Skip to content
Part 49 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Ana cikin wannan halin rannan ina kwance kan gadona da rana na ji wani motsi da yayi min kama da motsin da a cikina zumbur nayi na mike zaune na kasa kunne ko zan sake jin wani motsin ban ji ba, shiru ban sake jin komai ba na yi ta duba bakina ko zanga wurin da kurji ke shirin fitowa babu wata alama, har na hakura.

Washegari dai da sassafe na nemi izinin yaya Almü na zuwa asibiti, ba tare da ya nemi sanin abin da zani inyi ba ya bar ni na tafi ina zaune a gaban Likita yana yi min dariyar yanda aka yi wai na haihu har da ‘yan tagwaye amma na zauna da ciki yayi watanni ban gane ba, cikin zuciyata na ce Albamdulillahi na karbo magungunana na kama hanya na dawo gida ko Umma ban gaya wa abin da nake ciki ba, jan bakina nayi na yi shiru, gashi kuma nayi sa’a wannan cikin yasha banban da saura, cin abincina nake yi bani da wata mas’ala sai nayi kyau nayi kiba nayi mulmul gwanin sha’awa cikin kuma ya bace a jikina kamar babu shi, an dauki lokaci mai tsa wo yaya Almu bai gane ba shima don anyi dace ne yayi motsina shi kan ya ankara kuwa sai kawai yaga na haihu sai dai wannan karon ma da namiji aka samu sai aka sanya mishi Muhammad Bello wato sunan Baba kenan tun daga wannan lokacin ban sake wani tunani na neman hutun haihuwa ba tuni ma na daina sha’awarshi na kuma koma ganin wautar mata masu yi saboda irin illolin da ya haifarwa.

Abdulhakam bai gama cika shekaru takwas ba a duniya sai da na haifar mishi kanne biyar gabadayansu kuma maza don haka a yanzu yaya Almu ya’ya bakwai ne cif dashi mace daya Rabi’atu sai maza shida dan karaminsu kuwa shi ne takwaran yaya Junaidu.

A wannan lokacin tausayin Lailatu nake ji tun daga haihuwar Rabi’atu ko bari bata sake ba, tayi karyar cikin har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido ga Maryam mai auren kwanannan wai har ta haifi ‘ya’ya uku a gidan yaya Junaidu. Anti Rahma shida amma ita shiru, duk da mun yi kwanaki sun kai hudu ni da ita ba wani kula juna muke yi ba saboda in suna ‘yartsama da yaya Almu sai ta hada har dani da na ji tana yi mishi maganar zuwa asibiti bai kula ba wai shi ya gaji da biyan kudin wankin cikin da babu amfani, shiga daki nayi na dauko kudi nazo na bata na ce mata jeki Asibitin, ta ce a’a tana dasu na ce karbi dai nawan ai ba ke ya kamata ki biya kudin asibiti ba, ta je ta dawo kuma na tambaye ta abin da suka ce, bata boye min ba don haka da kaina naje na samu Baba na gaya mishi mas’alar da Lailatu ke ciki, bayanin da nayi mishin yasa ya sanya yaya Junaidu ya shiryawa Lailatu tafiya kasar Cairo don ganin Likita.

Bayan dawowan Lailatu Umma karama tazo gidan ban san me ta ce mata ba na dai ji ta kawai tana cewa a’a Umma ni na riga na gaji da wannan fitinannen zaman, a yanzu nafi bukatar zaman lafiya akan komai, musamman ma da yake duk mugun abin su da ake gaya min nima dai ita mun yiwa juna rashin kirki, tunda ita kam sha yanzu ne magani yanzu, to uwarta kam in na ce ta taba yi min wani abu ba alheri ba na yi mata karya, don haka a yanzu zan koma amfani da zahirin abin da idona ya gani maimakon jita-jita da tsofaffin labarai na abin da aka yi shekara da shekaru, ina jin Umma karama ta kama salati nayi maza nayi wucewa ta, cikin zuciyata dai murna nayi da Lailatu ta gane fitintunun dasu Umma karama ke sanyata ba komai zasu haddasa mata ba illa rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Tun daga wannan lokacin na dauki matakai masu yawa don ganin mun zauna lafiya da Lailatu, don haka in zan sai wa kaina abu sai itama in saya mata, in kuwa naji tana neman wani abu wurin yaya Almu bai yi mata ba sai in yi mata da kuma na lura tana kokarin gyara mu’amallarta da yara maimakon da da bata shiga harkarsu yanzu har tana sauraron maganarsu sai nima na rinka dorata kan al’amuransu, ko wani abu nasu ne ya taso sai in ce yaya Almu ya sata tayi, shima kuwa yayi matukar jin dadin hakan, nan da nan sai zaman mu ya dawo gwanin sha’awa rannan na shirya zan tafi makarantar islamiya ta asabar da Lahadi da nake zuwa sai na ce mata Lailatu ko zan karbo miki form ne mu rinka zuwa makaranta tare muna jin wa’azi? Kinga ba wani wahala ne da ita ba sau biyu ne kawai a sati? Yaya Almu yayi maza ya ce min a’a Lailatu ai tun tana ‘yar karama taji wa’azinta wuce su nayi na tafi don nasan zolayarta yake so yayi da zan dawo sai nazo mata da form din ta cike muka soma zuwa tare. Nan da nan ni da ita muka zama tanfar ‘yan uwa komai zamu yi tare muke yi, in wani abin gida ne ya taso sai in shawarce ta mati yawan cin lokaci kuma na kan yi amfani da ra’ayinta ne in bar nawa a wannan lokacinne na fahimci Lailatu mutunivar kirki ce, mafi yawancin abubuwan da tayi ta yi a baya sata aka rinka yi ba halinta ba ne ita da kanta Lailatu taji dadin halinta da ta canza saboda yadda matsayinta ya karu wurin yaya Almu ni da kaina ban san yana yi mata irin son da yake yi mata ba sai a wannan lokacin da ta yarda da zaman lafiya, nasha jin shi yana cewa yana girmamata da ganin darajarta tare da jin tausayinta saboda ita ce uwar Rabi’atu ‘yar da yake so kamar me? Sannan gashi bayan ita bata sake ba don haka a yanzu shagwaba take yi mishi irin yanda yanda taso nima kuma bana sanya ido kan abin da ya shafe ta da mijinta, tunda tana bani girmana ta kuma sa hannu biyu ta rungumi al’amarin yara.

Shekaru goma bayan wannan lokacin na isa gida da yamma ni kadai amsa kiran da Umma tayi min nayi.

Gidan cike yake da jama’a babu masaka tsinke, duk kuma wani wanda yake cikin gidan in ma dai da ne da baba ya rike ko kuma jika don haka taro ne na yan uwa, ma’ana babu wani bare a ciki.

Sashin Umma Amarya na fara zuwa, Jibrin na fara gani ya fito da sauri zai karbi jakar dake hannuna, na kalle shi nayi murmushi na ce mishi ga dukkan alamu aiki kuke yi saboda irin gumin da nake gani a tare da kai don haka jcka kayi aikinka ni zan iya kai jakata cikin daki tunda ai kaga makale take a hannuna ya taya ni murmushin da nake yi ya wuce ya tafi, na samu Umma a zaune a nemi wuri na zauna na gaishe ta na ce mata yaya jiki ta ce da sauki ai na ji sauki sosai na ce babu inda yake miki ciwo kenan? Ta kalle ni cikin natsuwa ta ce anya ana yin haka? Kayi irin wadannan shekarun da muka yi sannan ace an zauna babu abin da yake yin ciwo? An dai gode Allah tunda komai kana iyawa, na ce haka ne Umma sai da muka danyi hira kafin na mike na nufi wurin Umma karama na gaishe ta sannan naje wurin Ummana, tana ganina ta daure fuska ke in banda na kira ki in ce ko da ba za ki zo ba ne? Na yi shiru ban ce mata komai ba ta kama yi min fada, Lailatu dake wurin ta kalle ta cikin murmushi ta ce mata da kuma tahowa don kanta tayi Umma da kinyi mata fada kince tayi rashin kunya gaba daya aka kwashe da dariya Umma ta yi murmushi ta ce to shi kenan na bar fadan tunda yar uwarki ta tare miki to amma ai wannan sha’ani ba biki bane hidima ce ta addini ai kya zo ayi ta dake, ni dai ban ce mata komai ba. Anti Rahma ta shigo wacce ita da Lailatu’ ne a tsaye kan hidimar tunda aka fara ta sunyi kusan sati guda a gida suna shirye-shiryen zuwan ranar sun sauka Umma yanzu an tafi dauko su nan ba da dadewa ba za su iso, Umma ta kama murmushi tana share hawayen dake zuba a idonta tare da fadin babu Abdulhakam da uwa sai ni da Alhaji mune muke ganan musu, nan da nan aka shiga yi musu addu’a ita kuma ana bata hakuri.

Wajen karfe takwas da Rabi na dare suka iso kai tsaye babban falon karbar biki aka zarce an riga an shirya komai don haka ba’a dauki wani lokaci mai tsawo ba aka soma gabatar da al’amura bayan an gabatar da nau’o’in abinci iri-iri ga jama’a.

A hankali na shigo wurin daga can baya na tsaya ina kallon duk abin da ake yi Abdulhakam wanda ake yin abin dominshi yana zaune tsakanin baba da yaya Junaidu tanfar wani babba alhalin shekaru goma sha bakwai ne kacal da shi, kullum kamanninshi da baba kara bayyana suke yi abinda ke sa wa mutane da yawa suke zaton wai ko karamin danshi ne kamar kullum yauma anko suka yi dai dai yau ankon nasu ya dan banbanta a dalilin shi Abdulhakam yana sanye da alkyabba da kuma rawanin da aka nada mishi, Baba na samu yana magana kamar bayar da labari yana kuma maganar ne cikin murmushi alamar dai a Cikin farin ciki yake.

Ita kuwa ai hakurinta ba mai yawa ba ne uwarta ta fita hakuri, a zuciyata na ce a’a yau kuma me na yiwa baba yake kirana mara hakuri bayan na saba jin shi yane yabona akan hakurin? Da na kasa kunne da kyau sai na ji shi yana cewa, lokacin da ta rasa haihuwar nan ai nema tayi ta bijirewa Lamido na ce mata uwata aure daban haihuwa kuma daban ko babu haihuwa ana zaman aure ta ce a’a ita in bar ta kawai ta yi nesa da shi ya gara zama ya ce to a wancan lokacin nayi ta min addu’o’i da alkawura masu yawa saboda ina son auren nasu, na kuma san rashin-haihuwar ita ce babbar barazanar da auren yake fuskanta a cikin addu’o’i da alkawuran da na yi har da wanda  nayi yi dalilin taruwarmu anan yau na roki Allah ya baiwa uwata haihuwar da namiji da wasu mazan masu yawa bayanshi in ya bata da namijin to ni kuma ya bani rai da lafiyar da zan yi tarbiyar shi ta yanda zai zamo makarancin Alkur’ani wannan shi ne dalilin da ya sa da na ji tana da ciki sai na roketa da ta haihu mijinta ya nemi ta koma dakinta ba zai viwu in hanata ba sai nasa hannu na karbe jaririn duk da kankantarshi don nayi alkawari akanshi, to gashi nan a yau kun shaida alkawarin ya cika, sannan ita uwata bayan shi ta haifi wasu mazan har guda biyar ina ganin ma har yanzu bata da ya mace, ya dan juya da sauri yana sauraron abin da yaya Junaidu yake gaya mishi sannan ya juya cikin murmushi yana cewa au to, ashe kun ji wai daga bayan nan ta haifi Maryam cikin zuciyata na ce tafdijan wato ma Baba mancewa da ita yake yi, yanzu dai ga Junaidu nan zai gaya muku yanda tafiyar tamu ta kasance.

Yaya Junaidu yana mikewa sai ya soma godiya ga Ubangiji ya yabe shi kan alhairorinshi ya gabatar da salati ga Manzon Rahma (S.A.W) ya yi wa Alkur’ani kirari, ya fadi darajojinshi da daraicjin makarantunshi a ranar alkiyama da sakamakon wadanda suka tarbiyantar da yayansu akan karanta shı, da ya gama wannan sai ya shiga bayar da labarin gwagwarmayar da Abdulhakam ya yi a kokarinshi na yin haddar Alkur’ani mai girma da yadda suka tsaida shawarar shigar da shi cikin gasar karatun Alkur’ani don a kara zaburar dashi da ya zo karshe sai ya ce to tun a shekara bara mai alfarma sarkin Borno ya nada mishi rawanin zama goni a lokacin da ya lashe musabukar da ya shiga ta izifi sittin inda ya samu damar wakiltar kasa a musabukar duniya da za’ayi a birnin riyard ta kasar Su’udiya, to gamu a yau mun dawo ina kuma farin cikin shaida muku cewar shi ne yazo na uku, gaba daya dakin ya dauki kabbara mai karfi da aka natsa sai ya ce to kamar yanda aka saba a dukkan gasar da muke zuwa akan tuho da kyaututtuka to a wannan ma haka ne, an bashi dama ta yin karatu a jami’ar Madina an bashi kudi da littatafai to littatafai dama kullum shi ke amfani dasu kudi kuwa akan raba su ne a tsakanın malamanshi to wannan ma hakan za’ayi don haka a yanzu sai mu kara natsuwa don mu saurari karatun Alkur’ani mai girma daga bakin goni Abdulhakam Mustapha.

Abdulhakam ya mike cikin natsuwa dama kuma mai natsuwa ne bai da hayaniya gashi kama da kamun kai sai dai kuma fuskarshi bata rabuwa da fara’a cikin murya mai cike da natsuwa ga amo yana kuma karanto ayoyin kusa da karshe na cikin suratul Ma’ida, da ya gama sai ya koma ya zauna ya bar jama’a suna ta share hawaye, yaya Almu ya kalle ni a hankali ya ce min Allah ya yi mishi baiwa da murya ta karatun Alkur’ani, a hankali nima na ce mishi haka ne yaya, ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min gashi dai namu ne ni dake mu muka haife shi, to amma kin san ba renon mu ba ne bamu muka tarbiyantar dashi bai ba mu muka karantar da shi ba, Baba da matanshi guda uku ne suka yiwannan aikin mu namu ya’yan mun kwashe su duka mun kaisu karatun boko, na kalle shi cikin mumushi na ce mishi a bamu makara ba yaya ya yi maza ya ce to taimake ni rabina mu sake samun wani gonin kamarshi na ce mishi to.

Da muka shirya ni da yaya Almu zamu tafi sai na kamo hannun Maryam dina falon baba muka shiga shi da Abdulhakam muka samu suna cin tuwo da hannu a kwano daya tsayar mishi da yarinyar nayi a gabanshi ni kuma na durkusa a gefe na ce mishi baba gata nan na kawo maka ka ganta da kyau, Umma Amarya ce don nan gaba kar ka sake mancewa da ita baba ya zuba mata ido yana kallonta cikin murmushi zuwa can sai ya ce min na ganta da kyau uwata ba zan sake mancewa da ita ba duk inda na ganta kuma zan shaideta tunda ma gashi ta yi sa’a irin idanuwan Abdulhakam dina ne a tare da ita, ni da yaya Almu muka yi murmushi na fito naje na yi wa Umma amarya da Umma karama sallama sannan na nufi wurin Ummana da zamu yi bankwana da ita sai na ce mata Umma yi mun nasiha, ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min banı da wata nasiha da zanyi miki illa ta bin mijin ki rike shi gam da da hannunki bibiyu kiyi mishi riko irin Wanda kikaga nayiwa mahaifin shi ita kuwa kuwa kishiya ba ruwanki da lamarinta a Kullun dai ki tabbatar kin mata adalci,in baki mancema nama ai gaisawa suna da Karin maganar da suke cewa wai kowane tsuntsu kukan gidansu yakeyi,nace hakane imma nayi Mata sallama na like nake nayi sallama Dasu imma amarya da umma karama natafi naje na samu Yaya almu Dake ta faman jirana muka Kama January komawa kaduna badon hidimar ta Kareba saidon damamu kiranmu akayi muka Lailatul da anti Rahamane suke tsaye akan dukkan alamarin.

Akan hanyarmu ta komawa gida Ina kwance jikin mijina abayan mota yayin da direba ke janye damu,Yaya Almu ya ratsa hannayenshi ya Kara rungumo kafadata yace na gode miki Rabi da Kika zamo uwargida ta kirki a gareni, na gode Miki da Kika TSAYA wajen ganin na samu Zaman lafiya a tsakanin iyalina da gode Miki da Kika tashi shigowa gida baki shigo hannu haka ba sai Kika riko gishirin miyar umma kika tahomin tare dashi,na daga Kai ahankali na kalleshi cikin fara’a da murmushi nace mishi banyi nasarar yin hakan ba Yaya sai danayi nasarar yin dace da arziki da rufin asirin da Ubangiji yayi min wajen hadani da miji na kwarai bawa daga cikin bayinsa salihai,na godewa daya Sanya ka zamo miji gareni Kuma uban yayanmu,Dadi ya kamashi ya Kara kankameni ajikinshi.

Taimakeni Rabi taimakeni mu sake samun wasu mahaddatan acikin yayanmu, nace da iko Allah Yaya saidai aikin ba nawa bane ni kadai Dani da Kai da Lailatune zamuyi hakan, Yaya Almu ya kyalkyale da dariyar jin dadin kalamin da nayi mishi.

Fatan Alheri gareku dukkan ku na gode.

Hafsat chindo sodangi.

Karshe

<< Wace Ce Ni? 48

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×