatiha na gaishe shi nayi mishi ta’aziya na tashi na fito na dawo cikin gida.

Alhaji ya karbi gaisuwa har tsawon kwana bakwai saboda Jama’ar da ke ta zuwa mishi ta’aziya.

Bayan an gama karbar gaisuwa ne aka barni daga ni sai Uwa sai ko sauran mutanen gida.

A wannan lokacin ne na samu kaina cikin wani irin tsanani ga dai zuciyata dake cike da dacin mutuwar dan uwana da na rasa wanda bani da kowa sai shi ban kuma same shi ba sai bayan da na dandani azabar zama ni kadai, to na same shi ina murna gashi kuma na rasa shi rasawa na farat daya a lokacin da ban taba tunanin hakan ba, da Muntaka ya danyi jinya nema watakila da ban dandani azaba mai yawan haka ba to gani kuma tashe da uwa mai ciki wacce bata taba daina kukan mutuwar mijinta ba, wacce ta kaurace wa cin abinci na zama bani da aiki sai na rarrashi da ba da hakuri da nasiha tare da yin wa’azi in na dan samu ta dan sake ta dan soma zata yi magana yanzu ne zata soma hirar Muntaka daga haka kuma sai ta kama kuka, ni ba abin in ce zanyi mata yanda Alhaji yayi min ba, baya yarda maganar mutuwar tashi ta hada mu sai kawai ya mike ya fita a haka na zauna da Uwa wacce renonta yafi na dan jariri wahala, har cikinta ya kai wata takwas na shiga nuna don ganin sun kusa rabuwa itama ta huta watakila kuma in taga danta zata mance ta hakura dor ganin ga dan Muntaka a hannunta.

A wannan lokacin tuni na gama shirin baihuwarta komai na tanade shi sai jiran zuwan haihuwar kawai nake yi itama ta danyi kuzari har na soma zuwa makarantarmu tare da ita.

Rannan muna tsakar gida ni da ita zogale ta ce min tana sha’awa na aika aka sayo min danyenshi na gyara shi tsaf na dafa mata na tsiyaye ruwan a wani kofi na gyara ganyen na kwadanta mata shi yayi kyau yayi dadi na dauko na kawo mata na ce gashi nan ga kuma ruwanshi in kin kasa tauna ganyen sai ki kwankwade ruwan don dama yafi ganye amfani a jiki maigyada tana yi mana dariya tana fadin Hajiya kenan na ce eh to in banda dai sha’awa mai sama da wadannan kurarraji yaushe zai iya cin ganye?

Uwa ta tasa ganyen nan tana kallo nima ban tanka mata ba tunda dai ta yarda ta shanye ruwan sai ta kalle ni tayi murmushinta a hankali ta ce Umma ina son yi miki wata magana, ina tsoron nayi maza na ce haba Uwa tsoro ya hana ki gaya min magana, to wa za ki gayawa in ba ni ba? Ta dan saki wani lallausan murmushi ta ce kar hankalinki ya tashi ne nayi maza na ce mata gaya min kawai ba zai tashi ba ta ce ido nane Umma bai gane kalan abu komai sai nake ganinshi baki gashi kuma sai in rinka ganin mutane suna rabuwa mun bibbiyu.

Yanke jiki nayi na fadi a kasa saboda tsananin firgita da nayi da wannan bayani na Uwa, ciccibata akayi aka kaini daki nayi kuka rannan har na gaji ban daina ba, da Alhaji yazo dubani don anje an gaya mishi abin da ya faru na ce mishi aje a dauko ban boye mata komai ba ban ki gaya mata abin da nake tsoro ba don ta riga ta zama min ‘yar uwa da na gama yi mata bayani sai kawai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce to kina ganin kamar in muka hadu a nan da wani abin da zamu hana ne? Nayi maza nace mata bamu isa komai ba taya ni zaman gidan zaki yi, ta ce to shi kenan. Muka tasa Uwa a gaba ni kam komai tayi idona yana kanta sai dai banga wata alama ba.

<< Wace Ce Ni? 29Wace Ce Ni? 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×