Skip to content
Part 42 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Da gari ya waye shiryawa nayi na tafi gida nufina in je wurin Ummana in dan yi hira ko zan ji dadin zuciyata, ina zaune a gabanta cikin kwalliya sosai don dai taga kamar bani da wata damuwa, muna zaune muna hirarmu idanuwan Umma akaina suke ta zuba min su ko kiftawa bata yi ni kuma ina ta kokarin yawaita murmushi da fara’a a fuskata don dai ta dan ji dadi zuwa can sai naji ta ce min a dan tsakanin nan bana iya bacci Adawiyyah saboda nasan kina cikin wani hali, sannan a yanzu ramar da na gani a tare dake tafi komai tada hankali sai dai kuma hakan ba zai hana ni cewa ki kara hakuri akan wanda nasan kina yi ba, duk wanda ki ka ganshi ya yi hakuri bai ci nasara ba Adawiyya to bai yi hakurin mai yawa ba ne, na ce mata to Umma.

Ina zaune a gida bani da wani aiki sai na abincin gida da kuma sallolina dana sanya a gabana, saboda shi kanshi Yaya Almu in aka tambaye shi yaushe ne girkina? Ba zai iya fada ba, kullum dai nice a kicin nice mai abinci yayın da shi kuma yake wuni a dakin Lailatu, ya kuma raba dare yana tare da ita in kuma ya dan saci jiki ya shigo wurina to naan da nan mutanenta zasu tashi su yi ta furje-furje suna fadin maganganu na aibanta ni tare da Umma da fadin wai irin asire-asiren da muke yi mata suna zuwa suna tonewa kuma wai duk akan cikin da take dashi ne muke son barar mata, ni kam a yanzu ko mutanen nata sun tashi bana zuwa tunda na riga na san shakiyanci ne sai in bar shi shi kadai yayi ta Zirga-zirganshi.

Ni da shi muka zama wani iri tamfar bamu ne muka yi wancan zaman na lokacin dadin mu ba in ka ji ya kira ni to wani aiki zai sani ko kuma zai min fada kan wani laifi da aka ce mishi nayi rannan dai na gaji na ce mishi to wai ni wake baka labarin abubuwan da nake yi tunda kace bana yinsu akan idonka? Ya ce to masu fadan zasu yi miki karya ne? Nayi maza na ce mishi a’a ai sa masu gaskiya ne, ko zama a inda Yaya Almu yake bana yi saboda kallo daya zai yi min yaja wani mummunan tsaki ya ce dubi duk yanda ki ka maida kanki kin wani rame kin kanjame saboda bakin ciki ni ba ruwana tunda dai babu abin da nake yi miki ke ki ka tsangwami kanki in ce mishi haka ne in yi tafiyata.

Rannan ina dakina da daddare addu’a nake yi bayan na idar da sallah hakuri da dangana nake rokon a kara min, sai na jiwo salatin Lailatu cikin gurnanin kuka, da sauri na shafa fatihar na yiwo waje zan shiga dakin nata don naga kofar a bude sai kawai naji Yaya Almu yana rarrashinta wai ta bar shi yaje ya taso ni don bai kamata su tafi asibiti bai gaya min ba ina jin haka nayi sanaf-sanaf na koma dakina na hau gadona na kwanta tunda dai bata son in sani. Zuwa can ban san yanda aka yi ba sai gashi ya shigo dakina yana fadin ke Rabi tashi muje mu kai Lailatu asibiti ina ganin nakuda ce ta tashi mata kamar in ce mishi ba zani ba tunda bata da bukatar zuwan nawa sai kuma naga to don me zan yi hakan’? Na sanya hijabina na biyo bayanshi nasa hannu na kinkimi manyan akwatuna guda biyu da aka shake da kaya tanfar dai in anyi haihuwar can za’a zauna, shi kuma yaya Almu ya ciccibota ita da cikin nata zuwa cikin mota a haka muka isa asibiti, sai faman gurnani take yi ina ta nanata sannun da nake yi mata, amma ban samu ta amsa guda daya ba.

Gwajin farko da aka yi mata Nos din ta ce Hajiya da kin rike wannan nishin naki da kike faman yi sai bukatar nishin ya taso tukuna don in haihuwa tazo miki da sauri to sai kiyi ta nan da awa shida, na kalli agogo na ce zuwa takwas din safe kenan, yaya Almu ya bar mu a asibiti ya tafi gida kan cewar zai je yayi sallah ya yi wanka ya dawo na ce mishi to, ina nan a wurin sai ga mutanen gidansu sun iso in ban da na gaishe su da babu wanda ya ce min in ci kaina, muka zauna a haka suna sha’aninsu nima ina lazimina sai in sun jiwo mun hada ido su kwashe mun da dariya ina kallonsu.

Wajen karfe bakwai yaya Almu ya dawo, na ce mishi to bari nima inje gida in dawo ya ce, a’a bana so ta haihu ba kya nan a wurin nan na ce mishi to na hakura, haihuwa bata zo ba sai wajen karfe daya da kwata muna wurin a tsaye, Nos ta fito tana tambayar ina wadanda suka kawo Lailatu Mustapha muka yi maza muka mike ni dashi muka ce gamu suka ce to ta haihu an samu ya mace ni da Yaya muka kama murna yayin da fuskokin yan uwan Lailatu suka sauya alamar daa ba haka suka so ba.

Muna shiga dakin na nufi Lailatu na rungume ta don murna turus din da ta yi mun ya dawo dan Cikin haiyacina na juya wurin yaya Almu dake rungume da yarinyar cikin matsanancin farın ciki yana ganin na kalle shi ya miko min ita, ungo ta.

Rabi ‘yarki ce ki rike ta taki ce ki rike ta da zuciya daya kiyi mata reno da gata irin wanda Umma tayi min ki kuma yarda da cewar haka kaddara ta shiryo mana don kuwa kin san in da ina da iko akan al’amura to da ba haka ba, da na baki haihuwa kinyi ta-Rabi, kin yi ta har sai ta ishe ki kafin in baiwa sauran mutan da suke nema to bani da ikon komai don haka kiyi hakuri, na ce mishi babu komai Yayaa Ubangiji ya raya mana ita da imani yace mun amin.

Juyawan da zamu yi sai kawai muka ga Lailatu tana ta faman kuka da sauri Yaya Almu ya tambaye ta ko menene? Sai ta ce mishi wai tun bata wastsake daga azabar nakudar da ta sha ba har yayi mata kyauta da yarta kuma a gabanta yana cewa dashi ke ba da haihuwa to da ba ita zai baiwa ba ni zai baiwa t ai abin na Allah ne in ma shi ba ya sonta Ubangijin da ya yi ta yana sonta ni da Yaya muka yi ta rarrashi muna yi mata bayani don fahimta r da ita abin da ake nufi.

Bayan fitar Yaya Almu ‘yan uwan Lailatu suka shigo suka karbi yarinya ina jinsu suna cewa wannan yarinya irin kamar da ta yi da Ubanta ina jin da namiji aka yi niyyar yi, surkullen da aka yi tayi ne yasa tazo a mace, surkullen da aka yi kuwa cikin da ya fiddo mace ai shine watarana zai fiddo namiji, naje yi dai ko in ce a juri zuwa rafi da tulu gaba daya suka kwashe da dariya.

Ni kam jin su kawai nake yi ina kuma sabgogina tanfar dai ban san dani suke yi ba.

Tunda ‘yan uwan Lailatu suka wastsake daga kaduwar ya macen da aka samu maimakon namijin da ake sa ran gani sai kuma suka koma hirar da suka saba na fadin darajar mace mai haihuwa yanda nan da nan take zama ta gaje gida ta zama ita ce uwar iyali ita da miji kuma sun zama daya sun zama shi ya zama ita,  ita ta zama shi da dukiyarshi duka nata yanzu fa daga wannan haihuwar da Lailatu tayi komai na Lamido na tane, dayar ta ce na tane mana tunda ko mutuwa yayi ‘yarta ce mai gadonshi, gabana ya yanke ya fadi saboda jin ana anbatowa Yaya Almu mutuwa don kawai an haifi ‘ya guda daya tare dashi.

A wannan lokacin na samu kaina cikin tsananin son Ummana da jin tausayinta saboda na kara fahimtar ba karamin hakuri tayi ba a zaman da tayi gidan Baba ni dama nake zaune da Yaya Almu cikin gatan da babu wanda ya isa ya fito fili ya nuna min wata kiyaiya ko wulakanci saboda idon Umma ya tsare al’amura masu yawan gaske kenan nake ganin haka akan rashin haihuwata to ita fa yaya taji da nata a lokacin da babu mai tsare mata? Ni kam a yau na sami ko Umma karama dake ta faman kai-kawo cikin al’amarin a boye take yi sai dai ta cinma ayi amma bata fito fili ita da kanta tayi ba shi yasa ma ban taba buda baki na gayawa ita Umman ko baba irin zirga-zirgan da take yi a wurin Lailatu ba.

Hakika na yarda na sakankance cewar matar dake da mas’alar rashin haihuwa suna ganin abin da suke gani na bakin ciki da kunan rai, musamman idan suka yi dace da irin mutanen nan da aiki da hadisin Manzon Rahama mai cewa Imanin dayanku ba zai cika ba har sai yaso wa dan uwanshi abin da yake so wa kanshi.’ bai dame su ba.

A wannan lokacin ji nake yi tamfar ba don kaina nake son haihuwar ba ba kuma don Yaya Almu ba tunda shi kam ai ya riga ya samu son haihuwa nake yi don Umma na ta dai sa hannu ta dauki dan da na haifa dan da na san shi kadai ne zai zo duniya ya debe mata kishirwar haihuwa da bakin cikin rashinta da ta rayu a ciki, sannan ni ban damu ba ace mace ko namiji na samu in dai mutum ne mai amsa sunan bil’adam ai bani da zabi sai ko godiya, in na tuna halin da nake ciki da yanda Umma ta rasa kuzari da lafiya tun daga auren Yaya Almu zuwa yau duk da dai ta hadiye komai a cikinta babu mai sanin tana da wata damuwa.

Muna dawowa gida nayi shiri na dauki yarinya na lullube ta na hau Jirgi na nufi Legos da ita na kaiwa Baba ya ganta, tana hannun Baba bayan ya gama yi mata addu’a yana kallona cikin tsananin farin ciki ya ce a’a uwata kun samu ya a gidanku, na yi murmushi na ce mishi wannan tawa ce Baba ni kadai in ta sake haifo wasu to suma sai su samu, Baba yayi dariya ya ce kinyi gaskiya uwata.

Kwana uku ca dawowarmu Baba ya aiko min da wata motar sabuwa dal wai tukuicin kai mishi yarinya da nayi, Lailatu da ‘yan uwanta kuwa abin yayi matukar kona musu rai har suna fadin wai ai wannan shi ne wani da tusa wani da karbe riga, wannan in dai ba Jirgun sama Zai sai wa maijegon ba ai baa kulla gaskiya ba.

Kwana hudu da haihuwar Ummana tazo ganin yarinya kai tsaye dakin Lailatu ta fara shiga ta dubata suka kuma gaisa da yan uwanta sannan tasa hannu ta dauki yarinya ta fito da ita ta shiga falon yaya Almu na same su a ciki tana kokarin hudawa yarinyar kunne wanda in ban da Yaya Almu yayi kashedin kar a huda da tuni iyayen Lailatu sunyi hakan na ce Umma shi ne sai yau ki ka zo buda mata kunnen bayan tasha iska ta gane zafin jikinta, Umma tayi dariya ta ce ita dai raguwa ce kawai mika ta a bata nono na ce to na karbe ta na kai musu na dawo na zauna muka gaisa sai ta miko min wani dan akwatin da ta fiddo daga cikin Jakarta nasa hannu biyu na karba ina kallonta sai ta ce min kayan kwalliyar yarki ne a ciki na ce to Umma ai kuwa dai mun gode.

Anyi shagalin suna irin wanda ba zai yiwu a tsaya bada labari ba, abu guda daya da zan fadi dai shine, ‘yan uwa na birni da na kauye abokai na cikin kasa da waje sun halarci sunan, gaba daya cewa ake yi Lamido ya samu haihuwa, don haka ya zama dole a zo mishi suna Rabi’atu sunan da yaya ya sanya mata kenan, kyaututtuka kuwa irin wadanda Lailatu ta samu abin sai wanda ya ganı, amma bata gamsu ba saboda gaba daya kayan da ya fito daga gidanmu raba daidai akayi mana banbancin kawai shine kayan yara haka nan abokan yaya Almu suma kyautar raba daidai suka yi mana wannan dalili sai yasa ta kawar da kai daga kan abin da ta samu ta zubawa nawa ido tà mance cewar ita ce ta haifi ‘yar, ta mance da cewar ni zan iya bayar da komai nawa don in samu ‘yar kawai kar a hada mun ita da komai.

Bayan yan suna sun watse muka dunguma cikin wai sabon zaman kuma zaman da nake matukar son ganin nayi mu’amalla mai kyau da yarinyar da muka samu yayin da ita kuma uwar yar take iyakacin kokarinta wajen ganin ta shiga tsakanina da ita, nayi matukar kokarina wajen ganin al’amura sun daidaitu tsakanina da Lailatu musamman ma da yake ita ce wacce zata zama uwar ‘ya’yan yaya Almu to me zai sa muyi ta fitina da ita? Na so ace Lailatu ta yarda mun zauna lafiya tayi ta haihuwar ‘ya’yanta ni kuma ina renonsu to taki duk wani tayi na zaman lafiya da na kawo bata karba ba ta kabar dashi maimakon ta fahimci dalilin sassaucin da nake yi ta dan karyo don mu zauna lafiya, amma ina? Sai ta maida abin tsoro a bisa wannan dalili sai ya zama mun dole in kare kaina daga mummunan wulakancin da take fito min dashi babu abin da Lailatu ke yi min da yake matukar kona min rai irin sau goma in zan sa hannu in dauki Rabi’atu to sau goma kuma zata biyo ni tazo ta kwace ta ta tafi tana cewa zo muje kar a lashe miki kurwa kamar yanda aka lashewa ubanki.

Rannan tayi hakan akan idon Yaya Almu ya ce haba Lailatu me yasa kike yin irin wanan abin ne Ta ce a’a a’a ta haifi nata, yi kokari ta haifi nata kawai amma kar asa min ido akan nawa bana son iya yi da neman wurin shiga irin nasu na gado.

A fusace yasa hannu ya karbe yarinyar ya miko nmin ita ni kuwa sai nasa hannu na karbe ta na rungume ina rarrashi saboda kukan da take yi a dalilin tsorata da tayi ita kuwa Lailatu sai cewa tayi tir da halin rashin zuciya irin taku ke kam ina jin sanda ake rabon zuciya ba kwanan a wurin. Ta juya ta nufi dakinta tana ganin Yaya Almu ya shiga wurinshi tayi maza ta fito tazo ta sure yarinyar ta shige daki ta kullo kofa ta barta tana ta ihu.

A wannan lokacin dan kankanin abu ne zai tashi Lailatu tayi mun gorin haihuwa ta ce mun da sai dai inga shirwa ta dauko dan tsako, ko kuma ta ce haihuwa ai ba abar banza ba ce gadonta ake yi in na zauna zanyi kukan bakin ciki sai Baba Talatu ta rufe ni da fada ta ce kukan butulci nake so in yi in ba haka ba menene ba ayi min ba na ni’imomin rayuwa? In ban da halinki na rashin zuciya me zai sa ba za ki fita hanyar yarta ba ba akanta take wulakanta ki ba? Na ce ba ‘yarta ba ce Baba ‘yar Yaya Almu ce don haka tawa ce, ta ja tsaki ta ce ai sai kiyi.

<< Wace Ce Ni? 41Wace Ce Ni? 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×