Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Wata Kaddara by Shamsiyya Manga

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, Mammallakin duk wata halitta dake doron ƙasa mammallakin wuta da aljanna mammallakin al’arshi, Allah ina miƙo godiyata a gareka daka ƙara bani dama cikin rai da ƙoshin lafiya na fara rubuta wannan littafin Allah ina roƙonƙa yadda na fara lafiya kasanya na gamashi lafiya kakuma_ _bani ikon isar da saƙon da nake son isarwa na cikin wannan littafin, Allah ka bani ikon rubuta daidai akasin haka kuma Allah ka hani hannuna da rubuta shi, Allah ka sanya na rubuta abun da al’umma zasu amfana dashi Ameen ya hayyu ya qayyum.

Tsokaci

Wannan labarin ƙirƙirrarran labari ne banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba idan yaci karo da labarin rayuwar ki/ka ayi haƙuri a rashi ne.

*****

A lokuta da dama ƙaddara tana zuwar mana ba tare da mun shirya mata ba, na kasance ni mutum ne a rayuwata mai taka tsantsan sannan ni mutum ne da babu abun da na tsana a rayuwata kamar rashin tarbiyya, Tun da nafara girma nasan menene fari da baƙi,nasan ciwon kaina naji a rayuwata bazan taɓa iya auren macen da bata da tarbiyya ba,daga cikin abun da na tsana a rayuwata akwai SATA,na tsani SATA na tsani mai aikatata, Sai dai kuma kash! duk yadda nakai ga tsanartata hakan bai hanani cin karo da WATA ƘADDARA ba wadda ta sanya na auri ƴar gidan SATA ma’ana ita yarinyace da ta ginu akan SATA domin kuwa babu wanda bai san mahaifinta ba indai shahara ne a fannin SATA sannan itama yarinyar ta gado halin SATAR. Sai dai kuma abun da zai baka mamaki shine bansan wa na aura ba bankuma san ƴar wa na aura ba, duk kuwa da yadda ahalin ta sukayi shuhura ko nace ƙwarin suna a wajen SATA.

Tofah! Tirƙashi yaya Kennan zata kasance idan har ya buɗi ido ya gane da wadda yake rayuwa? Shin zai cigaba da zama da ita ko kuwa zai sawwaƙƙe mata dan gudun kar ta haifa mishi ƴaƴa su gaji halinta? Shin zai fahimci ainihin wacece ita ko kuwa bazai fahimta ba? To wai yama akayi ya aureta ba tare da yasan wacece ita ba, ba tare da yasan ainahin halin ta ba?

*****

Dare ne mai cike da duhu saboda tsabar duhun daren ko tafin hannu mutum baya iya gani kasancewar babu hasken farin wata, garin gaba ɗaya yayi shiru bakajin motsin komai sai irin kukan tsuntsaye da ƙwaruna haka, kasancewar ko wane mahaluƙi a wannan lokacin yana kwance domin bacci, kunsan ance dare mahutar bawa, wasu kuma sun duƙufa wajen kai kukan su ga mahallicinmu,wasu kuma waɗanda babu tsoron Allah a cikin zukatansu wannan lokacin shi ya zame musu lokacin da zasu fita domin aiwatar da munanan ƙudirinsu.

Haka ta kasance a ɗaya daga cikin unguwowin da suke cikin garin na TARABA STATE, a ƙaramar hukumar JALINGO, yanayin unguwar kaɗai zaka kalla ya tabbatar maka da cewa unguwar masu hannu da shuni ce, wasu matane suka shigo cikin unguwar su huɗune duk fuskokin su a rufe da baƙin face mask wanda idan za’a aikata mummunan aiki ake sawa watau aikin rashin gaskiya, wani gida na gani mai masifar kyau zamu iya sanya gidan a cikin jeran gidaje uku da suka fi kowane gida kyau da tsaruwa a cikin unguwar duk kuwa da kasancewar sauran gidajen unguwar suma masu kyaune,hasken wutane ya haske gabaɗaya illahirin ciki da wajen gidan,direct naga waɗannan matan sun nufa wannan gidan ba tare da tsoro ko wani shakku ba duba agogon hannuna nayi ganin ƙarfe biyu daidai na dare (2:00am), tsoro ne ya ɗarsu a zuciyata ganin ba tare da tsoro ba sun nufi wannan gidan kai tsaye,abun mamaki da kuma abun da ya ƙara sanyani a cikin tsoro bai wuce ganin su da nayi sun shiga cikin wannan gidan ba tare da sun buɗe ƙofar gate ɗin gidan ba sai gani nayi sun ratsa ta tsakanin shi sun wuce kamar walƙiya,falon gidan suka nufa inda suka tarar da wata mata a tsaye a falon alamun tasan da zuwan su.

Wata jaka naga ta miƙo musu wadda bansan ko meye a cikinta ba,karɓar jakar sukayi sannan suka juya suka fice a cikin gidan ta inda suka biyo tanan suka koma.

Ƙarfe 7:00am ya tashi daga kan gadon shi tare da yin miƙa, saida ya shiga toilet ya haɗa ruwan wanka sannan yayi brush,fitowa yayi daga cikin toilet ɗin yana goge ruwan jikinshi,matashine wanda a ƙalla bazai fi shekaru talatin ba haka ko talatin da biyu, kyakkyawane ajin farko,farine tass kamar ka latsa jikin shi jini ya fita,yaro mai ji da kuɗi kennan watau MUBARAK YUSUF MAI KUƊI shine asalin sunanshi,abokinshi kuma suna ƙiranshi da YOUNG BILLONIAR.

Direct wajen wardrobe ɗin da take jikin bangon ɗakin naga ya nufa bayan ya gama goge ruwan jikinshin,buɗe wardrobe ɗin yayi da niyyar ɗaukar wani abu a ciki saidai turus!naga yayi ya tsaya ganin baiga abun da yake nema ba, Cikin sauri ya shiga duba wardrobe ɗin tare da hargitsa duk wani kaya dake cikin wardrobe ɗin amma kuma baiga abun da yake nema ba.

Wasa gaske tun yana ganin abun kamar wasa har ya fara tsorata da lamarin domin kuwa duk wani waje da yasan zai ga abun da ya ajiye ɗin ya duba amma ko kamar abun bai gani ba.

Fita yayi daga cikin ɗakin sannan ya nufi ɗakin matar shi cikin sauri har yana shirin faɗuwa.

Tun daga falo yake ƙwala mata ƙira har ya shiga ɗakin nata,ƙarar buɗe ƙofar tashi shiya farkar da ita daga baccin da take ɗin,miƙa tayi da hamma ko addu’a babu,a hankali ta shiga buɗe idanuwanta waɗanda suke cike da bacci sannan ta sauƙe su a kan mijin nata da yake tsaye a kanta kamar wani soja,saida ta kalle shi sama da ƙasa sannan tayi wata miƙa ta miƙe zaune ta zauna.

Bawan Allah lafiya kuwa irin wannan ƙira da safiyarnnan kamar an aikoka?

Kallon ta yayi cikin jin takaicin halin matar tashi sannan yace

Ina kuwa lafiya RAMLAT , al’amarin gidannan ya daina bani mamaki sai tsoro

Kallon shi take da lumssasshun idanunta waɗanda suke nuni da cewar baccin bai isheta ba sannan tace.

Malam ka fito street forward ka faɗamun meye yake faruwa a gidan banson wata kwanakwana da kakemun.

RAMLAT ya za’a yi ace tun daga ranar auren mu har kama yau da muke ƙoƙarin shiga wata biyar da aurenmu amma ace kullum inadai zan kawo abu gidannan sai na wayi gari babu shi babu alamar shi,tun banason yin magana har an fara kaini maƙura na fara magana.

yanzun mai kuma aka ƙara ɗaukema?”””. Ta faɗa cikin yamutsa fuska da alama maganar bata dameta ba.

Ina agogona da wayata da nazo dasu jiya wanda nacemiki wayar a Farouk na siyowa,shikuma agogon nace miki dubu ɗari biyar na saya,to su na nema na rasa.

Tsaki tayi sannan ta koma ta kwanta.

To yanzu meye abun damuwa akan wannan abun har zaka wani ɗaga hankalinka har kazo ka katse mun baccina abun da ka riga kasan cewar kafi ƙarfin shi duka duka nawa dubu ɗari biyar take kaida kake bada kyautar ire-irenta ba tare da kaji komai ba amma shine har zaka ɗaga hankalinka akan wata waya da agogo wadda nasan wayar ma bazata fi dubu ɗari shida ba,sannan beside all this ma kasan dai gidannan ba ɓarawo ko,sannan babu wanda yake da key ɗin ɗakinka, kawai kaje ka ƙara duba inda ka ajiye kawai may be kayi misplacing wajene””ta faɗa tana ƙoƙarin jan bargo da niyyar komawa baccinta.

Cikin fushi yasa hannu ya fisge bargon sannan ya fara magana

Wai ke RAMLAT wace kalar matace wadda bata damu da damuwar mijinta ba,karki manta fa dubu ɗari biyar ɗin da kike maganar cewar nafi ƙarfinta ai ba’a ƙasa na tsinceta ba saida na fita nayi aiki da gumina kafin nasamu,sannan ni bawai agogon bane damuwata ba a’a wayar Farouk ɗin da bangani ba itace damuwata,yanzu wannan kuɗin wajen one million ake miki magana inda sadakar su na bada bazanji ciwon rasasuba saboda nasan akwai reward, amma nazo a matsayin ki na matata ina faɗamiki damuwata don mu samu hanyar da zamuyi solving problem ɗin amma kina nuna You don’t care about it.

Itama miƙewa tayi cikin fushi sannan ta fara magana cike da tsiwa kamar ba mijinta ba.

MUBARAK which kind of nonsense is this? yaushe muka fara ƴar haka da kai? yaushe muka fara wannan wasan dakai,ko ni kake zargi na ɗaukar ma kayanka ne ka fito ka sanar dani let me know if ma ni kake zargi i want to know, da har ina bacci zaka shigomin ɗaki,sannan har ka samu confidence ɗin sanya hannu ka fisge mun bargo,eh lalle wuyanka ya isa yanka lalle nayi laushi tabbas,ka sani fa wallahi ina ɗagama ƙafa ina maka karane kawai a matsayin ka na mijina amma baka gani ko,to mu zuba nida kai wallahi zan fitoma a ainahin wacece ni zan nunama true colour ɗina,to gidannan dai mu biyune a cikinsa and babu wanda yake da key ɗin ɗakinka balle kayi tunanin wani zai shiga,dalla malam sakarmun bargo bacci nakeji” Ta faɗa tana mai fisge bargon sannan ta koma ta kwanta.

Baiyi mamaki da abun da tayi mishin ba domin kuwa wannan ba sabon abu bane a hallayyar tata kullum abun nata gaba yake maimakon abu yayi sauƙi amma saidai yayi gaba.

Gani yayi tsayuwar babu inda zata kaishi kawai sai ya juya ya nufi ɗakin shi,zama yayi a bakin gado yayi tagumi da duka hannayen shi biyu cikin tausayin kanshi,ya ɗauki tsawon lokaci a zaune kafin ya tashi ya ɗauki key ɗin motar shi ya fice a gidan.

Direct gidansu ya nufa domin idan ta ɓata mishi rai babu a inda yake samun sauƙi sai wajen mahaifiyar shi,a zaune ya tarar da ita a falo,hannunta riƙe da ƙaramin ƙura’ani,kujerar gefenta ya nema ya zauna tare da ɗaga kanshi sama yana kallon silin ɗin ɗakin.

Saida takai ƙarshen aya kafin ta ɗago ta zuba idanunta a kanshi wanda baima san ta nayiba da alama yayi nisa a cikin tunanin da yake,kallon shi takeyi cike da tausayin halin da yake ciki na rashin samun matar kirki da yayi.

“MUBARAK ” Mahaifiyar tashi ta ƙira sunanshi,shiru bai amsa mata alamar baima san tana magana ba, ganin ba zai amsa ɗin bane ya sanyata kai hannunta tare da bubbuga saman kujerar da yake kai ɗin a hankali.

Cikin nutsuwa ya fara sauƙe idanunshi ƙasa har ya juyo gabaɗaya yana fuskantar mahaifiyar tashi.

“RAMLAT ce ko?” Mahaifiyar tashi ta jefa mishi wannan tambayar.

Shiru yayi bai bata amsa ba.

“MUBARAK nidai a kullum abun da zan ƙara faɗamaka shine ka ƙara haƙuri da halin matarka sannan ka ɗauki auren RAMLAT a matsayin ƘADDARAR ka kuma kayi addu’ar Allah ya baka ikon cinye wannan jarrabawar.”

Dogon numfashi MUBARAK ɗin yaja kafin ya kalli mahaifiyar tashi sannan ya fara magana

“Deede nifa a yanzu duk wani halin RAMLAT na daina mamakin shi,sannan wannan tunanin da kikaga inayi bakomai bane ya sanya sai SATA da aka dameni da ita kwana biyunnan,Deede tun ranar da aka ɗaura mana aure da RAMLAT har kawo rana irin ta yau ban isa nayi ajiya a cikin gidana ba na dawo na tarar da abun da na ajiye,sannan ni ba SATAR bace ta dameni a’a idan har za’a tsaya a ɗaukar mun iya kuɗaɗe to wannan da sauƙi amma har wasu abubuwana masu muhimmanci ɗauka ake,kuma abun mamakin shine daga ni sai RAMLAT sai kuma mai gadi da driver muke rayuwa a cikin gidan,nayiwa RAMLAT magana amma maimakon a matsayin ta na matata ta kwantar mun da hankali a’a sai ma wasu maganganu da ta fara waɗanda suka ƙara sanyani a cikin damuwa” “kwashe duk yadda sukayi da RAMLAT ɗin yayi ya sanar mata.

Shiru Deede tayi tana saurarar duk abun da yaron nata yake faɗamata, sosai take tausayawa halin da yake cikin ganin duka duka yaushe ma yayi auren da har za’a ce ya fara going through this problem,saida tagama jin duk bayanin nashi sannan taja gauron numfashi kafin ta fara magana.

“A gaskiya wannan maganar taka abar dubawa ce,domin kuwa lamarin SATA ba ƙaramin abu bane,to amma kai babban matsalar ka shine kai ba’a isa a faɗama laifin RAMLAT ba sai ranka ya ɓaci kuma alhalin kaima kasan tanada matsala,to amma ai naga akwai CCTV camera a gidan naka to meyasa bakaje ka duba ta can ba?”””.

Taɓ to shi ya manta da cewar ya sanya wata aba wai ita CCTV camera a gidan, maganar Deede ɗin ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi ɗin.

“Amma gaskiya kaje ka duba domin kuwa wannan abun da ɗaure kai yake ace ku biyu a gida sannan ka nemi abu ka rasa abun da gaskiya abun dubawa ne,tunda ɗakinka dai daga kai sai matarka kuke shigar shi na tabbata babu ta yadda za’a yi mai gadi ko driver wani a cikinsu yazo ya shiga har cikin ɗakinka ya ɗauki abu ba tare da sanin ɗaya daga cikin ku ba,sannan mai muku aiki ma ba’a gidan take kwana ba asalima yau wata biyu kennan kacemun da tafiyarta ƙauye ko?”

“Hakane Deede amma kuma ni na tabbatar cewa RAMLAT bazata ɗaukar mun abu ba.”

Cewar MUBARAK ɗin yana kallon mahaifiyar tashi.

“To ai kaga matsalar ka ko, nima fa bawai ina nufin cewar RAMLAT ita take ɗaukar maka kayaba kawai dai nacema kaje ka bincika cikin CCTV camera ɗin gidanka.”

“Deede ɗin ta faɗa tare da miƙewa ta nufi sama ɗakinta.

Shiru yayi nawani lokaci kafin can ya miƙe ya nufi hanyar barin falon don zuwa gida ya duba cikin CCTV camera ɗin.

“MUBARAK” Mahaifiyar tashi ta ƙira sunanshi.

Juyowa yayi sannan ya dawo kusa da ita ya zauna.

“Ka manta breakfast ɗinka fa yana kan dining kabari muje muyi breakfast sai ka tafi kaji”” ta faɗa tana mai kama hannunshi suka tashi suka nufi dining area ɗin,daman kullum a gidan yake cin wannan three square meals ɗin,kullum a zaune take safe,rana,dare duk sai yazo gidansu yake ci kamar wanda baida mata,saida suka gama cin abincin saida Deede ɗin ta tabbatar da ya ƙoshi kafin tabarshi ya tashi ya tafi.

Duk wannan abun da yake faruwa tsakanin MUBARAK da Deede ɗin nashi a kan idanun RAMLAT ya faru tana tsaye a cikin falon amma abun mamaki su bama su san da wanzuwarta a cikin falon ba, girgiza tayi tazama ƙuda sannan ta fice a cikin falon ta nufi gidan don zuwa ta goge duk wani abu na cikin CCTV camera ɗin kafin MUBARAK ɗin ya isa, RAMLAT bata tashi bayyana a ko ina ba sai a cikin falon gidan nasu,tsaye tayi a falon tana ƙarewa duk wani abu da yake cikin falon kallo, ɗakunnan da suke jerene a cikin falon guda biyar ta fara bi da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin daga bisani ta tsayar da idanunta akan wanda yake ƙarshe,a hankali ta fara nufar ɗakin har ta isa bakin ƙofar ɗakin handle ɗin ƙofar ta kama sannan ta murɗa ta shiga ciki,tsaye tayi a tsakiyar ɗakin tana ƙaremishi kallo idanunta ne ya fara sanja kalla daga fari zuwa baƙi ga wani hayaƙi da yake fitowa ta ciki,wani gefe daban naga ta nufa a cikin ɗakin inda tana zuwa ta sanya hannunta ɗaya ta tura wata ƴar ƙaramar drower da ba lalle ka fahimci awaita a wajen ba,wata siriyar ƙoface ta bayyana daga bayan drower ɗin ƙofar ta buɗe sannan ta shiga cikin ɗakin babu komai a cikinsa face tarin takardu da alamu ɗakin karatu ne ,bin ɗakin tacigaba dayi da kallo amma idonta bai ganomata abun da take nema,har ta juya da niyyar barin ɗakin sai kawai idonta ya sauƙa a kan wata System a can gefe, nufar wajen System ɗin tayi sannan ta kunnata password ta fara ƙoƙarin sanyawa System ɗin saidai kuma duk wanda ta sa sai ya nunamata invalid,shiru tayi tana nazari kafin ta sa wani aikuwa ya buɗe,nan ta shiga binciken komai na cikin System ɗin har tazo kan video na ranar da waɗannan matan suka zo ta basu wannan jakar,saida tagama kalla sannan tayi murmushi tare da danna format komai nakan System ɗin ya goge saida ta tabbatar da cewar babu wani abu da ya rage a cikin Computer ɗin kafin ta gyara komai ya koma inda yake kamar ba wanda ya shigo ɗakin sannan ta juya tabar cikin ɗakin,harabar gidan ta nufa tare da shiga Mota ta nufi hanyar fita a daidai sannan kuma MUBARAK shima ya ƙaraso ko kallon inda yake batayi ba ta sanya kai ta fice kamar ba mijinta ba,kai kawai ya jijjiga sannan ya nufi parking space ya ajiye motar shi tare da fitowa daga ciki ya nufi cikin gidan.

Manga Ce

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Wata Kaddara 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×