Rayuwata ta fara ne a wata safiya mai cike da abin alajabi, rana ce da bazan taba mantawa da ita ba. Na bude idanuwa na ne kawai na ganni a wani daki a kwance kan wani gado na karfe. Firgigit na mike cikin tsoro, a zuciyata ina fadin, "Ina ne kuma nan?"
Zuwa wani dan lokaci sai ga wata mata ta shigo dakin dauke da wani dan faranti da wasu yan karafuna kanana a kai ganina da tayi a zaune yasa ta ajiye farantin ta juya da gudu tana fadin yafarka nikuwa tuni tsoro ya kara lullubeni nakoma daga can. . .
Dakyau. Lallai wannan labari da alama zai bada citta. Allah ya sa an fara a sa’a. #haimanraees
Ameen summa ameen oga Ina godiya
Gaskia wannan labarin da alama zai yi dadi.
Allah kara basira!
Ameen thumma Ameen
Ina godiya