Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, Mammallakin duk wata halitta dake doron ƙasa mammallakin wuta da aljanna mammallakin al'arshi, Allah ina miƙo godiyata a gareka daka ƙara bani dama cikin rai da ƙoshin lafiya na fara rubuta wannan littafin Allah ina roƙonƙa yadda na fara lafiya kasanya na gamashi lafiya kakuma_ _bani ikon isar da saƙon da nake son isarwa na cikin wannan littafin, Allah ka bani ikon rubuta daidai akasin haka kuma Allah ka hani hannuna da rubuta shi, Allah ka sanya na rubuta abun da al'umma zasu amfana dashi Ameen. . .