Mun dawo gida Likitan da ya ganni a asibiti kuma shi ne wanda ya ci gaba da zuwa gida yana duba ni saboda irin alherin da Baba yayi mishi, magunguna ya rnka bayar wa tare da shawarwari kan irin abincin da ya dace in rinka ci saboda kurarrajin dake damuna, nan da nan na samu karfi a jikina saboda na fara rabuwa da yunwa da nayi kan kace meye wannan kuma sai ga cikina ya kama motsi akai-akai, ba zan iya kwatanta farin cikin Umma ba a wannan lokacin ba zan iya cewa ga halin da take ciki ba.
Duk da Umma karama tana gidan bata san me ke faruwa ba abin da ta sani dai kawai shine bani da lafiya, gashi kuma Umma tayi sa’a Baba ya ce kowa ya kama bakinshi yayi shiru ba ya so ayi ta yawo da maganar sai dai kashedin da Baban yayi bai hana Umman yin waya ta shaidawa Umma Amarya abin da ake ciki ba.
Sati biyu cif da tafiyar su Yaya Almu sai gasu sun dawo a gida suka sauka don isowar dare suka yi daga shi har Lailatu da Rabi’atun sun yi shar gwanin sha’awa da su kai ka ce ba asibiti suka je ba, daga hutun amarci suka dawo, sai dai ganina da yaya Almu ya yi a gida. yayi matukar bata mishi rai, kasa boye bacin ranshi yayi don kuwa ko tafiya masaukinsu da aka basu shi da Lailatunshi bai je ba, ya zauna gaban Umma yana tambayarta abin da yasa ake keta mishi haddin gidanshi.
Umma ta kalle shi cikin natsuwa ta ce mishi, to Babangida sai kayi hakuri nima kirana kawai Alhaji yayi ya ce min in zo in kai Adawiyyah asibiti bata da lafiya.
Cikin daren rannan muka hallara a gaban Baba saboda yaya Almu ya tubure ya ce bai yarda da gatan da ake yi min bá wanda yake bani damar wulakantashi, don me’ shi ba zan gaya mishi bani da lafiya ba sai bayan ya bar gida zan sa a fadaa a gida? In ba raini da wulakanci ba me zai sa in yi haka in ban da nasan ina da wadanda suka tsaya min? Yaya Junaidu shima ya shigo saboda kiran da aka yi mishi don yaya Almun ya ce yana da magana dashi.
A fusace ya kalle shi ya ce mishi kái kake daurewa Rabi gindi kan duk wani abin da take yi min, kana shiga cikin harkokin iyalina da yawa, a wurinka ta samu kudaden da ta sai gida har ta samu tashi ta bar dakinta ta koma can da taimakonka tayi hakan tayi min rashin kunyar da yasa na hanata zuwa biki katagun sai da ka nuna min rashin jin dadinka kan hakan ka ce ban yi mata adalci ba, na hanata zuwa cikin dangi yanzu kuma ka shiga gidana ba izini kaje ka fito da ita ba tare da ka nemi izinina ba kuma baka samu lokacin da kayi waya ka gaya min abin da ake ciki ba to ya ishe ni haka nasan duk kokarinka bai wuce wai kai ka nuna min kai kawunta ba ne, kan ya karasa maganar da zai fada yaya Junaidu ya katse maganar tashi ta hanyar ce mishi gyara maganar da kayi ta ce min wai kawu fusatar yaya Almu tayi yawa tanfar dai ya mance a gaban Baba suke sai ya sake ce mishi an ce maka wai kawu, ni ina yi maka abin da kake yi min ne ko kai ba ka da mas’ala ne a gidanka? Yaya Junaidu ya ce mishi ina da ita, ya daga ido ya kalli Baba cikin natsuwa da girmamawa ya ce mishi Baba Mustapha ya yi min rashin kunya na ce min wai kawu da yayi baba ya ce rashin kunya mai girma kuwa don ya kamata ya fi kowa sanin cewa kai din ba wai ba ne tunda ya san uwarta ce tasha nono ta bar maka, don haka tunda ka nemi ya janye maganarshi ya ki to ni nasan kai ba wai ba ne a wurin uwata, shi yasa ma nake shugabantar da kai akan dukkan al’amuranta, nima kuma ba zan yarda ya maida kai wai ba, don ka wuce wai din, yaya Almu ya yi maza ya ce to kayi hakuri Baba na janye maganar tawa raina ne ya baci da irin abin da Junaidu yake yi min, Baba ya ce eh ai nasan ranka ne ya baci shi yasa kayi mishi ràshin kunya a gabana ya kuma nemi ka janye rashin kunyar taka ka ki, saboda haka zan koya maka yanda zaka rinka yin magana dashi nan gaba ko ranka ya baci saboda Junaidu surukinka ne, kai Junaidu yaya Junaidu ya yi maza y ace na’am Baba, Baba ya ce mishi ka dauki uwata ka tafi da ita gidanka, kuje can ku sasanta randa Lamido ya gane kai din kawunta ne da gaske ba kawun wai ba ne sai ka mayar mishi da ita gidanshi.
Umma ta yi maza ta ce a’a Alhaji kar kayi irin wannan hukuncin a tsakaninsu shi Lamido ya ba Junaidu hakuri kawai ya dauki matanshi gobe su tafi gida.
Baba ya ce ba zata bishi ba, ai har da laifinki a cikin rashin kunyar da ya yi wa Junaidu, a gabana ya kira shi wai? Junaidu wai ne? A haka Umma tana kuka Baba ya zartar da hukuncin in bi yaya Junaidu gidanshi, ni kam nayi matukar yin murna da hakan saboda na riga na gaji da yaya Almu da matarshi ko da dai a yanzu na daina jin zafin da nake ji a zuciyata, game da su, to amma kuma ina bukatar nima in boye musu cikin da nake dashi kamar yanda shima baba ya ce bai son a baza labarin cikin ya fi so kawai a bar shi ya fito da kanshi a gani.
Ina zaune gidan Yaya Junaidu daga shi har Anti Rahma ji suke kamar zasu kashe ni saboda tarairaya ta da suke yi, ga kuma ya’yansu da suke matukar debe nmin kewa wadanda nayi matukar shakuwa dasu nake kuma son su kamar me, na yi matukar sakewa a gidan yaya Junaidu sau goma shima in ya shigo gidan sau goman kuma zai tambayi Anti Rahma ina Adawiyyah take? Ta ci abinci kuwa? tasha maganin ta? Nan da nan na dawo cikin hayyacina na samu lafiya da kwanciyar hankali a dalilin na rabu da bacin rai gashi nan babu mai kuntata min.
Yaya Almu kuwa yazo gidan nan ya kai sau goma don suyi maganata da Yaya Junaidu shi kuwa yaya Junaidun ya ki yarda suyi maganar sai suyi hirarsu su gama in ya kawo mishi zance na sai ya ce mishi mu bar wannan maganar tukuna sai ka gane ni din ba wai ba ne, yaya Almu ya ce haba Junaidu na ce kayi hakuri kan abin da ya faru ba zan sake ce maka kawun wai ba ka taimake ni ka barni in tafi da matata Junaidu.
Yaya Almu yayi shiru yana sauraron yaya Junaidu ya ce mishi to zan bishi mu tafi, sai kawai ya ji ya ce mishi to kaje sai na duba tukuna, abin yayi matukar bata mishi rai ya ce amma dai kasan babu gaskiya da adalci a cikin lamarin nan naka Junaidu, me nayi da zafi haka da zaka goyi bayan wannan abin da ake yi min? Me nayi wa Rabi wanda ba a taba yiwa wata ba? Ka fini adalcin aure ne? Yaya Junaidu ya ce to ka dai kama bakinka, yana fadin haka yaya Almu ya mike ya bar gidan.
Kwana biyar bayan nan sai ga aike daga gidan Baba wai maza-maza muje ana neman yaya Junaidu dani a lokacin nan kuwa kwanana arba’in ne cif a gidan Yaya Junaidu na yi mulmul, nayi gwanin sha’awa nayi kyau har ba a magana na maida jikina na murje nayi fes dani gashi nayi yar kiba mai ban sha’awa.
Mun isa gida muka samu Baban Tudu ashe shi ne yazo, yayi aiken muna shiga falo ya ganmu ya fara yin magana an ce maka kawun wai Junaidu, ni kuma na ce maka kawun banza kawun wofi, in ba kawun banza ba wa ke shiga gidan aure ya fito da ‘yarshı? Wannan yarinyar ce mara lafiya? Ja’ira mara kunya mara jin magana, kina wani zazzare ido kamar an shake k, kin samu ana daure miki gindi kina yiwa Babangida rashin mutunci, a kanshi aka fara yin mata biyu? me yake yi miki? Har ya kara aure? Wannan dai shi ne laifin nashi in ban da shi kuma ban ga abin da yayi muku ba, kai Junaidu ka fita daga idona ka fita daga goyon bayan Adawiyyah da kake yi tana yi wa mijinta rashin mutunci, wannan ai abin kunya ma kake yi don me za ka rike mishi matarshi? Maza-maza ka maida Adawiyyah dakinta, Yaya Junaidu ya amsa mishi ya kuma bashi hakuri, nima aka sallame ni na koma dakin Ummana akan zan shirya in bi Yaya Almu mu tafi tare, saboda har yanzu Umman tana nan don Baba ya ce ba za ta koma gida ba zata zauna nan ta kula da lafiyata, sai na koma dakina tukuna, itama zata soma canje-canje da su amma a yanzu canjin yana tsakanin Umma Amarya ne da Umma karama, ina cikin zaman sauraron yaya Almun ban san yadda aka yi ba sai kawai naji an ce ya tafi ba tare da ya yi sallama da kowa ba.
Tun daga nan ban sake komawa gidan yaya Junaidu ba ina zaune a gida daga Baba har Umma ji dani suke yi kamar zasu lashe ni, gashi kuma wannan karon Umma Amarya ma tazo tana nan kullum da sassafe take aiko min da abin karyawa wanda take shirya min da kanta, sai dai a yanzu duk da halin da nake ciki na kwanciyar hankali tunanina ya koma kan mijina na gaji da ganin abinda ake yi mishi kullum yazo gida sai ranshi ya baci so yake in koma dakina Baba ya hana nima a yanzu na fi son dakin nawa, yaya Almu mijina ne da muke .matukar son juna ni dashi, mafi yawancin abin da ya rinka shiga tsakanina dashi a baya daga mas’alar rashin haihuwa ne a yanzu bana tare da wannan mas’alar ciki ne dani har na tsawon watanni takwas har da wasu kwanaki, ba na jin haushin kowa ji nake tanfar ba zan sake bacin rai ba a duniya, tunda babbar mas’alata an riga an yaye min ita, a yanzu babu abin da nake sha’awa irin ace na zauna kusa da yaya Almu na yaye mishi cikin dake tare dani wanda nake ta faman boyewa cikin manyan riguna ya gani, in ga irin nashi farin cikin da zai yi to babu hali, Baba ya ce bai yarda a gayawa kowa sai dai duk da haka yau kam nayi kewar yaya Almu, ji nake tanfar in ganni a gabanshi na tsunduma cikin tunanin hidimominshi da alhairorinshi iri-iri a gare ni tun daga kuruciyata can baya lokacin da nake ganin tanfar ni dashi din uba daya muke har kawo zamana dashi a matsayin miji da mata, zuwan Lailatu da kuma haihuwar Rabi’atu da tayi da abin da ya yi ta faruwa a tsakaninmu a wannan na tabbatarwa kaina da cewar yayi komai don yayi adalci abin da ya faru na kuskure kuwa wannan ajizanci ne irin na dan adam, don haka ba ma shi da yake mijina kuma dan uwana ba, hatta Lailatu dake kishiya wacce mafi yawancin sabaninmu dashi ya auku ne saboda ita na yafe mata duk wani abin da tayi in na ganshi kuma zan roke shi gafara kan irin ‘yan rashin kunyar da na rinka yi mishi a dalilin kishi, ko da yake dai ni dama ba mai dabi’ar maidawa miji magana ba ne matukar dai ba wacce zai ji dadinta ba ne, balle aje ana jero mishi fiye da abin da yake fada saboda Ummana ta riga ta tarbiyantar dani da cewar shi miji girmamashi kawai ake yi a kuma yi mishi biyaiya, na mika hannu na dauki wayata na soma danna lambobinshi da nufin kiranshi karo na farko da nayi hakan tun bayan dawowana gida, har ta fara alamar zata shiga sai nayi maza na katse ta saboda tunanin wata kila yana tare da matarshi musamman ganin lokacin farkon dare ne, sai dai ina katsetan kiranshi ya shigo tayi kara har ta katse ina kallon wayar ban dauka ba ya sake har sau uku ban motsa ba da dai naga ba zai daina kiran ba sai kawai na kashe wayar tawa gabadaya.
Tsawon daren nan ban wani runtsa ba tunanin yaya Almu ya dawo cikin raina ban san dalili ba kishi ne yake damuna, na ni ina gida a zaune yaya Almu yana gidanshi tare da matarshi wajen wata hudu na bar mata shi ita kadai, Umma dake kwance can gefe da itama ta hakura da nata mijin ta bar wa Umma Amarya, saboda wai ba za ta rinka barina ina kwana ni kadai a daki da tsohon ciki ba saboda ba ta san abin da zai faru cikin dare ba, ta bude ido ta kalle ni ta ce min lafiya yau ki ka kasa bacci ko wani abu yana yi miki ciwo ne? Cikin natsuwa na ce mata lafiyata kalau Umma, yaya Almu ne kawai…..shiru nayi ban karasa ba saboda ganin yanda ta lumshe idonta a hankali ta kuma juya min baya alamar bata son jin maganar.
Washe gari da sassafe sai ga Yaya Almu ya iso har cikin daki ya shigo ya same ni, don da nayi sallah komawa nayi na kwanta, yayi kwalliya sosai yayi matukar yin kyau sai wani annuri ke fitowa daga fuskarshi ga kanshinshi na kowane lokaci a tare dashi, a bakin gadon ya zauna ya zuba min ido yana kallona me ya faru Rabi? Jiya kinyi nufin kirana ki ka fasa na kira ki kuma ki ka ki dauka daga baya ma ki ka kashe wayar me kike son gaya min? Na ce ban kira ka ba, ya yi murmushi ya ce ban san ki da karya ba Rabina gaya min kawai in kinji kewata ne Na daure fusaka na ce in yi kewarka saboda me tunda kai ba tawa kewar kake ji ba, ya ce uhun Rabi kenan, dama kin zo kin zauna a gida ne don kina tunanin zan rinka kewarki? Don ki samu ki yi ta azabtar dani ta haka, duk abin da ki ka rinka yi min muna tare bai ishe ki ba sai kin baro gidan kin dawo nan kin zauna saboda in yi ta azabtuwa da kewarki? Saboda in kuntata in kasa jin dadi, don kina ganin in ba kya nan a gidan ba zan samu natsuwar da nake bukatar samu ba, saboda ki nuna min ni din ba komai ba ne a wurinki, saboda ki nuna min cewar za ki iya rayuwa mai dadi ko da kuwa babu ni a kusa da ke har ma kina ganin in kinyi nesa dani za ki fi samun kwanciyar hankali don haka ma ki ka tanadarwa kanki wurin zama, to in ke mace za ki iya nuna irin wannan jaruntakar to ni namiji fa? Ko fa ni kadai ne mijinki iyakar kuma gatan da su Umma da Baba zasu yi miki bai wuce dai wanda suke yi mikin yanzu ba, su yi ta tattalinki suna tarairayarki kina kiba irin ta rashin zuciya, ni kuwa fa? Ya zuba min ido yana kallona ban san dalili ba sai kawai naga na kama yi mishi kuka bai fasa ba ya ci gaba da maganarshi zaman gidan nan da kike yi dai kema kin san ba bisa yardana kike yi ba. Fin karfina aka yi aka rike min ke, don haka ke kin fi kowa sanin irin zaman da kike yi, naje na kai kara gun Baban tudu shima ban san me Baba ya ce mishi ba, ya ce wai in dan kara hakuri kadan, to zanyi tayin hakuri Rabi ba kadan ba ma zanyi mai yawa, to amma ki sanı daga yau ban yarda ki sake fita daga cikin gidan nan ba ko da kuwa gidan Junaidu ne balle in ji labarin kinje wani wuri ko da kuwa yiwa su Umma rakiya ne zuwa tafiyarsu, ki gaya musu na ce ban yarda da fitarki zuwa ko’ina ba kiyi ta zama a gida tunda gidan yana yi miki dadi.