Wakar Pathaan
Kudu da Arewa duk ku zo,
Gabas da Yamma sun zo,
Murna ake yi bisa ƙwazo,
Don malmala ta wuce ƙanzo.
*****
Sarkin nan dai ya fito,
Ya wuce harkar 'yan hoto,
Ya zama gwarzo mai ƙoto,
Kambun nasara ya ƙwato,
Ya bar wasu can na yin toto.
*****
Kyankyaso babban ƙwaro,
Yau Pathaan ya fasa taro,
Giwa iyayen Toro,
Tabbas ko ba ki da tsoro,
Ka ba 'yan maza horo.
*****
Jummai gantali ma ta bi,
Wa ke zancen 'yan kinibibi,
KRK ɗan ƙota ma ya bi,
Wa ke batun 'yan Bjp,
Pathaan dai. . .