Ke Ce Ta Daya
Na zamo ɗan biri,
A fagen soyayya
Bishiyar so na hau,
Har ina juyawa.
Bani jin ko jiri,
Sai ka ce jariri,
Gani a sarari,
Amma bani nan a zahiri.
Na zamo hankaka,
‘Yar wani zan ɗauka.
Kan sonta nai hauka,
Ga zuciya na kuka,
Ke ce ta ɗaya a komai,
Ke ce ta ɗaya a komai.
Ke ce nake so tabbas,
Ke ce nake da tabbas.
Ke ce kika ce min ass!,
Amma na kasa kataɓus.
Don ke ce ta ɗaya a komai.
Ke ce ta ɗaya a komai.
Ke ce muradin ruhi,
Ke ce buƙatar ruhi.
Ke ce tunanin ƙalbi,
Ke ce a kullum zan bi
Ke kin ka zamto komai,
Ke ce ta ɗaya a komai.
Ke ce na ba wa sirri,
Ke ce nake ta buri.
Akan ki nake ta kuri,
Har anai mini kirari.
Don ke ce ta ɗaya a komai,
Ke ce ta ɗaya a komai.
Zuciya har jini,
Ke ce a gare ni.
Ki kasance da ni,
Kar ki guje ni.
Zan iya rabuwa da kowa,
Zan iya rabuwa da komai.
Domin na baki komai,
Saboda ke ce ta ɗaya a komai.
Kayi kokari
Na gode sosai.
#haimanraees