Ban Damu Ba
In na sa abu a gaba,
Matuƙar bai muni ba,
Ba zan taɓa bari ba,
Ko da gezau ba zan ba,
Ba kuma zan damu ba.
2.
Tsarina kenan ba na wani ba,
Ko da zan rasa yanzu ko gaba,
Matuƙar dai zaɓina ne haba,
Me zai hana ba zan jure ba?
Duk wuya ba zan damu ba.
3.
In so bai yi kisa ba,
Haƙuri bai gushe ba,
Muradi bai ragu ba,
Bege bai ragu ba,
To ba zan damu ba.
4.
Matuƙar dai alƙawari na nan,
Kan dai har amana na nan,
Ko da kowa baya nan,
Zan kasance a nan,
Ba kuma zan damu ba.
5.
Ko da ace ba a so,
In dai ni ina so,
Kowa ma kar ya so,
Zance ne na so,
Don haka ban damu ba.