Tufka
Da an yi tufka sai warwara,
‘Yan mata ke suyar awara,
Wasu suna sana’ar gambara,
Ga wasu na ta tsari ba kara,
A gama lafiya dai kura.
Sannu da hutawa zomanya,
Ke ce mai tare kan hanya,
Ki zabgi mutum da miyar tsanya,
Ke ce kaɗai ke bugun Sarauniya,
Kuma ki zam kwana lafiya.
Naira ke ce kakar kowa,
Naira ke ce uwar kowa,
Kina cikin zuciyar kowa,
Ke ce cikin tunanin kowa,
Kuma kin fi raini wurin ɗan kowa.
Saboda kuɗi yau ake shan fama,
Wasu na ɗinki, wasu ko noma,
Wasu na tuƙi, wasu ko jima,
Wasu na can yaƙi a fagen fama,
Naira dai ake biɗa dama.
Naira ta zamo bala’i,
Naira ta zamo masifa,
Naira ta zamo kaba’ir,
Naira ta zamo abar farauta,
A faɗin dajin duniya.
Allahu ka ba mu naira,
Mai amfani Rabbana,
Sannan ta halali bai ɗaya,
Mu zamo a wadace gaba ɗaya,
Har ma mu taimaki ‘yan uwa.