KEWA
Ina ta kewar sahiba,
Zuciya ta gaza samun nutsuwa.
Ina ne kika shiga?
Taimaka ki yi ado ga idanuwa.
Muryar nan taki,
Taimaka ki azurta kunnuwa.
Ke ce jini da jijiya,
Matallafin duka rayuwa.
Kar ki ɓoye mini,
Taimaka ki tallafi rayuwa.
Shi masoyi ki duba,
Laifinsa ba shi ƙirguwa.
Sai dai amma,
Bai da girman da zai ƙi yafuwa.
Domin ita ƙauna,
Haskenta ya game duhuwa.
Kuma kimarta ki duba,
Ya wuce komai a rayuwa.
In laifi ne da na yi,
Daure ki yi min afuwa.
A wurina dai,
Ke ce zan kira da bultuwa.
Sauran ‘yan mata kam,
A wurina su ne shamuwa.
A cikin zuciya,
Gare ni ke ce sabuwa.
Ina fatan ko a gaba,
Ki zamo ke ce tsohuwa.
Tsohuwar zuma,
Mai maganin dukkan damuwa.
Na gaza barci,
Idanuwana sun gaza rufuwa.
Kamar ɗan yaro,
Da ya gaza barci a idon uwa.
Hawayena zuba suke,
Tamkar ana ruwa.
Begenki a rai bebi,
Kullum yana ta ƙaruwa.
Daure mu haɗu,
Ko ruhina zai samu nutsuwa.
Ni da ke sahiba,
Za mu je hutawa.
A lambun so,
Za mu je shaƙatawa.
Mu yi hirar so,
Da ƙauna da walawa.
Muna nishaɗi,
A junanmu har da darawa.
Muna tare da juna,
Mutuwa ce kaɗai mai rabawa.