Da gari ya waye shiryawa nayi na tafi gida nufina in je wurin Ummana in dan yi hira ko zan ji dadin zuciyata, ina zaune a gabanta cikin kwalliya sosai don dai taga kamar bani da wata damuwa, muna zaune muna hirarmu idanuwan Umma akaina suke ta zuba min su ko kiftawa bata yi ni kuma ina ta kokarin yawaita murmushi da fara’a a fuskata don dai ta dan ji dadi zuwa can sai naji ta ce min a dan tsakanin nan bana iya bacci Adawiyyah saboda nasan kina cikin wani hali, sannan a yanzu ramar da na gani a tare dake tafi komai tada hankali sai dai kuma hakan ba zai hana ni cewa ki kara hakuri akan wanda nasan kina yi ba, duk wanda ki ka ganshi ya yi hakuri bai ci nasara ba Adawiyya to bai yi hakurin mai yawa ba ne, na ce mata to Umma.
Ina zaune a gida bani da wani aiki sai na abincin gida da kuma sallolina dana sanya a gabana, saboda shi kanshi Yaya Almu in aka tambaye shi yaushe ne girkina? Ba zai iya fada ba, kullum dai nice a kicin nice mai abinci yayın da shi kuma yake wuni a dakin Lailatu, ya kuma raba dare yana tare da ita in kuma ya dan saci jiki ya shigo wurina to naan da nan mutanenta zasu tashi su yi ta furje-furje suna fadin maganganu na aibanta ni tare da Umma da fadin wai irin asire-asiren da muke yi mata suna zuwa suna tonewa kuma wai duk akan cikin da take dashi ne muke son barar mata, ni kam a yanzu ko mutanen nata sun tashi bana zuwa tunda na riga na san shakiyanci ne sai in bar shi shi kadai yayi ta Zirga-zirganshi.
Ni da shi muka zama wani iri tamfar bamu ne muka yi wancan zaman na lokacin dadin mu ba in ka ji ya kira ni to wani aiki zai sani ko kuma zai min fada kan wani laifi da aka ce mishi nayi rannan dai na gaji na ce mishi to wai ni wake baka labarin abubuwan da nake yi tunda kace bana yinsu akan idonka? Ya ce to masu fadan zasu yi miki karya ne? Nayi maza na ce mishi a’a ai sa masu gaskiya ne, ko zama a inda Yaya Almu yake bana yi saboda kallo daya zai yi min yaja wani mummunan tsaki ya ce dubi duk yanda ki ka maida kanki kin wani rame kin kanjame saboda bakin ciki ni ba ruwana tunda dai babu abin da nake yi miki ke ki ka tsangwami kanki in ce mishi haka ne in yi tafiyata.
Rannan ina dakina da daddare addu’a nake yi bayan na idar da sallah hakuri da dangana nake rokon a kara min, sai na jiwo salatin Lailatu cikin gurnanin kuka, da sauri na shafa fatihar na yiwo waje zan shiga dakin nata don naga kofar a bude sai kawai naji Yaya Almu yana rarrashinta wai ta bar shi yaje ya taso ni don bai kamata su tafi asibiti bai gaya min ba ina jin haka nayi sanaf-sanaf na koma dakina na hau gadona na kwanta tunda dai bata son in sani. Zuwa can ban san yanda aka yi ba sai gashi ya shigo dakina yana fadin ke Rabi tashi muje mu kai Lailatu asibiti ina ganin nakuda ce ta tashi mata kamar in ce mishi ba zani ba tunda bata da bukatar zuwan nawa sai kuma naga to don me zan yi hakan’? Na sanya hijabina na biyo bayanshi nasa hannu na kinkimi manyan akwatuna guda biyu da aka shake da kaya tanfar dai in anyi haihuwar can za’a zauna, shi kuma yaya Almu ya ciccibota ita da cikin nata zuwa cikin mota a haka muka isa asibiti, sai faman gurnani take yi ina ta nanata sannun da nake yi mata, amma ban samu ta amsa guda daya ba.
Gwajin farko da aka yi mata Nos din ta ce Hajiya da kin rike wannan nishin naki da kike faman yi sai bukatar nishin ya taso tukuna don in haihuwa tazo miki da sauri to sai kiyi ta nan da awa shida, na kalli agogo na ce zuwa takwas din safe kenan, yaya Almu ya bar mu a asibiti ya tafi gida kan cewar zai je yayi sallah ya yi wanka ya dawo na ce mishi to, ina nan a wurin sai ga mutanen gidansu sun iso in ban da na gaishe su da babu wanda ya ce min in ci kaina, muka zauna a haka suna sha’aninsu nima ina lazimina sai in sun jiwo mun hada ido su kwashe mun da dariya ina kallonsu.
Wajen karfe bakwai yaya Almu ya dawo, na ce mishi to bari nima inje gida in dawo ya ce, a’a bana so ta haihu ba kya nan a wurin nan na ce mishi to na hakura, haihuwa bata zo ba sai wajen karfe daya da kwata muna wurin a tsaye, Nos ta fito tana tambayar ina wadanda suka kawo Lailatu Mustapha muka yi maza muka mike ni dashi muka ce gamu suka ce to ta haihu an samu ya mace ni da Yaya muka kama murna yayin da fuskokin yan uwan Lailatu suka sauya alamar daa ba haka suka so ba.
Muna shiga dakin na nufi Lailatu na rungume ta don murna turus din da ta yi mun ya dawo dan Cikin haiyacina na juya wurin yaya Almu dake rungume da yarinyar cikin matsanancin farın ciki yana ganin na kalle shi ya miko min ita, ungo ta.
Rabi ‘yarki ce ki rike ta taki ce ki rike ta da zuciya daya kiyi mata reno da gata irin wanda Umma tayi min ki kuma yarda da cewar haka kaddara ta shiryo mana don kuwa kin san in da ina da iko akan al’amura to da ba haka ba, da na baki haihuwa kinyi ta-Rabi, kin yi ta har sai ta ishe ki kafin in baiwa sauran mutan da suke nema to bani da ikon komai don haka kiyi hakuri, na ce mishi babu komai Yayaa Ubangiji ya raya mana ita da imani yace mun amin.
Juyawan da zamu yi sai kawai muka ga Lailatu tana ta faman kuka da sauri Yaya Almu ya tambaye ta ko menene? Sai ta ce mishi wai tun bata wastsake daga azabar nakudar da ta sha ba har yayi mata kyauta da yarta kuma a gabanta yana cewa dashi ke ba da haihuwa to da ba ita zai baiwa ba ni zai baiwa t ai abin na Allah ne in ma shi ba ya sonta Ubangijin da ya yi ta yana sonta ni da Yaya muka yi ta rarrashi muna yi mata bayani don fahimta r da ita abin da ake nufi.
Bayan fitar Yaya Almu ‘yan uwan Lailatu suka shigo suka karbi yarinya ina jinsu suna cewa wannan yarinya irin kamar da ta yi da Ubanta ina jin da namiji aka yi niyyar yi, surkullen da aka yi tayi ne yasa tazo a mace, surkullen da aka yi kuwa cikin da ya fiddo mace ai shine watarana zai fiddo namiji, naje yi dai ko in ce a juri zuwa rafi da tulu gaba daya suka kwashe da dariya.
Ni kam jin su kawai nake yi ina kuma sabgogina tanfar dai ban san dani suke yi ba.
Tunda ‘yan uwan Lailatu suka wastsake daga kaduwar ya macen da aka samu maimakon namijin da ake sa ran gani sai kuma suka koma hirar da suka saba na fadin darajar mace mai
haihuwa yanda nan da nan take zama ta gaje gida
ta zama ita ce uwar iyali ita da miji kuma sun
zama daya sun zama ita yashi shi ya ita ta zama
shi da dukiyarshi duka nata yanzu fa daga wannan
haihuwar da Lailatu tayi komai na Lamido na
tane, dayar ta ce na tane mana tunda ko mutuwa
yayi ‘yarta ce mai gadonshi, gabana ya yanke ya
fadi saboda jin ana anbatowa Yaya Almu mutuwa
don kawai an haifi ‘ya guda daya tare dashi.
A wannan lokacin na samu kaina cikin
tsananin son Ummana da jin tausayinta saboda naa
kara fahimtar ba karamin hakuri tayi ba a zaman
da tayi gidan Baba ni dama nake zaune da Yaya
Almu cikin gatan da babu wanda ya isa ya fito fili
ya nuna min wata kiyaiya ko wulakanci saboda
1don Umma ya tsare al’amura masu yawan gaske
kenan nake ganin haka akan rashin haihuwata to
ita fa yaya taji da nata a lokacin da babu mai tsare
mata? Ni kam a yau na sami ko Umma karama
dake ta faman kai-kawo cikin al’amarin a boye
42
take yi sai dai ta cinma ayi amma bata fito fili ita
da kanta tayi ba shi yasa ma ban taba buda baki
na gayawa ita Umman ko baba irin zirga-zirgan
da take yi a wurin Lailatu ba.
Hakika na yarda na sakankance cewar matar
dake da mas’alar rashin haihuwa suna ganin abin
da suke gani na bakin ciki da kunan rai,
musamman idan suka yi dace da irin mutanen nan
da aiki da hadisin Manzon Rahama mai cewa
Imanin dayanku ba zai cika ba har sai yaso wa
dan uwanshi abin da yake so wa kanshi.’ bai dame
su ba.
A wapnan lokacin ji nake yi tamfar ba don
kaina nake son haihuwar ba ba kuma don Yaya
Almu ba tunda shi kam ai ya riga ya samu son
haihuwa nake yi don Umma na ta dai sa hannu ta
dauki dan da na haifa dan da na san shi kadai ne
zai zo duniya ya debe mata kishirwar haihuwa da
bakin cikin rashinta da ta rayu a ciki, sannan ni
ban damu ba ace mace ko namiji na samu in dai
mutum ne mai amsa sunan bil’adam ai bani da
zabi sai ko godiya, in na tuna halin da nake ciki
da yanda Umma ta rasa kuzari da lafiya tun daga
auren Yaya Almu zuwa yau duk da dai ta hadiye
komai a cikinta babu mai sanin tana da wata
damuwa.
43
Muna dawowa gida nay1 shiri na dauki yarinya
na lullube ta na hau Jirgi na nufi Legos da ita na
kaiwa Baba ya ganta, tana hannun Baba bayan ya
gama yi mata addu’a yana kallona cikin tsananin
farin ciki ya ce a’a uwata kun samu ya a gidanku,
na yi murmushi na ce mishi wannan tawa ce Baba
ni kadai in ta sake haifo wasu to suma sai su
samu, Baba yayi dariya ya ce kiny1 gaskiya uwata.
Kwana uku ca dawowarmu Baba ya aiko min
da wata motar sabuwa dal wai tukuicin kai mishi
yarinya da nayi, Lailatu da ‘yan uwanta kuwa abin
yayi matukar kona musu rai har suna fadin wai ai
wannan shi ne wani da tusa wani da karbe riga,
wannan in dai ba Jirgun sama Zai sai wa maijegon
ba ai baa kulla gaskiya ba.
Kwana hudu da haihuwar Ummana tazo ganin
yarinya kai tsaye dakin Lailatu ta fara shiga ta
dubata suka kuma gaisa da yan uwanta sannan
tasa hannu ta dauki yarinya ta fito da ita ta shiga
falon yaya Almu na same su a ciki tana kokarin
hudawa yarinyar kunne wanda in ban da Yaya
Almu yayi kashedin kar a huda da tuni iyayen
Lailatu sunyi hakan na ce Umma shi ne sai yau ki
ka zo buda mata kunnen bayan tasha iska ta gane
zafin jikinta, Umma tayi dariya ta ce ita dai
raguwa ce kawai mika ta a bata nono na ce to na
44
karbe ta na kai musu na dawo na zauna muka
gaisa sai ta miko min wani dan akwatin da ta
fiddo daga cikin Jakarta nasa hannu biyu na karba
ina kallonta sai ta ce min kayan kwalliyar yarki
ne a ciki na ce to Umma ai kuwa dai mun gode.
Anyi shagalin suna irin wanda ba zai yiwu a
tsaya bada labari ba, abu guda daya da zan fadi
dai shine, ‘yan uwa na birni da na kauye abokai na
cikin kasa da waje sun halarci sunan, gaba daya
cewa ake yi Lamido ya samu haihuwa, don haka
ya zama dole a zo mishi suna Rabi’atu sunan da
yaya ya sanya mata kenan, kyaututtuka kuwa inin
wadanda Lailatu ta samu abin sai wanda ya ganı,
amma bata gamsu ba saboda gaba daya kayan da
ya fito daga gidanmu raba daidai akayi mana
banbancin kawai shine kayan yara haka nan
abokan yaya Almu suma kyautar raba daidai suka
yi mana wannan dalili sai yasa ta kawar da kai
daga kan abin da ta samu ta zubawa nawa ido tà
mance cewar ita ce ta haifi ‘yar, ta mance da
cewar ni zan iya bayar da komai nawa don in
samu ‘yar kawai kar a hada mun ita da komai.
Bayan yan suna sun watse muka dunguma
cikin wai sabon zaman kuma zaman da nake
matukar son ganin nayi mu’amalla mai kyau da
yarinyar da muka samu yayin da ita kuma uwar
45
yar take iyakacin kokarinta wajen ganin ta shiga
tsakanina da ita, nayi matukar kokarina wajen
ganin al’amura sun daidaitu tsakanina da Lailatu
musamman ma da yake ita ce wacce zata zama
uwar ‘ya’yan yaya Almu to me zai sa muyi ta
fitina da ita? Na so ace Lailatu ta yarda mun
zauna lafiya tayi ta haihuwar ‘ya’yanta ni kuma ina
renonsu to taki duk wani tayi na zaman lafiya da
na kawo bata karba ba ta kabar dashi maimakon
ta fahimci dalilin sassaucin da nake yi ta dan
karyo don mu zauna lafiya, amma ina? Sai ta
maida abin tsoro a bisa wannan dalili sai ya zama
mun dole in kare kaina daga mummunan
wulakancin da take fito min dashi babu abin da
Lailatu ke yi min da yake matukar kona min rai
irin sau goma in zan sa hannu in dauki Rabi’atu to
sau goma kuma zata biyo ni tazo ta kwace ta ta
tafi tana cewa zo muje kar a lashe miki kurwa
kamar yanda aka lashewa ubanki.
Rannan tayi hakan akan idon Yaya Almu ya ce
haba Lailatu me yasa kike yin irin wanan abin ne
Ta ce a’a a’a ta haifi nata, yi kokari ta haifi nata
kawai amma kar asa min ido akan nawa bana son
1ya yi da neman wurin shiga irin nasu na gado.
A fusace yasa hannu ya karbe yarinyar ya
miko nmin ita ni kuwa sai nasa hannu na karbe ta
46
na rungume ina rarrashi saboda kukan da take yi a
dalilin tsorata da tayi ita kuwa Lailatu sai cewa
tayi tir da halin rashin zuciya irin taku ke kam ina
jin sanda ake rabon zuciya ba kwanan a wurin ta
juya ta nufi dakinta tana ganin Yaya Almu ya
shiga wurinshi tayi maz ata fito tazo ta sure
yarinyar ta shige daki ta kullo kofa ta barta tana ta
ihu.
A wannan lokacin dan Rankanin abu ne zai
tashi Lailatu tayi mun gorin haihuwa ta ce mun n
da da sai dai inga shirwa ta dauko dan tsako, ko
kuma ta ce haihuwa ai ba abar banza ba ce
gadonta ake yi in na zauna zanyi kukan bakin ciki
sai Baba Talatu ta rufe ni da fada ta ce kukan
butulci nake so in yi in ba haka ba menene ba ayi
min ba na ni’imomin rayuwa? In ban da halinki na
rashin zuciya me zai sa ba za ki fita hanyar yarta
ba ba akanta take wulakanta ki ba? Na ce ba ‘yarta
ba ce Baba ‘yar Yaya Almu ce don haka tawa ce,
taja tsaki ta ce ai sai kiyi.