Skip to content
Part 39 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Sati guda bayan nan komai ya kammala na shirye-shiryen tafiyata saura tashi kawai, amma sai Yaya Almu ya yi kasa kasa ya ce babu in da zani saboda ba a nemi izininshi ta hanyar da ta dace ba, hanyar da aka bi wajen sheda mishin ya fi yi mishi kama da sanarwa maimakon neman izini.

Ina zaune a dakina cikin bakin ciki da takaicin abin da ya yi na neman ya kuntata min tunda sau nawa Yaya Junaidu yana shirya min irin wannan tafiyar bai tába cewa bai yarda ba sai a wannan lokacin, wannan neman kuntatawa ne kawai abin da zuciyata ta raya min kenan. Ya shigo dakina ya same ni don ranar ma girkina ne, na daga ido na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi me ka ke nufi da hana ni tafiyar da kayi? Ya cc abin da nakc nufi kenan ki gane zan iya nukurkusa ki in saki bakin ciki matukar ba ki janye daga matakan da kike dauka ba, na zuba mishi ido ina kallonshi, sai ya ce min kalle ni da kyau rabi don ki kara gane ko wane iri ne na iya yin rarrashi in yi alheri in kuma saka mai kyau da mai kyau kamar yanda zan iya kuntatawa in saka munmuna da munmuna in halin hakan ya kama, ina yi miki wannan bayanin ne don in fahimtar dake ki gane cewar babu abin da zai fi zaman lafiya da bai wa juna hakki dadi a tsakanina dake, na rasa abin da zan ce mishi sai kawai na kama yi mishi kuka ina tambayarshi me nayi maka Yaya Almu? Me nayi maka ka tsane ni ka ke nema sai ka gana mun azaba? Me nayi maka da zaka tsare ni a cikin gidanka ka hana ni zuwa in da zan ji sanyi bayan ba sona kake yi ba, na gama kukana na mike na wuce shi zan shiga cikin dakina in kwanta yayi maza ya mika hannu ya kamo ni na fada jikinshi zo ki gaya min abin da nayi miki wanda yasa kika ce bana sonki ina kuntata miki? In ina sonki me kike so in yi miki bayan wulakancin da kike yi mun yaushe rabonki da ki gyara mun shimfida?

Rannan dai dole na na yarda muka shirya da Yaya Almu saboda yayi rantsuwar ba zai yarda da danne mishi hakkinshi da nake yi ba, ganin mun shirya yasa na sake rokonshi ya bar ni in je in yi Ummara ya ce ba yanzu ba zai shirya mun hakan a lokacin da yaga ya dace, amma yanzu ga Lailatu bakuwa bai kamata in fita daga gidana in bar mata shi ba da irin wadannan kalaman nashi ya kwantar min da hankali.

Lailatu ba ta yi kama da amarya budurwa mai gane al’amuran gidan aure a hankali ba komai ake yi idonta yana kan duk da haka dai ina iyakacin kokarina wajen ganin na kawar don kaina, don in samu in cika umarnin da Umma ta bani na yi mata girgi tsawon watanni biyu wai taci amarci.

Rannan da safe naje zan shiga dakin Yaya Almu sai na ji ta a ciki tana ce mishi ni fa na gaji da karbe mun kudin cefane da ake yi da sunan wai ana taya ni girki, daga yau a rinka bani kudina a hannuna ina yin lissafin cefanen in an kawo sai ta girka in har abin kirkin take son yi maka da gaske ba iya yi ba, ba na son kina fadin irin wadannan kalmomin akan Rabi Lailatun rannan na gaya miki bana so maganar kudin cefane kuwa ni ban saba bayarwa ba mafi yawancin lokaci ma ni bana sanin loka cin da ake kawo abubuwan da ake amfani dasu a gidan nan, na koma da baya na koma wurina na basu wuri su gama maganganunsu sai da ya gama abin da zai yi ya fito yazo wurina zai yi min sallama ya miko min kudi ya ce ku raba ke da Lailatu wannan kuma ki bai wa Baba Talatu, nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya naje na bai wa Baba Talatu dubu goman da ya bata tayi ta godiya tana sa mishi albarka ita kuma Lailatu naje na ce mata amarya gashi in ji maigida dubu hamsin ne amma ko a ikinta na fito abina na dawo na same shi na ce mishi dukansu sunyi godiya muka gama maganar da za muyi da zai fita sai na ce mishi zan bai wa Amarya girkinta yau tunda kaga tayi wajen kwana arba’in a gidan nan gara muci irin nata girkin kuma muji irin dandanonshi bai yi wata magana ba alamar bai so in yi hakan, ni kuwa yana fita sai na kwala mata kira amarya, ta fito tazo ta ce mun gani, sai dai ni fa sunana ba amarya ba ne, ta yi maganar tana cune da baki na ce ni kuma sunan da nayi niyyar kiranki dashi kenan, Amarya ki shiga kicin yau ki yiwa mijinki abinci ya ci, na wuce ta naje dakina na yi wanka na tsala kwalliya na fito na zauna a inuwa a tsakar gid aina kallon mu’amallar ta da kicin din nata na kalli Baba Talatu dake gefena na ce mata ina jin anjima zan bukaci shan kunun gyada ko za ki iya dama min? Ta ce yanzu kuwa uwar dakina ai ba ma sai anjima ba.

Da daddare ranar ina dakina naji muryar yaya Almu yana kwala min kira nayi maza na amsa na tafi kwanukan abinci na samu a gaban shi ita kuma tana zaune a gefenshi tasha kwalliya ga baki Yasha jan baki ita da kwanukan abincin nata sai sheki suke yi, ina ce mishi gani ya fara fada meye sunan wannan abincin da ki ka kwaba yau? Ban ce mishi komai ba sai ta yi maza ta ce mishi ai ni na yi bai yi dadi ba ne? To bari in sake shirya maka wani ta yi maza ta suri kwanukan ta fita dasu ta koma kicin nima na juya zan koma dakina sai ya yi maza ya kira ni me yasa kika bata girki ba da izinina ba? Na ce saboda na gaji na wuce na fita na koma dakina ban tsaya a falo ba don ganin ya biyo ni dame kika gaji? Da abincin da za ki girka min in ci? Me yasa kike nema ki koyi rashin kirki da can shekara nawa ki ka yi kina yin girkin ke kadai? Nayi shiru yayi ta maganganunshi sai da naga bai gane zurun da nayi mishi ba sai na ce mishi ai nayi kokari in ma kai baka gani ba ni na gani kwana arba’in ina yi muku girki sanda aka kawo maka ni ai shekaruna basu kai nata ba ni sha tara ce a lokacin ita kuwa an kawo maka ita da ashirin da uku, ni a wancan lokacın waya rinka yi mun girki, tunda ta iya gyara maka shimfida ai sai ta iya baka abincin da zaka rinka ci, zuba mun ido yayi cikin takaici sannan yaya wani mummunan tsaki ya fita.

Tun daga wannan lokacin kullum ran girkin Lailatu ta rinka dibi-dibi kenan a kicin babu abin da zata girka ya gamsar gashi ita kuma fadin rai ya hanata ta rinka neman taimakona kamar yanda naji mijin nata yana bata shawara rinka yiwa Rabi dabara kina tambayarta wasu abubuwa zata koya miki ita ba mai ganin kyashi ba ce, bata bi shawarar tashi ba nima kuma ban yi karambani na tsoma kaina cikin lamarin ba, duk abin da ta girka dai ina kokarin in ci don kar ace aba ci mas’alar tsakaninta da shi ne don bai yarda ya ci abin da bai kwanta mishi ba, na maida ranar girkina lokacin shiryawa yaya Almu nau’o’in abinci iri-iri, kuma kala-kala in kuma tsala mishi kwalliya ta burgewa gani kuma da daukar kwalliyar gashi kuma dama ba wasu shekaru masu yawa na baiwa Lailatu ba ni ina tsakanin ashirin da hudu ne zuwa da biyar yayin da ita kuma take da ashirin da uku tazarar tamu ba mai yawa ba ne in ta dauro ma sai ayi ganin girmanta don ni jikina ba mai budewa ba ne da sauri ita kuwa daga zuwanta har ta fara habakewa in ina tare da Yaya Almu mancewa da komai yake yi ya tasa ni a gaba ya raba dare wajen jiyar da kanshi al’amuran da zai iya abin da yayi matukar damun Lailatu don nasha jin ta tana yi mishi kunkuni a duk lokacin da ta zo tana yi mishi magana ta ganshi yana gyangyadi a kishingide sai ka ji tana cewa eh ni kam ai in ina tare da kai ba ka da wani aiki sai na ramakon bacci tunda in kana can kwana kake yi idonka biyu, ko shi bai ce mata komai to balle ni kuma da dama maganar bata shafen ba.

Tun daga wannan lokaci sai wani, irin rashin lafiya ya same ta na kullum in ni ce da girki sai cikin dare kamar goma zuwa da rabi ya gama Kallon labaran kasa zai yi wanka ya yi shirin kwanciya sai ka ji ta kurma wani irin ihu mai tsanani daga cikin dakinta in anje ganin abin da ya faru sai a sameta amimmike babu numfashi. Yaya Almu ya yi ta faman fifita yana tofa addu’a iri-iris sai kuma ta kama buge-buge tana furje-furje tana wani irin gurnani, Lailatu, Lailatu yana kiran sunanta sai ka ji an ce kai kul shiga hankalinka ba Lailatu ba ce wannan, da sauři ya ce to waye? Sai a fadi wani suna na daban, na ce to ko zamu kaita asibiti ne? Sai kawai aka daka mun tsawa da wata irin murya mai ban tsoro matsa can munafuka ke munafuka ce ba ma son ganinki a kusa damu, da sauri Yaya Almu ya sake cewa ke Lailatu menene haka? Aka ce kai kul ka sake kiran wannan sunan an gaya maka wannan ba Lailatu ba ce Zubaida ce mun zo ne mu tayata murnar aure da kuma bakin cikin shanye mata miji da aka yi ta auri sammatacce an maka sammu an sihirce ka baka, da katabus sai abin da aka shirya maka baka gani saboda an rufe maka baki da ido, tsawon lokaci ana amfani da bakin Lailatu wajen aibanta Umma na duk wani tsohon abin da aka yis ai da aka fade shi na gaskiya da na sharri duka wai mutanenta ne masu maganar ba ita ba ce ina kallonta ina kuma kallòn Yaya Almu dake faman to fa mata addu’o’i, a haka muka kwana sai kusan Asuba ta dawo hankalinta bayan ta yi atishawa mai karfi guda biyu, tana bude ido ta ganmu kuma sai ta fa she da kuka Yaya Almu ya yi ta rarrashi nima: nayi mata sannu na ce mishi bari in je in dan mike tunda ta dawo cikin natsuwarta ya ce min to Rabi sannu kin ji? Bari in dan kara zama kadan don ba zai yiwu mu tafi mu barta ita kadai ba, don kar wani abu ya sake faruwa na ce mishi to

na tafi na bar su.

Tun daga wannan lokaci wannan ciwo na Lailatu ya zama mishi ka’ida kullum ranar girkina sai ya tashi ya yi dalilin da ya raba nr da mijina sai ya koma-dakinta sai a kwana lafiya ban taba cewa yaya Almu komai ba, tunda nasan shi kam da zuciya daya yake yin komai, Lailatun ce dai rannan tazo zata wuce ni ina zaune a tsakar gida yayin da Baba Talatu ke tsefe man kaina sai na ce mata zo nan Amarya, ta matso ta zauna kan kujerar dake Kallon tawa, na kalle ta nayi murmushi na ce mata, Amarya kenan, ba zan daina ce miki amarya ba saboda iyayenki ba su gaya min sunanki ba da suka kawo ki dakina, cewa suka yi ga amarya sun kawo sai dai tazo ne zata zauna ba ta leko ne zata koma ba, ko ba haka suka fada ba? Zuba min ido ta yi tana kallona don bata taba jin nayi mata irin wannan maganar ba, na ce to kema kenan balle ni don haka na kira ki ne in baki shawara ki gayawa mutanenki dake zuwa cewar in sun zo su rinka tsayawa kan abin da ya kawo su kawai su daina zagan min uwa suna aibantata, in ba ki sani ba kuma in gaya miki ni da kike kallona babu abin da ban iya ba, duk abin da naso yi kuma ina kwatantawa, don a shekaruna na kuruciya yaya Aimu ya kai ni maka rantar kwana don haka suma irin wannan da kike yi ina ganin kamar zan iya yin wanda ya fishi tunda ai ke an ce jeka ka dawo ma kika yi ko? Jikinta yayi matukar yin sanyi da maganganun da nayi mata har na tashi naje na kama aikina bata motsa ba.

Rannan kuma sai muka kwana lafiya ni da mijina mutanen Lailatu bas u zo sun shiga tsakaninmu ba, sai girki biyu bayan nan sai kuma aka sake, don haka nima ranar girkinta sai nayi mata irin nawa suman da na iya wanda ya bambanta kwarai da wanda take yi. Yaya Almu ya kwana yana dibi-dibi a kaina ita cikin matsanancin tashin hankali har yana kwalla yana gayawa Baba Talatu cewar tunda yake bai taba sanina da wata matsala ba sai yau.

Wajen karfe hudun asuba na farfado na tashi na zauna cikin natsuwa ina magana da kyar-da kyar na ce mishi jeka ka dan huta Yaya, ya ce to Rabi gobe sai muje asibiti, na ce mishi to, ya tashi ya nufi dakin Lailatu don ya dan huta kafin ya nufi masallaci kamaar yanda ya ke yi a wurina in ta kwana da irin wannan ciwon sai kawai yake ya samu ta garkame kofa bude min mana Lailatu yaya za ki rufe min kofa? Tana daga ciki tace mishi ka koma can ka karasa kwana tueda kaje can ka kwana, ya ce a’a haba Lailatu lalurar rashin lafiya kuma wa ya fiki ciwo a gidan nan? Ta ce ai nata ciwon na karya ne, karya take yi lafiyarta kalua ciwon kare ne yayi juyin duniya ta nude mishi kofa taki har ya gaji ya tafi nashi dakin ya kwanta.

Gari na wayewa Lailatu tayi yaji ta tafi gidansu da yamma aka dawo da ita na shiga na gaida iyayen nata da suka rakota na fito naje na gayawa yaya Almu zuwansu shima yaje ya gaishe su inajin shi yana yi musu bayanin abin da ya faru yana kuma gaya musu ita Lailatun tafi kowa yawan lalura, suka ce eh ai ita dama haka take wani lokaci sukan tashi mata sai dai da tayi aure yanzu ne suka fi tashi saboda tana yawan samun bacin rai an gama maganganun sun tafi dare yayi yaya Almu ya nufi dakin amarta ashe wai zance bai kare ba a fusace na ji shi yana cewa, ke Lailatu kama bakinki ban saba irin wannan rashin mutuncin ba, ni mijinki ne ba’ayi miki tarbiyar girmama miji ba ne? Ban san me take fada ba sai ya shiga cewar ya ishe ki haka lallene kisan ya ishe ki Umma ba uwar Rabi ba ce tawa ce kama bakinki kiyi shiru watakila bata ji wannan kashedin da yayi mata ba ne cikin fusata mai tsanani don kuwa nan take naji ya rufe ta da duka mai tsanani yana dukan kuma tana zaginshi tana hadawa da Umman tana kwashe musu albarka abin da ya kara tsananta al’amarin.

<< Wace Ce Ni? 38Wace Ce Ni? 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×