Skip to content
Part 15 of 18 in the Series Warwara by Haiman Raees

FUSHI

Yayin da zuciya ta fusata,

Hankali tabbas zai ɗimauta,

Kai da za a haɗe da magauta,

Lallai kuwa da za’a fafata.

Jini ke tafasa har fata,

In an yi nishi a ƙuta,

Da a ce tsautsayi zai gifta,

Haƙiƙa dole ne za a kafta.

Jama’a duk mu hankalta,

Mu rage fushi da fusata,

Kar mu zamo masu wauta,

Haƙuri, ribarsa mu rabauta.

Fushi matsala tai yawa gareta,

Ga shi ba shi barin zuciya ta huta,

Shi ko bai kwaɓar baki kar ya furta,

Zancen da zai sa a husata.

Da na saninsa ya ko gawurta,

Bayan duk ka ƙare mita,

Ɓaɓatu da zagi da wauta,

Sai ka ji ina ma ƙasa ta tsage ka bi ta.

Kai idan fushi ya nufo ka,

Kai maza kama gabanka,

Ko ma ka arce abinka,

Domin ko hakan ya fi maka.

Don shi fushi musiba ne,

Sannan fushi bala’i ne,

Kai fushi fa jarrabawa ne,

Sannan abin gudu ne.

<< Warwara 14Warwara 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.