Sanin halin Ummana da nayi na kin dabi’ar ‘yan zamani na nuna rashin kunya da rashin kara kan yayan da suke haifa na fari ya sa nayi matukar kamewa don dai in kara mata farin cikinta, tun washe garin haihuwar da yaya Almu yaje gida da zai dawo ya taho min da Baba Talatu da Rabi’atu, don haka Baba Talatu ke kula da al’amarin yaron yayin da Rabi’a kuwa take manne dani don bata manta ni ba, Lailatu kuwa da ‘yan uwanta ba za a ce musu komai ba don ko barka ba su zo ba, itama Lailatun sai da taga abin zai zame mata bacin rai sannan ta biyo shi suka zo tare saboda sun ce wai dan ba na asali ba ne dashen shi akayi min don dai an matsu a ga na haihu.
Gaba daya Baba ya hana shagalin suna mai yawa ya ce maimakon a maida hankali ga yin Shagalin suna gara ayi ta addu’a Ubangiji ya raya abin da aka samun ya kuma sa ya zamo mai albarka don haka gaba daya sai ya ce a tafi katagun ayi wannan dalilin yasa tun ana saura kwana biyu sunan yaya Junaidu da iyalinshi suka nufi katagun ya hada har da Rabi’atu wai ba za’ayi sunan Baba ita ba itama Umma amarya shiryawa ta yi ta yi tafiyarta wai zata kóma gida saboda masu zuwa gidan don Umma karama ma tana katagun din sai aka barni daga ni sai Ummana sai ko Baba don Baba Talatu ta tafi.
Ranar sunan da safe Baba ya shigo daidai Umma tana fama da yaron wanda ya tashi da rikici sosai yasa hannu ya karbe shi daga gare ta yana kallon kukan da yake yi tare da yi mishi magana tanfar dai yana jin abin da yake gaya mishi haba Mallam me yà same ka? Menene damuwarka? Kai kuwa ai hakuri ya kámata kayi don kuwa wanda ka gaji sunanshi mai hakuri ne, Umma ta daga ido cikin natsuwa ta kalle ni ta ce sun fadí sunanne? Baba ya ika mata shi ya ce bata shi ta bashi nono tayi maža ta karbe shi ta miko min, ina bashi ya kama ya shiga tsotso yana ajiyar zuciya tanfar da ba’ayi ta fama dashi ya kama ya ki ba, Umma tana zaune tana sauraron abin da Baba zai ce mata sai ya kalle ta ya ce dazu Junaidu ya yi min waya ya shaida min cewar Abdulhakam Alhajin tudu ya kira mish, ba Umma ba hatta ni da ban san shi ba gabana faduwa yayi don ban yi zaton hakan ba sunan mahaifina mutumin da ban zo duniya na same shi ba sai dai tun daga ranar da aka ba ni labarinshi shi da matarshi ban taba fashin yi musu addu’a ba.
Umma ta daga ido ta kalli Baba ta ce ikon Allah, Abdulhakam ne? Sai kuma hawaye suka biyo bayan maganar tata suka yi ta gudu a fuskarta shar, shar,shar suka ki tsayuwa, Baba kuwa sai ya kawar da kanshi ya fita ya bar mu, ina gama bashi nono Umma ta karbe shi tasa a bayanta ta goya ta shiga hidimominta nima na gyara na kwanta wunin rannan kuwa babu abin da zuciyata ke yi in ban da tunanin mahaifana Abdulhakam da Uwa kamar yanda su Umma suke kiranta.
Satinmu biyu da haihuwa yaya Almu ya fara tasa Umma a gaba da maganar komawana dakina, ta ce ya dan kara hakuri muyi koda wata guda ne ya ce mata to, muna cika watan ya dawo ya ce mata Umma nazo ne kan alkawarinmu na komawar Rabi gida, Umma tayi murmushi ta ce ai kuma alkawari abin cikawa ne tayi maza ta mike ta nufi dakin Baba zuwa can sai gata ta dawo fuskarta a daure, ta nemi wuri ta zauna ta kalli Yaya Almu ta ce mishi Alhaji ya ce bai hana ka tafiya da matarka ba duk lokacin da ka shirya yin hakan, amma ya ce in gaya maka ita kadai zaka dauka ban da Abdulhakam, gabadayanmu daga ni bar yaya Almu tsura mata ido muka yi muna kallonta.
Umma ta ci gaba da magana nayi kokarin ya yarda ku tafi in yayi wayo sai a dawo mishi dashi bai yarda ba, shiru yaya Almu yayi kamar ruwa ya cinye shi don haka maganar tafiyar dai ranar bata yiwu ba.
Ranar da muka cika wata biyu cif ranar ne kuma yaya Almu ya gama azumi sittin din da ya jera ranar kuwa a Legos yayi buda baki, ni na shirya mishi abin shan ruwa na kai mishi dakin da yake sauka bayan na tsala mishi kwalliyar da ko a ranar sunan ban yi irinta ba, sai da ya gama addu’o’in shi muka shafa kafin ya jefa dabinon da ya yi buda bakin dashi bakinshi duk abin da ya ci a lokacin dangin fruit ne sai da yaje yayi sallar Isha’i, ya dawo sannan ne ya soma cin abincin da na shirya mishi yana cin abincin ya daga ido yana kallona yanzu yaya zamu yi da maganar Baba Rabi? Na ce kamar yaya? Ya ce to za ki yi ta zama a gida ne don renon yaro? Ai gara dai musan abin yi ko? Ni yanzu nazo mana da wata dabara zan rinka zuwa kawai ina yin kwana biyu anan in-je can in yi kwana biyu zan koma rabon kwana tsakaninki da Lailatu kin san ba zai yiwu inyi ta zaman zuba miki ido ba Rabi ba sai na tsaya yi miki dogon bayani ba tunda a yanzu babu maganar jan rai da wahalarwa a tsakaninmu.
Na ce eh yaya Almu amma dai gaskiya irin wannan tsarin ai zai yi wahala yau kana nan gobe kana can kuma a gabansu Umma da Baba suna kallonmu ma bai yi tsari ba, ka dai yi hakuri kawai ka dauka ni na zo wankan gida ne a gida kuma kana da matarka in ka samu lokaci kawai sai ka rinka zuwa duba mu.
Ya sake kallona kafin ya ce min zan so mu fahimci juna ta yanda zamu taimaki kanmu mu duka ni da ke da yaron in kin yarda da hakan zan iya barinki har wata hudu nan gaba don ya samu yasha nono na tsawon watanni shida kafin in dauke ki mu tafi mu bar musu shi in kuwa baki yarda ba sai mu tafi yanzu mu barshi ai ba nono ke raya mutun ba, nayi maza na ce hu’un ba zan ya ba ya ce to shi kenan amma za ki kwana anan yau ko? Na ce ba zan iya ba hira kawai zan yi in tafi ya ce to jeki kawai ki bar hirar bana so na ce to na tashi nayi tafiyata.
Washegari da safe na fito daga wanka kenan na gama shafa mai ina cikin sanya kayana sai kawai Umma ta ce mun wai baba ya ce a tambaye ni in akwai abin da nake so ayi mun in fada don satin nan zan koma dakina, na kalli Umma cikin natsuwa ace mata Umma da yaron? Ta yi maza ta tsuke fuska ta ce mun babu yaro anan gidan za ki bar mishi shi tunda Lamido ya ce a bashi ke ku tafi naga kuma kema tun randa uwarki ta haife ki ta bar mishi ke shi ya rene ki ba nono ba, na yi maza na ce mata kiyi hakuri Umma saboda na gane ranta ya baci da maganar da nayi tana jin na bata hakurin kuma ta juya ta fita.
Umma ce taja shirin komawar tawa har aka kai sati biyu saboda ta gane ina da damuwa game da barin yaron, duk da dai na boye don ba zai yiwu Baba ko Umma su zartar da hukuncin da ba zan iya hakuri dashi ba ko da kuwa wane iri ne.
Ana gobe zan koma Anti Rahma ta dawo daga Kaduna saboda ita ta jagoranci aikin gyaran wurina da aka yi ina jin ta tana baiwa Umman labarin irin yanda aka tsara wurin da yanda aka tsarawa yaro dakinshi Umma tayi murmushi ta ce shi Junaidun bai san ban da yaron ba ne a komawan har yake kashewa dakinshi kudi? Anti Rahma ta zaro ido tana kallon Umma sai dai ta kasa ce mata komai.
A haka na koma gida washe gari Umma karama ta maidani don da yaya Almu yazo daukarmu sai Ummana ta ce mishi ya tafi da Baba Talatu da Rabi’atu ni kuwa Umma karama ce zata dawo dani hakan kuwa aka yi tayi waya ta ce mata tazo ta maida ni dakina.
Na koma gida na samu Lailatu cikin wani irin hali bata yi zaton dawowana ba watakila ta yiwa yaya Almu maganar raba mana gidane don ta fahimtar dashi cewar bata son zama dani, Lailatu bata dauki maganar dawowa na da sauki ba watakila tafi gwanmace wa da wata sabuwar kishiyar aka kawo mata kwana biyun farko da nayi a gidan nayi sune cikin halin zazzabi mai tsanani a dalilin ciwon nonon da ya rufan mun shi da kanshi yaya Almun duk zumudin shi na son in dawo da zalamar da ya nuna a sarari ya hakura ya saurara min saboda ganin halin da nake ciki amma hakan bai sa Lailatu ta shigo dakina ta tambaye ni yaya jiki ba, gaba daya hidimar gidan kuma ta tsame hannunta wai ba girkinta ba ne, duk da hakan da tayi ban canza ba daga niyyar da na dawo da ita don kuwa Umma ta gaya min cewar ya zama dole in samarwa yaya Almu kwanciyar hankalin da yake bukata a cikin gidanshi na ce mata to ai wancan karon ma ba akan son raina aka yi wancan zaman ba ta ce eh amma ai ke macece gidan ki kuma tazo kin san yanda zaki yi ki gyaran da ya dace, gaba daya laifin abin da ya farun a kaina Umma ta dora shi shima yaya Almu ta ce abin da ya yi duka ba wani laifi ba ne hakan da tayi ya sanya ni na yi ta yi mata kuka.
kwana uku nayi ina fama da zazzabi na samu sauki don haka washe garin rana ta hudu ranar da zai sake dawowa dakina kenan sai na wastsake na fito nayi shirin karbar mijina a yau tun safe nake ta shirya irin nau’o’in abincin da zan shirya mishi gaba daya littatafan girkina na dauko ina ta dubawa don in ga abin da ya dace in shirya mishi.
Ina zaune a tsakar gida ina jira a gama min gyaran kicin din mai aikin da Lailatu ta kawo ce mai yi min aikin Azumi don na riga na yanke shawarar yin mu’amalla da kowa, sai ga Rabi’atu ta nufo ni da gudu zata zo wurina cikin murna da dariyarta kan ta iso sai kawai naga Lailatu ta biyo ta da sauri ta cafe ta tana cewa ja’ira mara zuciya, ni duk tsiyar mutum ba zai lashe min ke ina kallonshi ban ce mata komai ba, sai da na gama komai bayan cin abincin dare nayi kwalliya sosai wurin yaya Almu zan tafi sai na shiga dakin Lailatu nasa hannu na dauki Rabi’atu dake bacci na sabata a kafadata zan fita da ita ta kalle ni ta ce ina kuma za ki kaita? Na ce zan je in lashe ta tawa ce ai tunda agabanki akan idonki Babanta ya bani ita daga yau na karbe ta na wuce naje na kwantar da ita a dakin da aka shirya don yaro wanda ba’a dawo dashi ba.
Babu fitinar da Lailatu bata yi akan karbar yarinyar da nayi ba har yaji ta yi ta ce wai ba za ta dawo ba sai an mayar mata da ‘yarta, Ummana ma ta ce in mayar mata da ‘yarta tunda ta dage kan hakan na ce mata sai dai in ba za ta dawo ba tayi ta zama da kuwa naga zata tilasta ni mayarwa Lailatu da ita nayi maza na gayawa Baba, shi kuwa ya ce ai ba kwace mata ita nayi ba shi bai taba ganin in da aka kwacewa uwa danta ba musamman ma da yake ba barin gidan akayi da ita ba don haka ta ishe mu dukanmu suka gaji da rike ta suka dawo da ita, aka zauna a haka, ni kuwa na dauki matakin duk in da zani da Rabi’a nake tafiya har Ummarar da muka tafi da Anti Rahma da ita na tafi ban barta a gida ba.
Gaba daya al’amuran gidana na karbe su babu wani abin da nake sanyawa Lailatu ido akanshi in tana sha’aninta da mijin ta babu ruwana in kuma hidimar gidana ta ce ba zata yi ba sai kawai in sa ta yi ba tare da na saurareta ba, da kuwa na ji mijinta ya ce min ciki ne da ita sai kawai nasa aka nemo mana mai girki na danka mata hidimar abincin gidan amma ban da na yaya Almu wannan ni da kaina nake yi mishi ban kuma damu da cewar ga girkina ba ga nata ba, ana cikin haka nima na samu kaina cikin matsanancin halin zazzabi ga wasu kurarrajin bakin da nake fama da su nayi kamar in gayawa yaya Almu sai kuma kawai na ce bari dai in hakura tunda yana zumudin cikin da Lailatu ke dashi wacce har a tsakar gida take gayawa masu aiki cewar wannan karon namiji itama zata haifa ban tanka ba kallon su kawai nake yi musamman ma da yake ba ni take wa zancen ba.
Rannan ina zaune a gida ina tare da yaya Almu abin karyawa nake shirya mishi sai ga yaya Junaidu yana sallama yayi maza ya mike ya karbe shi suka shigo tare nayi mishi sannu da zuwa na kuma zuba mishi nashi abin karyawar shima yana cikin karyawan ne ya kalle ni ya ce min Mustapha ya gaya miki cewar zan yi aure ko Adawiyyah?
Da hannu biyu na dafe kirjina saboda tsananin kaduwar da nayi na ce aure yaya Junaidu? Me Anti Rahma tayi? Nagga kuma tana iyakacin kokarinta, ya yi maza ya daure fuska ya ce kina nufin sai mace ta gajiya ne ake kara aure? Da aka ce mu auri mata bibiyu ko uku-uku ko hurhudu kina nufin in matan sun gajiya ne zamu yi hakan? Ba haka ba ne in mun gamsu da adalcinmu ne aka bamu ikon yin hakan in kuma muka ga ba zamu iya ba sai aka ce to mu zauna da guda daya, nayi ajiyar zuciya mai karfi na ce haka ne to Allah ya sanya alheri amma Anti Rahma fa? Ya ce na bari Umma zata je gidan tayi magana da ita ni kam zaman Jimami na koma na rasa me zanyi? Murna zanyi kawuna zai yi aure ko kuwa bakin ciki zanyi za’ayiwa Anti Rahma kishiya.
Shi da kanshi yaya Junaidu ya gane jikina yayi sanyi da zancen auren nashi ya kalle ni ya yi murmushi ya ce Adawiyya kenan wato ku dai mata zumuncinku karfi ne dashi in ba haka ba ni da Rahma wanene ya fi kusa da ke? Na yi murmushi na sunkuyar da kaina kasa ina yi mishi bayanin ba wai bana murna ba ne tashin hankali ne ba shi da dadi ya ce haka ne to ki kwantar da hankalinki babu wata wacce zata zo ta dagawa Rahma hankalinta in dai ba ita ce ta nemi ta daga wa wani ba, zan yi iyakar kokarina don in ga sun zauna lafiya, na ji dadin kalaman nashi na ce to Allah ya sanya alheri ya ce amin, na sake wani murmushin na ee lalle za muyi biki kenan ga bukin gidan ma ya zo yau bai fi saura kwana goma ba ga kuma wannan yaushe za ayı?