Skip to content
Part 31 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Rannan muna kwance ni da ita a gado dama kuma tare muke kwanciya ita kuwa yaya Balki tana daya gadon sai naji tamfar Uwa tayi magana na ce mata me kike fadi? Sai da nayi mata tambayar sau biyu sai ta ce bada ke ba ne nace da waye? Ta ce da wannan ne na sake jin wani faduwar gaban nayi maza na mike zaune na ce mata a ina kika ganshi Uwa? Kan ta ce min komai sai yaya Balki ta ce min ke kuwa me yasa kike irin wannan binciken ne Zuwaira? Me za ki iya yi ne? Kinga yanda kika maida kanki kuwa cikin ‘yan kwanakin nan? Ashe shi mai imani ba da mika wuya aka sanshi ba? Kalaman yaya Balki ba su hanani kuka ba, cewar da uwa tayi da Muntaka take magana ya kara firgitani ina kuka na cewa Yaya Balki sai yaushe zan samu abin da nake so? Duk wanda naso rasa shi nake yi ta ce min da dai kin tuba kin yi ta istigafari kar ki sanya kanki cikin wata fitina, duk abin da kika so kika rasa din ai ba naki ba ne ajiyanshi aka baki ko sai mai shi ya fasa karba don kina so?

Kwana biyu bayan nanne kawai Uwa ta haifi yarta mace bayan yar gajeriyar nakuda mai sauki bata kai awa guda bayan nan ba ta ce garinku na kalle ta a kwance a shimfide na ce shi kenan Uwa shi kenan Rabi’atu kun tafi ke da mijinki kun bar min ‘yarku shi kenan maimakon in yi kuka mikewa nayi naje na soma shirya ruwan da za’ayi mata wanka ni da kaina na wanketa da taimakon Maryam da Hauwa na sanya mata kayanta nayi mata addu’a aka zo aka fita da ita ina kallo nayi zaman karbar gaisuwa kwana uku da akayi bakwai kuma Alhaji ya ce sunanki Rabi’atu ya mayar miki da sunan Uwarki, na sa maigyada ta nemo min mai reno ta kawo min Talatu, da aka yi sati biyu sai na samu Alhaji na ce mishi so nake ya yardan min in je Katagun in dan zauna a dakin Baba in dan huta, ya ce min to in dan saurare shi tukuna na ce to. Rannan da ya shirya zai yi tafiya sai kawai ya ce min dauko yarki muje na ce mishi to, dani yayi wannan tafiyar da muka dawo kuma bai dawo dani gida ba sai ya ajiye ni a gidanshi na Legos, bai kuma sake sha’ani za’ayi sai bayan shekaru uku sai dai yaya Balki kanje Legos tayi min bakunta, tun bakuntar farko da taje mun kuwa na ce mata taje ta kwashe kayan dakina taje ta gyara nata wurin.

Sai da aka gama ginin gidan nan na dawo muka sake haduwa dasu Karama saboda a lokacin kuma Alhaji yayi nufin sake hada iyalinshi wuri, daya na, zo,na samu gida, çike da iyali ga yara maza da mata don sun riga ni dawowa.

*****

Na daga ido na kalli Ummana cikin tausayawa bakin cikin da tayi na rasa wadanda take, so nayi ajiyar zuciya sannan na ce mata wato dai Umma ba ke kika, haife ni, ba mutanen da kike so ne suka haifan miki ni? Sai da ta zuba min ido kafin ta ce min kwarai kuwa, na kwantar da kaina jikinta na ce mata to kar ki sake gayawa kowa labarin nan Umma ki bar su kawai a kan ke kika haife ni tunda ma dai ai nononki nasha na girma.

Umma tayi murmushin farko tunda ta fara ban labarin ta ce ban shayar dake nonona ba Adawiyya, Alhaji bai yarda nayi hakan ba na rene ki ne ta hanyar shayar dake da abincin jarirai, Babangida shine yaron da na shayar dashi nonona, ina ganin biyu bisa ukun nonon da ya sha nawa ne saboda kullum a wurina yake kuma a wancan lokacin, Maryam kanyi yaji in suka yi fada da Karama, ta barshi kan wannan dalilin sai ya zama nike shayar dashi. Nan take naji kishin yaya Almu ya kama ni na ce wato yaya Almu ma danki ne? Ta yi maza tace nawa ne mana Adawiyya, Alhajj ne fa ya haife shi, Baba kuma ya bani shi na kuma rene shi ta hanyar shayar dashi nonona, shi kuma bai taba nuna min yasan yana da wata Uwa ba in ba ni ba ce Lamido ai na wane Adawiyyah nawa ne, ke kuwa Muntaka da uwana ne suka haifarmun ke, don haka bani da kamarku ke dashi sai ko Junaidu dukanku na wane hakan nema yasa na baiwa Alhaji sunan Junaidu lokacin da ya ce in taya shi zaben wanda zai barwa shugabancin kamfanoninshi.

Na daga ido na kalli Umma zuciyata ta sake raya min wasu al’amura game da ita, ban sani ba ko ta gane tunani nake yi sai na ji ta ce min taimake ni kar ki ji wani canji a tare da ni don na ce miki bani ce mahaifiyarki ba, ke din kece komai nawa kece Muntaka, kece kuma Uwa, a duk lokacin da na daga ido na kalle ki na kan ganki ne da kamanni guda biyu, kina kama da Muntaka kamannin dake sawa mutane suna ganin kamanninki dani amma ni da aka haifi Uwa akan idona na kuma rene ta ta girma a gabana nasan abubuwanki da yawa nata ne mafi yawancin lokaci nakan biki da kallo ne saboda wasu abubuwa da kike yi wadanda nake ganin tamfar koyar dake su tayi sai dai kuma tunda nasan baki santa ba to na sanbà koyo ba ne gado ne.

Na matsa jikin Umma na kwantar da kaina a cinyarta cikin hawayen tausayi nace mata, ke ce komai dina Umma ba zan canza komai ba game da ke sai dai ma in kara sonki….kan Umma ta ce min komai sai naji muryar Baba a cikin falon Umma yana cewa me Zuwaira take yi ne a wurin nan ta barni ni kadai har yanzu? Kan tayi magana sai Baba ya shigo ya gammu tare, ashe baki baiwa Lamido matarshi ba shima ya samu ya huta kamar sauran ‘yan uwanshi? Umma ta ce kayi hakuri gani nan zuwa, ya ce a’a kar ki zo alamar yayi fushi, ya juya ya tafi.

Umma tayi maza ta dauki wayarta ta kira Umma amarya taimake ni kije gun Alhaji kar ki bari yayi fushi sai da safe zan shiga wurin naku, ta maida wayar ta ajiye hakan da Umma tayi bani wani mamaki ba don nasha ganin tana baiwa Umma amarya kyautan girkinta.

Gari na wayewa Hajiya Hauwa ta iso saboda wayar asuba da Umma tayi mata tana shigowa ta ce mata ‘yarki zaki kai gidan mijin ta tun Alhaji bai fito ya ce ta tafi ita kadai ba ki ce don ni uwar miji ce yasa na bari yayi hakan Umma

Hauwa ta ce eh mana me zai hana ni fada? Umma Karama kawai aka kai ni nayiwa sallama saboda Umma amarya bata fito daga wurin baba ba, a haka muka bar gidan daga ni sai Umma Hauwa sai ko Baba Talatu da Ummma ta ce ta biyo ni don dama zamana take yi a gidan muna tafiya ni da Umma abaya direba da Baba Talatu a gaba Umma Hauwa ta ce to ke Talatu ai gara ki hakura ki bar kuka haka tunda ga uwar dakinki kuna tare.

Ni kam har muka kusa isa kaduna ina kuka, tausayin Ummana ne ya ke damuna ko damna can babu abin da nake so kamar Umma, amma ban taba sonta ba kwatankwacin son da nake yi mata a yau ba.

Mun kusa shiga Kaduna direba yana Kallon motar dake biye dashi ta cikin madubi saboda bata wurin da yayi ta wuce taki ya ce au Hajiya ai Lamido ne yake biye damu, Umma Hauwa tayi murnmushi ta ce, a to, uwarshi ta ce wai yayi gaba saboda yayi fushi da abin da Adawiyya tayi mishi ana fushi da Amarya ne?

Yaya Almu ne ya wuce direba yabi bayanshi muka karasa gidan babu kowa a cikin gidan yaya Almu ne yasa makullai ya bude ko ina muka shiga ko’ina gwanin sha’awa sai kamshi da kamshi ke tashi komai tsaf komai a tsare a tsaftace gwanin sha’awa ga wani sanyi na ni’ima ai Alhaji yayi dabara daya ce kowace amarya tabi angonta kawai ba sai an kaita ba da yanzu duk wurin nan an lalatashi, tana wannan maganar ni kuwa ina takure wuri daya cikin lullu6i ina ta karanto addu’o’i iri-iri da Baba Balki ta bani ta ce in karantasu a lokacin da na shiga gidan mijina sai a wannan lokacin ne ta fado min a rai wato haka ta ce ita ce mahaifiyar Uwata, wani tausayin ya sake kama ni da na tuna su san san uwa wato mahaifiyata nice ban san taba ban santa ba ban san Babana ba sai Umma da Baba na sani. Wasu sabbin hawayen suka soma zuba abin da ya fusata Umma Hauwa tayi tayi min fadi baba Talatu tana ta bata hakuri.

Direban da ya kawo mu ya shigo rike da manyan iedoji ya ajiye ya koma ya sake debo wasu ya kawo, Umma ta ce kai sun isa haka bai ga mu uku ba ne?

Da aka natsa Umma ta sanya ni na sake wanka na tsalla kwalliya cikin wani tsalelen leshi mai matukar laushi ya kuma karbe ni sosai don ya dace da kalan jikina gashi kuma dama Jikin nawa yayi shar a dalilin lallen da ta mulke ni dashi gaba daya.

Tunda muka iso babu wanda ya sake jin motsin yaya Almu sai da muka yi sallar La’asar Umma ta ce a kira mata shi don zata tafi, lokacin ne ya shigo dakin cikin ladabi a kasa ya zauna kamar yanda nima dama aka san ya same ni sai Umma ce akan kujera. Sai da ta amsa gisuwar da yayi mata sannan ta ce mishi ni zan

tafi Lamido ga matarka nan na kawo maka ba

sai na ce maka komai ba, kafi kowa saninta,

kayi tayin hakuri Allah ya saba halayenku ya

kuma sa ta zame maka uwar iyali tana fadin

hakan ta mike tayi waje tana goge fuskarta da

gefen gyalenta yaya Almu ya mike cikin

natsuwa ya bi bayanta don ganin tafiyarta. Baba

Talatu kuma ta shigo tana ta bani hakuri tana

cewa aike aure mai dadi kika yi uwardakina

mijin da zai yi hakuri dake ai shi aka baki.

Yaya Almu ya sake shigowa bayan tafiyar

Umma Hauwa Baba Talatu tana ganin shi ta

mike zata fita ya ce a’a kuyi zamanku Baba

Talatu ya juya ya fita bai sake shigowa ba sai

bayan sallar Isha’i, yaya dai Baba akwai

damuwa ne? Tayi maza ta ce mishi babu

babangida ya ce to kuna son wani abunci? Ta

sake cewa a’a bamu da bukatar komai don

akwai, yayi murmushi ya ce, to sai yaushe

amaryar zata fara yin magana? Ta taya shi

murmushin don jin ya shigar da raha cikin

lamarin yace ina jin dai so take a sayi bakinta,

ya juya zai fita yana cewa, ta yata kwana Baba,

da sauri Baba Talatu ta ce mishi a’a ai ba za ayi

haka dani ba, ba girmana ba ne yin hakan bai

tsaya ba ya tafi. Da sauri na kalli Baba Talatu na

69

ce mata me yasa kika gaya mishi haka? Ta ce

wane ni ai kawaici yayi mun so kike in jira shi

sai ya ce in bashi wuri? Tana Cikin maganar wai

kawai naji yaya Almu ya sake shigowa ta wata

kofar daban san da ita ba Baba Talatu tana ganin

haka tayi maza ta fice ta tafi wurinta shima yana

karasowa ya maida kofar falon ya kulle ya dawo

inda nake zaune cikin murmushi nazo sayen

bakin amarya ne, yana maganar yana kallona ya

miko hanmu a hankali ya tallabi habata ya

karanto wasu addu’o’i ya tofa min a fuskata

sanan ya mike ya sure ni zuwa daya daga cikin

dakinan kwanan da suke wurin.

Da Asuba na bi umarnin da ya bani na

komawa daya dakin na kwanta bayan na idar da

sallar Asuba kas ancewar tsawon daren ban samu

na runtsa ba ga kunma gajiya da rashin bacci na

kwana da kwanaki bacci mai nauyi Sosai nayi

ban farka ba sai bayan shabiyu ko lokacin ma

kuwa dana farkka dana lura sai na gane Baba

Talatu ce ta taslhe ni saboda ganinta da nayi tana

matsa min kafata, na kalle ta cikin natsuwa

maimakon in gaya mata wata magana saboda

kidimewa sai na ce mata bani da lafiya Baba

tayi maza ta ce na sani uwardakina ko daga farin

cikin maigidan da na gani na san abin da ake

ciki balle tun safe ya wanke shinfidun da suka

70

lalace ya shanya su ga kuma alheri mai yawa da

yayi min turaren atamfofi da turare gami da

kudi ya bani Allah dai yayi muku albarka ya

kuma sa ku zame mishi uwar iyalinshi.

Ban tanka mata ba don ba abin da nake nufin

gaya mata kenan ba na so ne kawai ta fahimci

zazzabi ya kama ni. Mikewa nayi cikin karfin

hali na shiga bandakin na dan hora kaina da

ruwan zafin da na zubawa detol tunda na riga na

girma ba sai na jira an gaya min abin da zan

taimaki kaina dashi ba, na fito na samu abincin

da ta kawo min na gama koma1 na sanya kayana

bayan na gyara kaina nayi matukar yin kyau

zani da riga na sanya na yadin material mai

kyaun gaske, har na zauna da shirin ka ryawa

sai na tambayi Baba Talatu yaya Almu ya fita

ne? Ta ce a’a na ce to me aka kai mish1? Ta ce

bai karbi komai ba na dai ce mishi akwai.

tsallake abin karyawan nawa nayi na nufi kicin

din don ganin abin da zan shirya mishi tunda na

gane shima ba karya ba nan da nan na shirya

mishi abubuwa masu sauki na hada da farfesun

kajin da Baba Talatu tayi da na koda naje na har

falonshi na kai mishi sai dai ban yarda na zauna

mun karya tare ba kamar yanda ya nemi inyi

fitowa nayi na dawo wajena na zuana ina

karyawa da Baba Talatu tana yi min hira sai dai

71

gaba daya hirar tata yau kan budurcin ya mace

ne ni kam ina jinta.

Tun daga rannan na shiga kicin don girkin

abincin da yaya Almu zai ci ban yarda amarci ya

hanani yin hakan ba saboda irin kalaman da

Umma na tayi mun kan muhimmancin aure da

kuma kula da miji, sai dai kuma na kasa

daurewa in barshi ya sake matsowa kusa dani

saboda gani nake tanfar ya kware ni ko kuma in

ce ya so kanshi da yawa a kaina don haka ina

kai mishi abincin nake dawowa wurin in shiga

in kulle ko’ina in yi kwanciyata.

Rannan da safe ina kicin zan shirya mana

abin karyawa rannan kuwa satina guda ne a

gidan sai ya shigo kicin din yazo ya same ni ya

ce amuna dai kin san tunda kika zo baki yi mun

shinfida ba cikin ladabi na ce mishi bari in gama

in zo in yi ya ce a’a bar wannan aikin kije kiyi

mun wancan din tukuna, don ya fi muhimmanci

a wurina na ce to na yi maza na wanke hannuna

da sabulu na goge shi da tawul kafin na shiga

dakina naje na dauko wani zanin gadon da zan

canza mishi sai da na shiga can cikin dakin

dakin wanda sai ranar na fara shiga naga komai

a kintse a tsabtace ga kamshi mai dadi dake

tashi a ciki,  lokacinne na gane wayon da yaya

Almu yayi mun saboda ganinshi da nayi a jikin

72

kofa r dana biyo ya tsare ko’ina ban ce mishi

komai ba don na riga na gane abin da yake nufi.

<< Wace Ce Ni? 30Wace Ce Ni? 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×