Skip to content
Part 44 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Sati guda cif da dawowana sai ga Umma Amarya tazo da sassafe ina zaune a kasa a gabanta bayan na gama shirya mata abin karyawa shima yaya Almu yazo ya gaishe ta ya kuma ki fita don ya san Baba ne ya turo ta, sai ta ce min Alhaji ne ya turo ni in zo kiyi min bayani kan abinda ke faruwa, bayani na dalla-dalla na yiwa Umma tun daga farkon zuwan Lailatu gidan har kawo ranar da na bar gidan ban rage komai ba tun daga girkin wata takwas da ya sani nayi babu sannu babu madalla har kawo marina da tayi a gabanshi da hukuncin da yayi na sanya Lailatu ta rama dukan da nayi mata kawo kan cewar da ya yi na yi asirin da na raba shi da ita don kar ta sake haihuwa, babu abin da ban gaya mata ba har da maganganunshi na cewar bakin ciki zai kashe ni.

Shiru tayi tamfar wacce ruwa ya cinyeta bata ce komai ba sai shi Yaya Almu ne da yaga shirun yayi yawa ya ce amma Umma tayı maza katse shi ta ce ba wurinka ya aiko ni ba ka bari sai ya ce yana so ya ji naka bayanin sai kayi wa wanda ya aiko maka tana fadin hakan kuma sai ta mike tayi tafiyarta.

Da yamma na isa legos saboda Baba ya kira mu gidan a cike yake su yaya Zubairu su Yaya Kabiru dukan su suna nan sun zo gaba dayansu kowa fada yake yi min kan abin da nayi.

A falon Baba kowa yana nan har da Ummana da Umma karama da Umma Amarya gasu yaya Zubairu duk an hallara, Baba ya ce kai Kabiru na kira ku ne anan dukanku don ku zo ku shaida abin da ke faruwa ko ya faru tsakanin Lamido da uwata cikin ku dukanku babu wanda ban yiwa shari’a tsakaninshi da iyalinshi ba, hakan bai damen ba saboda zo mu zauna zo mu saba, amma bayanin da Maryam tazo min dashi dazu ya bambanta da naku don haka na ce kuzo ku taya ni ji ke uwata kiji tsoron yin karya don ba za ta amfana miki komai ba, ki fadi gaskiya na ce mishi to, yadda na rattabawa Umma Amarya komai haka nan nayi bayani sai ma da na ga Umma karama a zaune na shaidawa Baba cewar duk sati biyu take zuwa gidan tunda Lailatu tazo bata kuma taba shiga dakina ta zauna ba wani lokaci ma fitanta kawai nake gani nan da nan jikin Umma ya dauki rawa ta kama kame-kame tana fadin wai ai ita Rabi’atu take zuwa gani, Baba bai kula ta ba wurin Yaya Almu ya juya ya tambaye shi anyi wadannan abubuwa ko ba ayi su ba? Yaya Almu ya sunkuyar da kai ya ce anyi su Baba, amma akwai dalilai, Baba ya yi maza ya ce to ko zaka gaya min dalilin daka saka uwata tayi wata takwas tana girki ita ka dai bayan ga abokiyar zamanta?

Ya soma kame-kamen bayani ya sake tambayarshi da ta mare ta a gabanka ka hana ta ramawa wane hukunci ka yi mata? Baba ya sake juyowa wurina ya ce min ke uwata don me ba ki taba gayawa Zuwairah abubuwan dake faruwa ba? Na sunkuyar da kaina na ce mishi naje zan gaya mata ta ce min kar in koyi kai karar mijina in zama matar rufin asiri, Baba ya yi shiru dakin ma ya yi shiru, zuwa can sai ya ce daga yau na Sanya Maryam da Junaidu su zama wakilai akan al’amarinki duk abin da ya dame ki ki gaya musu, na ce mishi to Baba.

Baba ya sake kallon su yaya Kabiru ya ce musu a yau na taraku ne anan don in shaida muku cewar randa duk aka wayi gari bana duniya to dukanku na bar wa amanar uwata ba wani mutum daya ba saboda ni da Baba ya yi gamsuwar da ya bar min amanaar Zuwaira ni kadai bayanshi rayuwa tasa na barta ta wahala balle Lamido da ya iya wahalar da uwata akan idona da na uwarshi, lokaci mai tsawo Baba ya dauka yana yin magana kafin ya ce, ke uwata laifin da kika yi na zartar wa kanki da hukunci da kike yi shi ne yasa ba zan yi komai kan duk wani abin da akayi miki ba, ina kuma so in kara jaddada miki cewar ko bayan raina ban yarda kisa kafa ki fita daga gidan Lamido ba don haka ki koma dakinki ki zauna na ce mishi to, ke kuma karama ba zan ce miki komai ba kije kiyi duk abin da kika ga yayi miki daidai.

Mun fito zamu tafi yaya Junaidu ya kira ni nayi maza naje wurinshi sai ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min kar ki rudu da abin da Baba ya yiwa Mustapha a cikin mutane ki dauki hakan tamfar wata dama a wurinki da za ki rinka yi, mishi abin da ki ka ga dama ina fatan dai kina sane da cewar hakkukuwanshi da suke kanki basu sauya ba, sannan duk da bayanan da ki ka yi nina yarda da cewar babu wani abin da Mustapha zai yi da nufin ya cuce ki don haka kiyi hankali da kanki ya wuce ya tafi ya bar ni a tsaye cikin tunani.

Kalaman Yaya Junaidu sun kashe min jiki sai dai kuma inda mas’alar take shine a yanzu ba na son ganin Yaya Almu a kusa dani ko maganarshi naji sai in rinka jin gabana yana faduwa, babu lokacin da na kan samu natsuwa irin lokacin da na san ba ya gari bisa wannan dalili sai nafi sha’awar da a bar ni in koma wurina in yi zamana ni kadai in yaso su bar auren ace yana nan bai mutu ba don kuwa ni kaina ban taba sha’awar mutuwar auren namu ba don bana yiwa kaina sha’awar zawara.

A wannan dawowar da muka yi babu abin da bai yi ba don mu daidiata mu zauna lafiya naki yarda bana shiga komai na hidimar gidan sabuwar ‘yar aikin da suka kawo ba na sa ta ba na hana ta tsakanina da ita ina kwana ne kawai ina gajiya?

Kayan da nayi amfani da su nawa nan take nake gyara su in adana na ma daina shiga kicin din da yake na hadakan a wanda yake cikin falona nake aiki na ba na kuma yin girkin tare da kowa, ina zaune cikin falona, Ice-Cream din da nayi nake sha, yaya Almu ya shigo ya zauna yana yi mun magana, Rabi’atu ta rarrafo ta shigo cikin falon tazo ta dafa jikina ta mike ta tsaya tana kallona da sauraron inyi mata wasannin da muka saba, don kawai in bata mishi rai na kwalawa Baba Talatu kira ta shigo na ce mata dauke min wannan yarinyar ki bai wa wancan matar ita ta mika ta dakinsu, Baba Talatu tayi maz ata fice daga dakin tayi tafiyarta ba tare da tayi abin da na ce din ba, shima yayan ficewa yayi ya bar min dakin saboda yazo iya wuya da abin da nayin, sai bayan fitarshi ne nasa hannu na sureta muka shige can ciki, ko zuwa wurina yayi ranar girkina zai min wata magana sai in gaya mishi in raba ka da mai haihuwa zai mun wata magana sai in gaya mishi in raba ka da mai haihuwa don ka zauna tare dani da bana haihuwa to ai kai kuma sai kawai ka fita hanyata me zaka yi dani? Duk wani abin da na rinka yi mishi a wannan lokacin shanyewa ya rinka yi tanfar dai ba shi ne yaya Almun da na sani ba, illa iyaka dai gaba daya shima ya kame kanshi ya fita harkata.

Ina kwance a dakina ranar Talata da safe bayan na gama wanke kurarrajin bakina da garin ararrabi da aka bani shawarar anfani dashi, ji nake tanfar in kurma ihu saboda tsananin zugin da bakina ke yi, Baba Talatu ta shigo ta same ni, yaya dai uwardakina? Na kalle ta cikin nutsuwa na ce mata bakina ya dame ni Baba ga kada gwarzo yau ma ya sake fito min ko ruwa ba na iya sha, ta kalle ni cikin kulawa da tausayawa sannu uwardakina ai kece kina fama da ciwo amma kin ki yarda ki gayawa maigidan an taba yin haka ace kana zaman mutum amma ba za ka gaya mishi damuwarka ba.

Ina kwance anan wurin ina fama da kaina saboda matsanancin zazzabin da ya kama ni ina cikin tunanin abin yi sai ga Yaya Almu ya shigo cikin kwalliya sosai nan da nan kunshin turarenshi ya gauraye ko’ina ina shirin mu gama gaisawa in nemi izininshi don zuwa ganin Likita kan mas’alolin da suke damuna sai kawai naji ya ce min zan yi tafiya zuwa London da Lailatu zan akai ta ayi mata wankin ciki saboda yawan barin da take yi a dan tsakanin nan ina daga kwancen nace mishi to sai kun dawo, Allah ya kiyaye hanya, ya juya bayan ya ce amin, itama Lailatu ta shigo ta sha kwalliya ita da Rabi’atu sunyi matukar yin kyau suma kamshin suke yi mai dadi na mike muka y1 sallama nayi musu rakiya har zuwa jikin mota sai da suka tafi sannan na shigo gida, ina hawa kan gadona na soma kuka na fara gajiya da al’amuran yaya Almu, komai kankantar abin da yayi min a yanzu sai in ji kirjina yana ta ciwo in ji kamar zan sa hannu in dauko zuciyata saboda tsananin zafin da take yi min, Lailatu da ta haihu watanni takwas da suka wuce ita ce wai an tafi da ita London don yi mata wankin ciki saboda tana yawan yin baci alhalin ni tun zuwan Lailatu gidan ya hanani zuwa ko’ina, hatta bikin da aka yi a Katagun bai bar ni naje ba duk da a gidanmu ne sai kawai ya tasa Lailatu a gaba suka yi tafiyarsu ya ce wai ta riga ni tambayarshi zuwa bikin kuma zata kai musu Rabi’atu su ganta, na ce haka ne ni kuma bani da abin kaiwa a gani sai kun dawo.

Jikina yayi tsananin zafi saboda tsananin bacin rai ga kukan da nayi tayi don haka sai na kwana cikin matsanancin halin da sai da Baba Talatu ta taya ni kwana, gari na wayewa ta yiwa Baba waya ta shaida mishi halin da nake ciki, ba a dauki wani lokaci mai tsawo da yawa ba sai ga Yaya Junaidu ya iso yana ganin halin da nake ciki ya tasa ni a gaba sai Legos kai tsaye gida ya kai ni gaban Baba, ya zuba min ido yana kallôna wane irin lalacewa kika yi haka uwata? Gaba daya kin tsangwami kanki kin hana kanki sakat kin ki ki saki ranki kiyi kyan gani, maganganun da Baba ya Soma yi min yasa na kama kuka ina rokon shi ya barni in zauna a gida na gaji da zama da yaya Almu yana nema ya haddasa min ciwon zuciya, tsawon lokaci yana rarrashina kafin na hakura na daina kukan da nake yi.

Washegarin zuwana Legos Ummana ta iso saboda kiran da Baba ya yi mata a dakinta ta same ni a kwance nayi kuka har idanuwana sun kumbura, Umma ta zuba min ido tana kallona cikin natsuwa da tausayawa me ke damunki haka Adawiyyah? Na ce mata ban sani ba Umma illa iyaka dai kirjina yana min ciwo zuciyata ji nake yi tanfar in dauko ta saboda tsananin zafin da take yi min ga kada gwarzon dake damuna ta ce to tashi muje in kai ki asibiti ga Junaidu yazo zamu tafi tare nace mata to.

Ina zaunc gaban Likita ina amsa tambayoyin da Likita ke yi min, sai Umma ta ka rbe tambaya ta hanyar cewa tana da mas’ala ne Dakta, gwaje-gwajen da aka yi mata a baya sun nuna tana da mas’alar kankantar mahaifa da yawa wanda suka ce ba zai bari ta haihu ba, Likita ya sake kallona kafin ya ce to amma a sakamakon wannan gwajin ai ya nuna ciki ne da ita, ji na nayi tanfar ina yawo kan gajimare saboda rudewa, Umma kuwa cewa tayi a kira mata yaron da suka zo tare yana nan a waje, nan da nan yaya Junaidu ya shigo hankalinshi a tashe saboda yayi zaton wani abu ne mai tsanani ya faru. Zauna ka taya ni jin wata magana Junaidu, ya yi maz aya zauna yana kallonta cikin sanyin jiki ya tambaye ta me ya faru Umma? Umma ta kalli Likita ta ce mishi Dakta me ka ce yana damun Adawiyyah? Likita yayi murmushi ya ce shekara nawa ne da auren nata ne Hajiya? Har ki ke so ki debe tsammani ta ce mishi bakwai har da wasu watanni, yaya Junaidu ya gyara zama ya ce mishi menene Dakta? Likita ya kara kallon takardun da aka kawo gabanshi ya ce, wannan normal abu ne yake gare ta, yaya Junaidu yayi wani motsi mai karfi kafin ya ce yi mata scarning Dakta don mu kara tabbatarwa yayi maza ya ce to shi kenan.

Ina kwance kan gadon, Likita gaba daya hankalin Umma da yaya Junaidu har da nima yake kan allon computer da Likita ke dubawa, bayan ya shafa min wani ruwa mai dan sanyi yana kuma bin marata da dan wani mulmulallen abu yana goyawa nan da nan allon ya shiga baiyanar da abin da ake son gani gashi nan ai har ya zama mutum maganar Likita kenan yaya Junaidu ya ce tsarki ya tabbata ga Ubangiji, ya shiga yin tasbihi yayin da Umma ke ta faman kuka, ni kam a kwance nake zuciyata sai faman bugawa take yi ji nake tanfar a mafarki nake wai ciki ne dani abin da na riga na debe tsammani kowa ma ya hakura cikin zuciyata na ce Allah na gode maka, Ubangiji kasa abin da nake ganin na motsin mutum a cikin cikina ya tabbata gaskiya ne ba mafarki nake ba, ciki ne gashi watanni kusan biyar ba ya motsi ne mai karfi a dalilin karancin kuzarin da ke gare shi, bata cin abinci bata kula da kanta ta rasa abubuwa masu yawa, don haka shima ya rasa karfin kuzurin, jikin Umma yana rawa ta ce yanzu meye abin yi Dr.? Ya ce zamu dan sa mata drip don ya rage mata yunwa kafin mu dauki matakin da ya dace.

Ina kwance kan gadon Likita ana yi min Karin ruwa a sabon dakin da aka kaini bayan tafiyar yaya Junaidu gida har lokacin Umma dake zaune a gefe na bata iya cewa komai ba in ban da kukan da take yi tsawon lokaci muna nan a haka har bacci mai karti ya dauke ni, farkawa kawai nayi daga baccin na samu Baba a tsaye a kaina tare da Likitan da ya duba nin, 1tama Umma tana tsaye a gefenshi, kin tashi uwata? Na ce eh Baba na yunkura don in tashi in gaishe shi yayı maza ya maida ni da hannunshi koma ki kwanta ki huta ki samu natsuwa, in Allah ya yarda Allah zai kawo mana karshen damuwarmu, ban yi magana ba saboda sai na ji ina jin nauyin amsawa, ya sake kallon Likitan ya ce mishi tunda ta farka a sake yin scarning din nan da nan Likita ya bi umarnin da aka ba shi. Dr ya ce gashi nan yallabai, mutunne ka ganshi in kana son sanin mace ne ko namiji ma zamu iya dubawa, baba yayi maza ya ce a’a ba abin da nazo gani kenan ba mun gode Allah shine mafificin mai baiwa shine wanda ba a debe tsammani daga samun alherinshi, Umma ta yi ajiyar zuciya mai karfi ta ce haka ne, ya kara Juyawa wurinta ya ce iko sai Allah, wa yaga mun Zuwairah rike da dan da uwata ta haifar mata?

Umma tayi murmushi a karo na farko tun bayan kukan da tayi, ta yi ta ce a’a menene da ban sauran ya’yan da nayi ta dauka fa? Yayi murmushi ya ce uh’uh dai Zuwairah, yak sake maida hankali wurin Likita ya ce mishi sallame ta su koma gida za a kula da ita kai kuma in ka tashi sai ka biyo ka karbi goron albishirinka, ya ce to ya yi ta godiya tun kafin yasan me za’a ba shi.

<< Wace Ce Ni? 43Wace Ce Ni? 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×