Duk da ban wani samu isasshen bacci a cikin daren ba, ga gajiyar wahalar biki ga rashin bacci da suka hadu suka haddasa min ciwon jiki mai nukurkusar kashi.
Da gari ya waye na yi kokari na fito bayan na idar da sallah na shiga kicin na fara shirya abin karyawa saboda Ango da Amarya da kuma sauran Jama’ar dake gidan. Tunani sosai nayi don in shirya abin da zan gamsar da mutane, sai da na dama kunun gyada na shinkafa nayi alala sannan na shirya potato da corned Beef ga abubuwan da nayi amfani da su:
(1) Dankalin Turawa manya takwas
(2) Butter cokali takwas
(3) Albasa guda biyu manya
(4) Naman jajjagagge daidai kima.
(5) Kayan kamshi dan madaidaici
(6) Dessert Apple guda biyu manya
Da yake abincin nawa bai wuce na mutum hudu ba, to ga yanda nayi na sarrafa komai, wanke dankalin nan nayi sosai ya wanku da kyau ba tare da na fere shi ba, na ajiye shi wuri mai tsabta sai da ya bushe sannan na goga mishi butter na dora shi kan bakin sheet na saka sh1 a oven ya gasu na kusan awa daya cikin madaidaiciyar wuta sai da naga ya gasu. Sannan na ciro su na kwakule cikinshi sai dai na kiyaye ban lagabar dashi ba ban kuma huda wani bari ba, na kawo jajjagagren naman nan na hada da wannan garin dankalin da na kwakwale na hada da maggi yankakken apple din nan da kayan kamshi na cakuda shi da albasar da na soya cikin butter tayi laushi sannan nayi ta cusawa cikin dankalin nan sai da na gama maida shi ciki gaba daya na sake sanyawa a oven ya yi ta gasuwa kafin na sake ciro shi na sanya shi cikin kwanon da na tanada mai tsabta.
Ina cikin kokarin dora ruwan zafin da na tafasa cikin flask sai ga Baba Talatu ta shigo sannu da aiki uwar dakina, na ce yauwa Baba kin shigo? Ta ce mun eh, ta kuma kara marsowa kusa dani alamar wata magana zata gaya min, don haka na kara bata hankalina. “Kinga idon wannan yarinyar kuwa? Ta yi mirsisi da ita ni nace anya ma ihun nan da take tayi jiya na kama hannunne kuwa da gaske?
Banga alamar ta kai budurcin nan ba.” Na ce “Baba”
Ta ce “Na’am.” Na ce “Mu bar wannan magana.” Ta ce “To.” Ta shiga taya ni kintsa wurin zuwa can sai na sake jin ta ce min “in banga maigidan yayi wankin kayan shimfida ba irin na wancan karon anya budurcin nan..Nayi maza na katse ta na ce “Baba Talatu daina yi min wannan maganar, tana fadar min da gaba, don bana son jin ta wannan abinda ya shafe su ne ita dashi bai shafe ni ba.” Daga bayana na ji muryar Yaya Almu yana cewa, “menene bai shafe ki ba? Baba Talatu tayi maza ta fita ni kuwa na soma gaishe shi bai wan1 amsa ba ya kara matsowa gab da jikina, me zan samu Rabi? Na sunkuyar da kaina don bana son kallon fuskarshi, na ce duk abin da kake so akwai, ya ce ‘to in dai haka dan fara bani bakinki in ji kwananshi, in ji laushin labbanki, nan da nan wani abu ya tokare ni a zuci har ban san lokacin ‘da na bude baki na ce mishi, uh’uh in baka ji wadannan ba ai ka ji wasu..bai bari na karasa ba ya ce mun kul, kar ki rinka irin wannan maganar in ina tare dake ina tare dake in bana tare dake kar ki yarda zuciyarki ta raya miki komai ki dai yarda kawai a duk inda nake ina kewarki ina kuma son ganinki a gefena, na ce haka ne.
Na kammala shirya komai kan tire na dauko na barwa Yaya Almu wanda zai taimake ni dashi juyowan da zanyi sai kawai naga Lailatu tana lekowa ta matsin kofarta tana kallon abin da ke faruwa tsakanina da Yaya Almu. Na yi kamar ban ga abin da take yi ba, na wuce naje na shirya komai.
A falon shi na sake dawowa na shiga dakin nata nace mata Amarya ina kwana? Ta ce min lafiya, amma dai sunana Lailatu, na yi kamar ban ji ta ba, na ce mata ki zo falo maigidan yana jiranmu, na juya na fita na barta.
Mun zauna muna karyawa dukanmu muna kuma hira dukanmu saboda kokarin da Yayan ya yi wajen ganin ya tsoma kowa cikin maganar tashi, da aka natsu sai ya kalle ni ya ce mun Rabi ga Lailatu nan na sani kishiyarki ce, to amma zan so ki maida ita yar uwa ki yarda cewar taki ce zaki yi mu’amalla da ita bisa adalci ba don kowa ba sai don ni, tunda kin san ni na kawo ta na kuma san za kı iya yi min adalcin maida duk wani abu nawa ya zama naki ko da kuwa ba akan son ranki yazo ba, saboda kin san duk wani abin da ya shigo gidan nan arzikinki yazo ci in kuma mallakarshi nayi to na ki ne.”
Cikin natsuwa ba tare da zuciyata ta raya komai ba, na ce mishi haka ne, sai kuma ya juya wajen Lailatu ya ce mata, ke Lailatu ga Rabi nan matata ce, ko babu aure tsakanina da ita kuma ‘yar uwata ce na kuma san duk yanda kishi yakai da zafi cikin zuciyar ta a ifin halinta da na sani da kuma irin tarbiyar da aka yi mata zata yi iya kokarinta wajen ganin tayi miki adalci, to ki bata hadin kai ki bata girman da ya dace da ita don ina bukatar ganin kun zauna lafiya kun samu fahimtar juna a tsakaninku.
Wannan shi ne sha’awata da burina game da mata biyu, ke Rabi kinji abin da na ce? Na ce mishi eh, naji Allah ya taya ka riko, ya yi maza ya ce min “amin, Lailatu dai bata ce komai ba har na fita.
Zuwa can wajen karfee sha biyu da rabi bayan fitar Yaya Almu, ina falona ni da Baba Talatu ina kuma hango duk abin da tsakar gida ke ciki, yayin da Lailatu ke falonta tana kallo sai ga Umma Karama da Hajiya Hairan sun shigo gida da sauri na fito ina yi musu sannu da zuwa na kuma jagorance su don in kaisu dakina duk da dai nasan Umma Karama bata taba takowa tazo gidan saboda ni ba, to amma sanin da nayi cewar duk bakon da yazo gidanmu matukar ya fara ganin Umma to ko ba wajenta yazo ba to wurinta zata fara sauke shi ta bashi ruwa da abinci kafin tasa a kai shi wurin wanda yazo, to balle Umma Karama duk yanda takai da kina dolenta ni ‘yarta ce, kan idonta aka haife ni ko babu wata alaka tsakanina da Baba ta dalilin Umma kawai ita uwata ce, balle kuma inta juya ta wurin Baba ni jikarta ce har yanzu kumna surukarta matar dan mijinta, amma bata şhiga dakin nawa ba sai ta ce min na rako Hairan ne tazo taga dakin Amarya, bari mu fito tukuna. Cikin murmushı na ce mata to, na shiga kicin na shirya abinci na bisu dashi zuwa dakin Lailatu na shiga na same ta tana cewa, in ana zancen aure ai babu maganar zumunci a ciki dukanku daya ne dukanku daidai kuke in ta dauro ma kwanan nan sai ki kwace shi tunda ke kam ai matar haihuwa ce kadan ya rage banyi bari ba, nayi maza na shanye bugun da zuciyata tayi nayi sallama suka amsa na shiga na kai musu abin da na shiryo musu na kuma gaishe su har na tsaya ina tambayar Umma, Umma daga Legos kuke ne? Ta ce a’a a satin nan ne dai zan tafi na ce ai, na tashi na tafi nawa wurin da suka gama abin da zasu yi kuwa daga tsakar gida ta yi mun sallama wata kilama da ban ga fitowarsu ba da tafiyarsu kawai suka yi ba tare da sunyi min sallamar ba.
Baba Talatu ta kalle ni ta ce tafdijam, wannan mata da rashin mutunci take in ban da Hajiya ta samu da ba a san irin tsiyar da ta yiwa mutane ba, na yi dariya kawai na tashi na nufi kicin don shirya abincin rana. Ina shiga kicin din sai ga Yaya AlImu ya dawo cikin kicin din ya biyo ni, na kalle shi cikin murmushi na yi mishi sannu da zuwa, ya kalle ni cikin wani murmushin mai gamsarwa ya ce min ran uwargida ya dade, na daga ido na kalle shi kamar in yi mishi wata magana in gaya mishi bana son sunan sai kuma na fasa na sunkuyar da kaina kawai da nufin in kama aikina, sai na ji ya matso kusa dani sosai yana fadin ke uwargida ce Rabi duk da mas’alar da muke da ita kuma zuciyata tana raya min cewar kcce uwar iyalina, musamman ma da yake a yan kwanakin nan ina mafarkin kin haifar mun ya mace, na yi murmushi saboda jin dadin kalaman nashi, na jawo kayayyakin da na hada zan soma aiki na sai ya ce mun me za ki shirya mana ne yanzu kuma? Na ce mishi stuffed chiken (2) in ba ka manta ba ka taba cin 1), din ya ce ch ban manta ba Rabi duk da dai na cishi ne tun ina saurayi, to gaya min me dame ki ka tanada? Na ce mishi gasu nan a gabanmu kana kalio sai dai hakan ba zai hana in gaya maka sunayensu ba:
Kaza, Butter, shinkafa, kayan lambu, nama, curry, sai kuma maggi. Juyowan da nayi na hango Lailatu tana leko mu ta matsin kofarta yasa na ce wa yaya Almu jeka wurin amarya yaya in na gama zan zo in same ku bai yi musu ba ya juya ya tafi.
Na kama aikin abincin san zuciyata a kuntace saboda ba wastsakewa nayi daga zafin kishin dake cina ba, gashi kuma na gane ita Lailatu bata shigo gidan da niyyar yarda da tayin zaman lafiyar da ni da Yaya Almu muke gabatar mata ba idonta da hankalinta gaba daya to kan mu’amala ta da mijina take duk da cewar shekaran jiya ne kawai ta shigo gidan wannan in ta yi kwanaki yaya za’a kwashe da ita? Wannan ita ce tambayar da tazo cikin zuciyata, gani kawai nayi na gama girkin amma ban san yanda aka yi na hada komai ba, saboda tsananin tunanin da na samu kaina a ciki har na kammala na shirya komai kan tire na dauko na nufi falon Yaya Almu ban san da wani a ciki ba don haka ban wani tsaya yin doguwar sallama ba na tura kaina cikin falon jikinshi na same ta tana yi mishi wasu abubuwan da nayi maza na kawar da kaina daga gare su, naje na ajiye musu abincin duk da ba yunwa nake ji ba na zauna muka ci tare don kar in basu damar da zasu gane na samu wata damuwa, sai da aka gama na tashi na tafi wurina.
Da daddare ma na sake shirya tuwon Semovita miyar kuka da kuma farfesun bindin saniya, ina idar da sallar Isha’i nayi wanka na hau gado na na kwanta da nufin in yi wadataccen baccin da zan ji dadi in samu naatsuwa a jikina sai dai kuma kash! Hakan bai yiwu ba ina rufe idona da nufin yin bacci sai inga Lailatu a jinshi tana tuhumarshi irin dai yanda na same ta tana yi mishi sai kuma in ji zuciyata tana raya mun cewar yanzu haka ma abin da ke faruwa a tsakaninsu kenan, na yi kuka rannan har na gaji saboda ganin abin da ban taba ba kan na farko ken an da naga wata mace tana taba Yaya Almu a tsawon rayuwata tare dashi.
Nayi matukar kokarina na shanye komai na hadiye duk wani abin da ya dame ni na yiwa Yaya Almu da Amaryarshi duk wani abin da ya dace in yi musu na kyautatawa a tsawon kwanaki bakwai din da yayi a dakin nata, duk da kasancewar kwanakin masu tsanani ne kwarai a gare ni.
A haka rannan ya dawo dakina bai jira naje nashi dakin ba wurina yazo ya same ni sai dai duk kokarin da nayi na in nuna mishi bani da wata mas’ala na kasa sakin jikina dashi sosai, ya zuba min ido yana kallona saboda ya gane abin da nake nufi a hankali cikin natsuwa da murya kuma irin ta rarrashi ya ce min auren da na yi fa bai canza komai ba tsakanina dake sai ma kara wa da ya yi saboda a yanzu babu abin da nake tausayi kamar ki ina ji ya ambaci tausayi sai na ji zuciyata tana raya min cewar saboda yasan ya cuce ni, nan take na kama yi mishi kuka, na yi kuka irin wanda ban taba yi ba, na yi kukan da tun yana rarrashina cikin tausayi har ya gaji ya ture ni ya fita daga dakin ba zan iya wannan zaman ba ba zan iya ba, abin da zuciyata take gaya mun kenan, na mika hannu na kira Umma da nufin in gaya mata cewar ta yafe mun tayi hakuri ta bar ni in yi abin da naga zai fiye min sai na ji muryar Yaya Junaidu yana cewa, Hello Adawiyya yi magana magana, menëne? Ashe lambobinshi na danna ban sani ba nayi maza na kashe wayar na maida ita na ajiye sai dai kuma kama ruri tayi shi ne ya sake bugowa cikin natsuwa nace mishi kayi hakuri Umma nayi nufin kira ya ce da wannan tsohon daren za ki katse mata baccinta? Na ce ar na fasa ya ce min to sai da safe, na ce to mu kwana lafiya na maida ita na ajiye sai dai kuma gari yana wayewa da yaya Junaidu muka karya a gidan da sunan wai yazo ganin Amarya yayi wa yaya Almu fatan alheri ya kuma yiwa amarya kyauta sannan ya nemi izini Yaya Almu ya biyo ni har cikin falona, nasiha mai yawa yayi min ya kuma nuna min muhimmancin in yi kokari ina boyewa Umma damuwata saboda ita din ta riga ta fara girma na ce mishi to ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min in kina da damuwa rinka gaya min zan taimake ki da shawarwarin da zasu taimake ki, na sake ce mishi to ya sake kallona ya sake tambayata yanzu menene damuwarki? Na ce mishi ina so in yi nesa da Yaya Almu ina so in daina ganinshi a kusa dani, ya sake zuba min ido cikin natsuwa ya ce min amma kin san mijinki ne, wannan aure da yayi kuma ba laifi yayi ba halal dinshi ne, na ce eh, ya ce to kar ki yawaita tsananta al ‘amarin a wajenki ki dauki komai da sauki zan kuma shirya miki tafiya Umra don ki je kiyi ziyara a Madina na ce mishi to.