Makiyana
Allah Kai ne Ka yi kowa,
Da sunanKa zan farawa,
Albarkacin shugaban kowa,
Annabi Jagoran Annabawa.
*****
Allah Kai ke da kowa,
Kai min ni’ima ina godewa,
Kamar yadda Ka yi wa kowa,
Ka tsare autan Hauwa.
*****
Tun fari dai da farawa,
Ka duba cikin Larabawa,
Ko su cikin Yahudawa,
Ko kuma cikinmu Hausawa.
*****
Babu tantama a Yarbawa,
Kai har da su Jamusawa,
Duba cikin Amurkawa,
Maƙiya kamar saukar tsawa.
*****
Ko me ka ke yi Malam,
Magana ka ke yi ko gwalam,
Noma ka ke yi ko kwaram,
Maƙiya ba za ka rasa ba.
*****
Nima akwai su a gabana,
Na baro wasu a bayana,
Ga wasu nan a dama na,
Ga wasu kuma a hagu na.
*****
Rayuwar kenan ba ba ƙari,
Jira suke yi na yo tari,
Yanzu-yanzu su yo ƙari,
Su je su ce n kashe ƙwari.
*****
Komai na yi ban burge ba,
Alherin ba za su gani ba,
Kuskure ba za su ƙi gani ba,
Sharri ba za su ji nauyi ba.
*****
Allahu Kai je jigona,
Sannan kuma Kai ne gata na,
Kare ni da ahalina,
Daga sharrin duk maƙiyana.
This was beautiful Admin. Thank you for your reflections.
You are welcome.