Warwara
Ga tufka ga warwara,
Mai hassada ke yin kyara,
Maji tsoro shi ke ƙara,
Mai tsafta shi ke yin shara,
Kowa ya yi kuka ya ɓara.
Bugu da bugu sai dai jarmai,
Kyan dambu ace ya ji mai,
Sai an ji daɗi ake maimai,
Wurin wuya ko ujmaimai,
Haƙuri na aiki ga komai.
Tunƙwal-tunƙwal uwar daka,
Yau furar gero ake ta daka,
Ita hakima tana ɗaka,
In an jima ta ɗan leƙa,
Tana lasar miyau tun a ɗaka.
Ya kamata a warware tufka,
In ya so sai a gyara saƙa,
Yadin nan na mamar a ɗinka,
Ko sosa ce sai a ɗinka,
In ka fito aka ganka,
Ka wuce dai a zage ka.
Na yo zance a birkice,
Bisa nazari da bincike,
Ramukan sai ku ciccike,
Ko a nemo ci-wake,
In za a je a hau keke.
Basamude narkeke,
Gashi nan ɓarkeke,
Shiga kamar basarake,
Ku ce baki ya wanke,
Kafin ice sai marke.