Yunwa
Da sunan Allah gwanin mulki,
Allahu mai iko a kan sarki,
Tsira da aminci ga mai tsarki,
Muhammadu wanda bai raki,
Allahu Ka lamunci wannan aiki.
Domin nema a kan yi aiki,
Abun ne dai babu sauƙi,
Ba tajiri balle musaki,
Talakka ne ko ko saraki,
In ciki ya murɗa, to da walaki.
Wani ka ga duk ya yi laushi,
Kamar rana ta bugi lawashi,
Balle alayyaho da karkashi,
Da rana ta yi bugu su yi laushi,
Haka za ka ga ƙato yai tafshi.
Idan ɗiyan hanji suka ɗau bayani,
Za ka fara biɗar su dashishi,
Ko kuma tuwo miyar agushi,
In ka fara awon gaba da shi,
Ba a jin ko da labarin shi.
Yunwa sam ba ta da hankali,
Kuma sai ta koyar da hankali,
Ita babu ruwanta da jahili,
Balle tukaru mai jangali,
Sarki, mugu ko kuma adali.
Ina liman mai tarin ilimi,
Kai yanzu dai dubi bijimi,
Wa ne kai ka nu nai ƙarfi,
Sai dai tuni ta kayar da shi,
Kai wannan aikin na yi ne.
Wani loton in yunwa ta bugo,
Ko da kana kwance cikin bargo,
Aradu da hanzari za ka rugo,
Cikin kitchen za ka antayo,
Sauƙi ka je maza ka nemo.
Allah ka raba mu da yunwa,
Yunwar nan dai ‘yar tabahuwa,
Wacce bata son komai sai dahuwa,
Da abokin nan nata wato ruwa,
Su ne mahaɗin dukkan rayuwa.