Sati guda Yaya Junaidu ya yi kafin ya dawo, tun safe ya yi waya ya taso amma. Bai iso ba sai gab da za a yi sallar Magriba. Yana isowa sashin Umma ya fara zuwa dama kuma dukkan su al’adar Su kenan duk inda suka je suka dawo. to wurin Umma za su fara zuwa, su gaishe ta kafin su je su gaida sauran matan gidan.
Ina ganin shi na yi tsalle na karbi jakar da ke hannun shi. Ina ta tsalle kamar wata ‘yar karamar yarinya, Umma ta ce, “Kai ke kam Adawiyya Allah ya shirye ki har yanzu ba ki daina yi wa Junaidu irin wannan oyoyon ba?” Yaya Junaidu ya yi murmushi ya zauna a kasa a gabanta suna gaisawa tana tambayar shi labarin hanya yana gaya mata ai wurin da nisa.
Umma suka dan yi hira da ya tashi za1 fita sai ya ce mini ina fata kin tanadar mini abin da zan ci don tun sauran bread din ki da na ci da safe ban sake cin komai ba.
Na ce,”Na yi maka girki, amma ina ganin ba za su hanaka cin abincin gida ba. Anti Basira ce ta yi girkin na kuma ji Umma ta ce ya yi dadi, don ta kawo mata.”
“Ke ba ki ci ba kenan?” Na ce, “Eh, saboda ban sha ruwa ba tukunna na yi azumi.”
Ya ce,”To bari in je in gaida su Umma kafin a yi kiran sallah ni in yi sallah in yi wanka, ke kuma kin sha ruwa sa1 ki kawo mini dakin mu.”
Na ce mishi to.
Sai da na gama shan ruwa, sannan na dauki abin da na shirya mishi na je na kai mishi shi da Yaya Almu na samu a cikin dakin na su suna hirar tafiyar tashi. Na je na durkusa na gaida Yaya Almu kafin na sake yi mishi sannu da zuwa na ajiye mishi kwanukan da na zo mi shi da su a gaban shi na kuma bude mishi, ya zuba ido yana kallo cikin murnmushi; Adawiyya ba zan ci girkin nan na ki ba.
Sai kin gaya mini sunan shi da yadda kika yi kika yi shi”
Na kalle shi na yi murmushi na ce, “Ai kuwa don na matsu da ka ci ne kawai zai sani yin hakan ka ga wannan salad ne, amma kaza wato Chicken Salad, wannan kuwa.”
Na kara karkata mishi kwanon don ya gani da kyau na ce mishi, “Salmon pie sunan shi, bari in lissafa maka abubuwan da na yi amfani da su kafin in gaya maka yadda na’ yi.”
Shi kam Yaya Aimu bai jira bayanin da zan yin ba ya mika hannu ya dauki Salmon pie din guda daya, sai da na gyara zama sosai na fara lissafawa Yaya Junaidu kayayyakin amfanin.
Na ce, Bari mu fara da Salmon pie, na yi amfani da kwababbiyar fulawa da na cakuda ta da butter, gishiri, pakin powder, sai shinkafa, albasa, cream, kafin gwangwani, dafaffen kwai, butter da na dafa shinkafa na tsameta na tsantsame sai na yanyanka albasa na soya shi cikin butter, sannan na zuba shinkafar da kifin tare da cream na gauraya su da kyau, na rinka yanko kwababbiyar fulawar nan ina amfani da board wajen murzata tana yin fadi. Sai na rinka debo hadin shinkafa da kifin nan ina zubawa a tsakiya ina rufewa da rabin barin fulawar bayan na zuba yankakken kwai a kan shinkafar in ya ruhu da kyau sai in sa wuka in yanke sama da kasa, don ya zamo a bude kamar haka.”
Na daukoo guda daya ina nuna mishi, don ya gane sosai. “Don ya rinka fitar da tururi daga nan sai na salka a oven ya gasu na kusan mintoci ashirin, shi kuwa chiken salad ga abubuwan da aka yi amfani da su:
Dafaffiyar kaza,
kwai dafaffe
Mai, cokali biyu.
Atile
Mayonniase.
Tafarnuwa
Dakakken 6awon lemon tsami,
yaji.
Ina shirin fara gayawa Yaya Junaidu yadda na yi na shirya mishi chicken salad din sai kawai wayata ta yi kara in dauka sai na ji muryar Julde yana tambayata.
“Ina kika shiga ne? Gani nan a falon Umma ina jiranki.”
Na kashe wayar na kalli Yaya Junaidu cikin murmushi na ce mishi, “Kawai Yaya Junaidu tun da ka ce sai na yi maka bayanin yadda na yi za ka ci, to ka ci salmon pie din kawai, tun da shi na yi maka bayanin komai, barwa Yaya Almu kawai ya cinye chicken salad din. Ni na yi bako Julde ya zo wurina zan je mu sha hira.”
Ina fadin haka na fice dakin da gudu na nufi sashin Umma, don ganin Julde.
Julde dan aminin Baba ne da suka taso tare suka kuma matukar son juna, har suka zama kamar yan’uwa saboda dadewar abotar su Baba Wulle.
Ina shiga falon Umma na same shi a zaune ya sha kwalliyar Kananan kaya dama kuma ma’aboCin sanya su ne sai kamshi yake yi, yana ganina ya saki wani lallausan murmushi ya ce, Ban gajiya na zo miki.”
Na yi maza na yi wura-wura da ido don ganin ko Umma tana kusa ta ji abin da ya fada, da na ga an yi dace ba ta nan sai na fada mishi a hankali.
“Kai Umma fa ba ta san na je ba.”
Gaba daya ya bude baki da idanuwa nuna alamar mamaki.
To ya ya aka yi haka?”
Na dan yi murmushi na ce mishi, “Kai dai ka shown kawai.”
Ya yi murmushi ya ce, “To na yi.”
Na je na kawo mishi abin sha na kuma zauna muna hira, har sai wajen goman dare, sannan ya tafi, saboda ya san iyakacin hirar da bako ke yi a gidan mu kenan in dai ba kwana zai yi ba, don goma tana yi ake rufe get din gidan mu, in an rufe kuma ba a budewa. Wannan umarmin Baba ne.
Sati guda da faruwar haka mun fita unguwa ni da Yaya Almu cikin sabuwar motar shi, Kwalliya sosai na yi na kuma yi matukar yin kyau, sai ma da Umma ta yi ta rokona sannan na yarda na yane kaina da dan siririn gyale, don kuwa kwalliyar kananan kaya na yi muna tafiya cikin motar ina sauraron wakar da Yaya Almu ya sanya a cikin motar mai matukar dadi ta Whitney Auston ce mai taken ‘l am saving all my love for you.
Yaya Almu ya dan waiwayo ya kallen ya ja tsaki mai karfi tare da galla mini harara ya ce, “In wani ya ga yadda kike kada wannan sai ya yi zaton wani rawar arziki kika iya, nan kuwa ba ki iya komai ba.”
Cikin sauri tamkar na mance da wanda nake magana na ce mishi, “Allah ya sauwaka ai ni cuwa na rantse ba daga nan ba, lalle ma baka sani ba Yaya Almu ai ni duk wanda ya sanni ya san ni gwansce wajen iya rawa in ba ka sani ba ma ni lokacin da nake S.S.3 har Queen kawayena suke kirana. “
Na sake kallon shi na ce, “Tabdijam ashe dai ba ka sanni ba, aiko kwana biyar da suka wuce na faki idon Umma tana barci na fita na je gidansu Asabe Aliyu tana partin cika shekarunta a can muka gamu da Julde har muka yi rawa tare da shi, shi ne ma ya biyo ni wai ya yi mamakina har yana yi mini rantsuwar ai duk ‘yan matan da ke wurin babu wacce ta kai ni iya rawa.”
Shirun da na ji Yaya Almu ya yi ne mai tsawo ya barni ina ta zuba yasa na juyo don in ga abin da ya ke yi. Yanayin da na gani a tare da shi kuma sai ya kara fahimtar da ni cewar ba karamin sabutar baki na yi ba naa bashi wannan labarin.
Tsoro ya yi matukar kama ni, har na rinka tunanin
lalle ni kam ina jin ungozman da ta yi bikina ba ta gasa mini baki ba da kyau.
Jimawa kadan sai na ji ya ce, ‘Ai ni ma na yarda ban sanki ba Rabi, amma yanzu zan soma neman sanin naki, wato har party kike zuwa da daddare, Umma ba ta sani ba?
Shi Baba maigadi fa yana ina?”
Jikina ya dauki rawa na ce mishi, ‘Ai sau daya ne kafin nan ban taba zuwa ba.”
Ya ce, ‘Wannan shi ne karya.” Ya juya kan motar ya fasa inda ya ce za mu je ya juyo damu gida kai tsaye dakin shi ya wuce da ni.
“Ta ina kika fita kika bar gidan nan ko kuwa Baba Maigadi ne ya bude miki?”
Na yi maza na ce mishi, ‘A’a.” Cikin rawar jiki da rawar murya na ce mishi, Ta can baya ne wurin raguna akwai wata wayar da ta balle tanan na bi”
Yaya Almu ya kara zuba mini ido fuskar shi dauke da alamar mamaki ya sake cewa, “Na kara yarda dai ban sanki ba, to da kika dawo sai kika cewa Umma me?.
Jikina ya dauki rawa sosai na shiga yi mishi kuka ina ba shi hakuri, ya ce, “Ai sai kin gaya mini in kuma kika yi mini karya zan yi bincike in na gano za ki gane kuskurenki.”
Muryata tana rawa na ce mishi, “Cewa Umma na yi da kai muka tafi don in ba haka ba za ta yi wa duk wanda nan kira mata sunan shi magana.”
Ya yi shiru ya buga uban tagumi ya zuba mini ido yana kallona, ban da kukan da nake yi kirjina sai dakan uku-uku yake, saboda tsananin tsorata da na yi da irin kallon da yake yi mini gani nake tanfar in ya mike kaina zai nufo.
“Ka yi hakuri Yaya Almu. Ka yi hakuri ka rufa mini asiri kar ka gayawa Baba da Umma za su yi fushi da ni gara ka yi mini koma me za ka yi mini na roke ka kar ka bari su ji su yi fushi da ni, tun da ka ce mini fushin iyaye bala’i ne akan da.”
Ajiyar zuciya mai tsananin karfi ya yi, kafin ya sauke tagumin shi ya ce, ‘Ai ke ba kya tsoro, ba kya gudun bacin rai wa zai taba tsammanin za ki 1ya yin wannan abin da kika yi? “
A hankali ya bude baki ya ce, “Ko a mafarki an taba zaton za ki iya yin hakan ba, amma je ki zan yi tunanin abin da ya dace in yi a kan ki.”
Har kusan kwana bakwai ina sauraron hukuncin da Yaya Almu zai yi mini.
A duk lokacin da na gan shi da Umma sun kebe kuwa gabana ya rinka faduwa kenan, sai in rinka ganin kamar abin da ya zo ya gaya mata kenan.
Gabadaya hankalina baya tare da ni, kowanne lokaci cikin zullumi da tunani nake na me zai yi mini?
Ko me zai faru?
Rannan dai da safe sai aka wayi gari ana kara tsawon katangar gidan mu, ashe dama tun washegarin wannan maganar ya sa aka soma aikin ginne can bayan dáma kuma shi ne bangaren da aka yi amfani da waya wajen tsare shi aka kara gini, sannan aka zagaye saman katangar da murdaddiyar wayar nan ta tsaro mai dauke da wutar lantarki.
Ban samu dan kwanciyar hankali a jikina ba har sai da na ga Baba ya zo gida ya yi kwana biyu ya tafi ban ji an ce mini komai ba, haka nan Umma sai na gane dai Yaya Almu ya ji rokon da na yi mishi na kar ya hada ni da su.
Julde kuwa tun daga wannan lokacin ban san dalili ba, ko waya na yi mishi baya dauka in kuwa a wani wuri muka hadu to yana ganina zai yi maza ya bar wurin.
Ana cikin haka ne yaya Almu ya samar mini Federal Poly garin mu na soma zuwa har ga shi na shekara guda har da wasu ‘yan watanni a cikin ta tun da ga shi an turo ni nan hukumar zabe ina zaman koyon sanin makamar aiki.
Tun da na fara zuwa dai Yaya Almu ne mai dawainiyar kai ni da dauko ni, saboda ku san kullum a makare nake zuwa su Yaya Junaidu ba sa iya jirana, saboda su dukkansu ma’aikatan gwamnati ne, shi kuwa Yaya Almu Lawyer ne mai zaman kan shi, in ba yana da zama a kotu ba uzurin gaban shi kawai yake yi, tun da harkokin kasuwancin shi ma yake yi, tsakanin Nijeriya, da kasar China.
Ina zaune kan kujerata da ke Daura da ta yallabai a offishin hukumar zabe ‘yan takardun da aka nuna mini yadda zan rinka cikewa nake ta faman kokarin yin hakan cikin tsaiko don na san yallabai yana ganin na gama cike su zai sake miko mini wadansu.
Ran Hajiya Rabi’atu ya dade gabana ya yanke ya fadi jin iin kiran da yallabai ya yi mini don dai na san kwanan zancen a duk lokacin da ya yi mini irin wannan kiran na dan zuba mishi ido cikin suararo da nuna girmamawa ya dan sha mur kadan a dalilin ya fara gajiya da murmushin da yake yi mini, a duk lokacin da zai mini irin wannan maganar.
“Ina fata dai yau ba za ki sake kawo mini wani uzuri akan ‘yar rakiyar da nake cewa ki yi mini ba?”
Na zuba mishi ido cikin nutsuwa na ce mishi, To bari tun da ka matsa a kan hakan in Yayana ya zo sai in nemi izini wurin shi.”
Da sauri yallabai ya fara cewa, Kai ashha! Ashsha!!” Sannan na ja wani irin mummunan tsaki kafin ya fara cewa, ‘Ke kam ina jin ke ce ‘yar farin gidan ku? Gaba daya saboda wautarki ta yi gaban kwatance.”
Na ce.mishi, ‘A’a ba ni ce ‘yar farin Babanmu ba.”
Ya ce, “Eh ai na yarda da abin da kika gaya mini na cewar shi wannan miskilin mutumin mai muzuran tsiya wanki ne, don sai da na je na yi bincike kan hakan aka tabbatar mini, saboda ko kadan dabi’unshi ba na wan na kusa ba ne, yafi kama da saurayi mai matukar kishi akan budurwarshi, shi ne za ki je kina gaya mishi wannan maganar ta shiri da za ta kasance tsakanin ni da ke kawai
Ko kin san tun da yake zuwa wurin nan bai taba amsa gaisuwar da nake yi mishi ba?
Ni kuwa ina yi mishi gaisuwar ne kawar darajar an tabbatar mini ubanku daya, amma inda don ta bayanin da kika yi mini ne ba yarda zan yi ba, sai in dauka kawai irin wayon ku na yan mata za ki yi mini.”