Abin da yaga dama yayi shi da kanshi kuma nasan yasan ya kware ni tunda duk wani abin da yayi na ya gamsar da kanshi ne kawai, na kwance a gefe ina kallonshi cikin hikima a zuciyata dai tunani nake yi ko kowa haka yake ko kuwa yaya Almu ne kawai mai irin wannan halin? Ban ankara ba da idona ya kai kan agogo sai naga wai sha biyu ta wuce na yunkura cikin karfin hali na fita na bar dakin yana kirana rabi, ban tanka mishi ba na koma dakina na zauna Baba ta biyo ni za’ayi miki wani abu ne? Na ce mata a’a in dai kin karya shi kenan ta ce to ta juya ta fita nima nayi abin da zanyi na kwanta.
Tun daga rannan na yiwa yaya Almu yaji ban sake yi mishi girki ba ban sake leka koda falonshi ba ne balle in kai ga shiga ko tsakar gida bana shigowa.
Kwanana hudu da daukan wannan matakin ina kwance a dakina tun safe ban fito ba shima yaya Almu yana wurin shi sai kawai na ji sallamar da ta yi min kama da muryar Ummana da gudu na yiwo waje ashe kuwa ita ce sai dai har ta shiga wurin yaya Almu can na same su yana ta faman ina yaka saka da ita. Fadawa nayi Jikinta na kwanta ina tumurmusarta kamar wata yar yarinya yaya Almu ne ya kawo mata abin sha ya koma gefe ya zauna cikin farin ciki yana cewa Umma ba ki ce mana zaki zo ba.
Ta ce eh ai zuwan nawa ba na shiri ba ne Talatu ce tayi mun waya ta ce bata gane kan matar gidan ba da farko dai ta karbi hidimar gidanta gwanin sha’awa amma yan kwanakin nan bata gane mata ba shi ne na ce to bari in zo in ji me ya faru? Na nemi wuri na zauna cikin natsuwa saboda jin maganar tata ban ga kuma alamar wasa a tare da ita ba, ta sake kallona ta ce me ya same ki Talatu ta ce kin saki hidimar mijinki? Ban yi magana ba na soma kuka saboda ganewan da nayi cewa dan kankanin laifi zanyi tayi min fada ganin ina kuka sai ta juya wurin yaya Almu ta tambaye shi nayi zaton ba zai yi magana ba sai kawai naji yace wai daga nasata ta shigo dakina ne Umma.
Umma tayi shiru ba ta ce mishi komai ba, ta dai yi wasu yan maganganu ta mike zata tafi na ce baki shiga wurina ba fa Umma, ta ce sai randa na sake zuwa tunda ba kya jin magana ta fita waje Baba Talatu ta fito tana yi mata magana ta kawo kudi ta bata ta shiga mota ta tafi ta barni ina cizon yatsa saboda takaicin kin shiga wurina da tayi yan kwanaki kadan bayan wannan lokacin har nan kuma ban yarda mun shirya da yaya Almu ba don nasan abin da shirin namu yake nufi sai kawai Umma ta bugo mun waya dana dauka sai ta ce min shiryawa zaki yi kiyi wa Lamido rakiya zuwa kasar Philipine kuje can kuyi amarcin daga nan kuma akwai aikin da zai yiwa Alhaji in kuma har ku ka dawo ba ki saki jiki dashi ba zan sa Talatu ta koma gida abar ku ku biyu a gidan ai kunyarta yake ji da bai yarda da wannan sakarancin ba.
To hakan kuwa akayi ba karamin morewa amarci yaya Almu yayi ba a wannan tafiya da muka yi tunda daki daya muke bayan haka kuma na kara yarda da maganar Umma ta cewar kunyar Baba Talatu yake ji. Cikin sati ukun da muka yi ya tilasta min sabawa da lalurarshi akan dole na hakura da hakan don babu dama yaga na bata rai sai ya ce min raguwa kawai, yara kanana ma ana aurensu su zauna kalau da mazansu balle ke bari muna komawa gida naga za ki sake kawo min wani sakarci sallamar Baba Talatu zanyi daga nan ta koma gida ta zauna tunda ba ki fahimci adalcina ba kina so ki fake bayan kunyar ta da nake ji ki takura min.
Ban ce mishi komai ba har muka gama abin da zai yi muka dawo gida, a Legos muka sauka wurin Baba don yi mishi bayanin komai, Ummanane a wurinshi don bhaka ba karamin sauka muka samu ba. Bayan mun gama cin abinci falon Baba ni da Umma muka dawo dakinta muna shiga ta ce mun kinga kyan da kika yi kuwa, ko kuwa dai kin tsallake wata ne?
Na ce kai Umma kenan, na ki maganar ta ce cika na soma yi mata kukan shagwaba ina fadin, bana son abin da kike yi min Umma, ta ce to na daina, na daina Adawiyya.
Ba mu dawo gida ba sai da muka je gidan yaya Junaidu wanda a yanzu na fahimci kawunane kanin mahaifiyata uwa daya uba daya, ita tasha nono ta bar mishi.
Wata sabuwar mu’amalla muka yi tsakanina da Yaya Junaidu, girman darajarshi ya karu a idona shima ya kara kamewa sosai alamar dai ya na game matsayinshi a wurina, itama Anti Rahma kauna mai yawa ta nuna min da kulawa da zamu tafi kuma sai ta ce min ke ‘ya ce a gidan nan kawunki ya riga yayi min bayanin komai don haka bai yiwuwa ki shigo gidan nan ki fita ba tare da kin ce ga abin da kike so ba, na yi murmushi na ce Anti Rahma Philipine muka fito kan hanyarmu ta dawowa kuma mun tsaya a Dubai.
Ta ce ko a ina kika tsaya ai bai wuce in yi miki kyauta irin ta uwa ga ‘yarta ba, na ce haka ne Anti, to hijabin dake jikinki yayi min kyau ina son shi, warddrop ta bude ta debo mun sabbi guda shida tana zuba min su cikin ledar shagon da aka saye su tana gaya min ai fitinar kawunki yawa ne da ita wai har a cikin gida bai yarda in rinka yawo haka ba, saboda masu shigowa gidan nayi murmushi na ce yana da gaskiya Anti, mun fito falo inda su yaya Almu suke na zauna cikin ladabi ina yiwa Yaya Junaidu sallama sai ya ce min haka za ki fita ba ki dauki komai a gidan ba? Na ce na dauka na samu hijabai masu kyau wurin Anti Rahma, ya ce to madalla ku gaida gida.
Mun dawo gida ni da yaya Almu abin gwanin sha’awa amarci sosai muke yi ni da shi, jin juna a rai muke yi yaya Almu ji yake tamfar ya lashe ni don dadi, ganin na saki jiki dashi na daina tsananta yi mishi rowar kaina sai dai in yi mishi shagwaba. Mun yi matukar shakuwa tamfar dai auren namu ba sabo ba ne, ko da dai dama can akwai sabo da shakuwa mai yawa a tsakaninmu, to amma kuma ai shakuwar miji da mata daban ne tunda shakuwa ce ta aure.
Muna isowa gida a dakin Yaya Almu muka tare abin da ya ce kenan hakan kuwa nayi mishi sai in wuni in kwana ban shiga wurina ba in har ba bakuwa ce tazo ba ma dakinshi komai zanyi anan nake yi nasa hannu biyu na karbi hidimar mijina da gidana, gaba daya kowane lokaci cikin shirya mishi nau’o’in abinci iri-iri nake yaya Almu mutum ne da ya san darajar mace ba mutum ba ne da ya damu da ya zauna komai sai anyi mishi in ma yaga zanyi dawainiya mai yawa zai taya ni zai kuma gaya min duk wannan abin da kike yi fa yi kike yi kawai don neman lada amma muhimmin aikinki anan gidan shine gyara mun shimfida.
In ce mishi kai yaya Almu kar fa Baba Talatu ta ji ka, murmushi yake yi ya ce ba komai don ta ji ni tasan gaskiya nake fadi.
Ina jin dadin zama da Baba Talatu ina kuma son zama da ita din a yau kuma ban dauke ta mai yi min hidima ba na dauke ta wani bangare nawa tanfar uwa musamman da na gane son da take yi mun na gaskiya ne, tunda taga zan bata wa mijina tayi maza ta shaidawa Ummana tazo tayi gyara ban da haka baba Talatu mai kamun kai ne mai rike girmanta ganewan da tayi yaya Almu ma’abocin shiga kicin ne in har ina ciki in ta ganni zan yi girki tasan yana gida kauda jikinta take yi ta shige wurin ta, da nayi mata magana sai ta ce min Lamido mai kunya ne bai, kamata in rinka nema in takura mishi ba, ganewar da nayi Baba Talatu tana sona tana kuma son mijina sai na kara sonta da ganin girmanta.
Rannan muna hira da Baba Talatu a tsakar gida saboda yaya Almu baya nan yana Abuja, don yana da case a babbar kotun Abuja, wato (Court of Apeal). Baba Talatu bani wani tsohon labari na wani abin da aka yi tun ina ‘yar karama sai da na gama sauraronta naji tayi shiru sai na ce mata Baba za ki yi mana girki ne yau? Ta kalle ni ta ce saboda Lamido baya nan shi ne ba za ki yi mana ba ko? Na yi murmushi na ce a’a Baba bana jin dadi ne kawai yau kuiya nake ji shi yasa na ce bari in huta, ta yi murmushi ta ce sai in yi mana ai ma ina ganin kokarinki ke cikinki bai saki wani laulayi mai tsanani tanfar ba cikin fari ba.
Nayi murmushi na ce tafdijan, wai ni me yasa ake yi min haka ne Baba? Babu dama in dan yi wani abu sai ace ciki Umma ta ce ciki yaya Almu ma haka gashi kema kin fara, ta ce eh ai kinyi kama da mai cikin ne kinga yanda kika dawo kuwa? Na ce to bani da komai sai na gama cin amarcina tukuna, tayi maza ta ce uh’uh kar dai kiyi wani abin da za ki kwari kanki ciki ba zai hana ki Cin amarci anan gidan ba sai dai ma ya kara miki ba sai na tsaya ina gaya miki darajar dan da za ki haifarwa Babangida ba, kin kuma Sani sarai uwarki zata fi kowa murnar ganin hakan.
Kwanaki kadan bayan nan na samu kaina cikin al’ada, yi alwala ki zo muyi sallah kinga ban samu jam’i ba a masallaci, yaya AImu ne ya ban wannan umarnin, sai na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi, ai da na je wanka dazu sai naga al’ada tazo min shi yasa ban yiwo alwala daga can ba, abin da kawai na gaya mishi kenan ya tsuke fuska tanfar wani mummunan labari na bashi.
Cikin dare muna kwance na farka daga bacci na ganshi ido biyu, me ya faru yaya Almu ko kana da wata shari’ar ne gobe? Ya dan yi ajiyar zuciya kadan ya ce, al’adarki ce ta ishe ni, ni tana takura min a dalilin in tazo bata daukewa da wuri, gashi kuma dama na tsani ganin kina yinta, na ce ba ka son ganin ina yi fa ka ce?
Yayi maza ya ce eh bana so shiga tsakanina dake take yi tsawon kwanaki bakwai ban da haka kuma na gaji da ganinki haka so nake in ganki da ciki Rabi, ya zuba min ido cikin natsuwa yana kallona, na dan matsa kusa dashi don in kwantar mishi da hankali sai na ce mishi ai amarci muke yi yanzu yaya, yayi maza ya ce bana son amarcin ya ishe ni haka tunda ke a wurinki in an samu ciki amarci ya kare ne, kina nufin ki ce min sauran ‘yan matan dukansu sun daina amarckine? Ke kadai ce ba ki da komai Rabi in ba ki sani ba in gaya miki, a hankali na ce mishi in mana sani amma yaya zanyi laifina ne? Na soma yi mishi kuka, yayi maza ya soma rarrashina ba laifin ki bane Rabi nima na sani yi hakuri kiyi hakuri kiyi shiru amma ina so ki fahimci cewar ba amarcine muhimman abu a wurinmu ba, muhimman abu shiine mu samu haihuwa kema kin san Umma da Baba suna Bukatar ganin danmu kema kin sani sarai cewár babu wani da da zai debe musu kewar son ganin wanda zamu haifan musu don haka ina rokonki in akwai wani abin da kike yi ki daina don ina yawan jinki kina ambaton amarci nayi miki alkawarin daga ranar da kika tabbatar mini da abin da nake fatan gani a tare dake zan shigar dake cikin amarcin da baki taba sanin shi ba, a hankali cikin sanyin jiki na ce mishi bana yin komai yaya ya kara jawo ni jikinshi yana fadin na yarda Rabi na yarda ba za kiyi abin da zai cutar damu ba, don haka daga yau mu shiga yin addu’a kinji ko? Na ce mishi to.
Tun daga wannan ranar yaya Almu ya dora min karanta suratul Maryam, kullum bayan kowace sallah ta asubahi, shi kuwa dama ma’abocin karatun Alkur’ani ne. Muna gaf da cika wata tara cif da yin aurenmu sai kawai akayi waya aka ce wai Anti Aina’u ta haihu, an samu da namiji, tafdijam na kalli yaya Almu na ce mishi ba mu ma fa cika wata taran ba saura kwana goma, ya daure fuska ya ce to sai me, Ance miki dole ne sai kowa ya kai wata tara daidai? Ko kuwa a lissafinki ne ba a cika wata tara ba awatan kalanda mu anamu lissafin an kai, naja bakina nayi shiru saboda ganin canzawar fuskarshi.
Mun dawo daga sunan Anti Aina’u da kwana biyu, Anti Kubra ta haifi ‘ya mace, kwana uku bayan nan sai ga waya daga Legos cewar Anti Rahma ma ta haihu kuma da namiji aka samu, cikin daren muka isa Legos saboda bamu iya hakurin bari sai gari ya waye ba.
Hankalina bai tashi ba na samu kaina cikin tsananin damuwa sai da naga mun shiga wurin Umma don yi mata barka, maimakon tayi murnar ganinmu ni da yaya Almu kamar yadda ta saba yi wai sai kawai ta fashe da kuka, kuka kuma mai tsanani, jikina yana rawa na durkusa a gaban Umma na ce mata Umma don ban haihu ba ne kike kuka’? Umma ai zan haihu zan haifanwa yaya Almu da wanda za ki rike ki rene shi kiyi mishi riko irin wanda kika yi min, Umma me yasa zaki yi min haka? Ina fadin hakan nima na soma yi mata kuka bama irin wanda take yi ba saboda zuciyata ta soma karaya.
Yaya Almu yayi ta baiwa Umma hakuri wacce ganin kukan da nake yi yasa ta hakura da nata kukan tayi shiru, shi kuma yaya Almu sai ce mun yake yi ke kin yi magana mai dadi kin zo kuma kina kuka, yi hakuri kiyi shiru Rabi, nima zuciyata tana gaya min cewar za ki haihu, Rabi za ki haihu ya’ya masu yawa ma ba daya ko biyu ba.