HASSADA
Mai hassada ya wahala,
Wanna ya faɗa juhala,
Ya yi wa kansa talala,
Da igiya yawan malala.
Da ma ka gane ka daina,
Kafin wataran ka ganka rana,
Ana yi ma ature da ƙuna,
Kai ko kana ta ƙara.
Yo in banda ba wa kai aiki,
Me zai kai ka neman ilimi ga jaki,
Ina fa za a gama makaho da tuƙi,
Balle a haɗa shi yin faɗa da zaki?
Magana ce dai nake ka duba,
Kafin ka fara nuna gaba,
Ka cire hassada a gaba,
Ka kama Manzona da Rabba.
In kuwa ka ƙiya to ka sani,
Kai tamkar mace ce ba zani,
Ka ga ko cikin ‘yan zamani,
Ita ake gudu kamar zarni.
Allah mu dai ka tsare mu,
Faɗawa sharri a junanmu,
Hassada, gulma Ka tsare mu,
Daga mu har zuwa iyalanmu.
Allah mun tuba Ka shirye mu,
Kafin mutuwa Ka ganar da mu,
Laifinmu duka Ka yafe mu,
A aljanna Ka haɗa mu da Manzonmu.