Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Wata Kaddara by Shamsiyya Manga

Bissimillahr Rahmani Rahim

MUBARAK yana shiga cikin gidan direct ɗakin sirrin shi ya nufa inda zaije ya duba cikin CCTV camera ɗin don ganin mai yake faruwa a gidan nashi,yana zuwa ya ɗakko Computer ɗin wata kujera ya janyo ya zauna a kai,buɗe Computer ɗin yayi sannan ya danna password ɗinta ya buɗeta,saidai tun daga farkon kunna Computer ɗin ya fahimci wani abu a game da ita, bincike ya fara yi a cikinta saidai kuma duk inda ya shiga a cikin Computer ɗin sai ya nunamishi empty,mamaki ne tsantsa ya cika shi domin kuwa shidai yasan cewar idan banda mahaifiyar shi babu wanda yasan cewar da wata aba wai ita CCTV camera a gidan dan ko RAMLAT bai sanarwa ba,to mai yake shirin faruwa dashi ne wai,haka yayi ta ƙoƙari duk wani bincike da zaiyi yayi shi amma baiga komai a cikin System ɗin,shiru yayi tare da dafe kanshi da duka hannayen shi,wani zazzafan zazzaɓine yaji ya rufe shi lokaci ɗaya domin abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba tare da ɗaure mishi kai ba,da ƙyar ya iya maida System ɗin inda ya ɗakkota sannan ya miƙe ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin ko ƙofar ɗakin ya kasa janyowa,da ƙyar ya iya jan kanshi ya iso falon gidan.

Zubewa yayi a kan kujera yana jin ƙwaƙwalwar shi kamar kamar zata tarwatse to wannan wana kalar abune haka kamar aikin aljanu,wayar shi ya zaro a aljihun shi da yaji tana ringing ganin sunan Deede ɗin da yayi ya bayyana ɓaroɓaro akan Screen ɗin wayar shi ya bashi damar ɗaukar wayar tare da karata a kunnenshi ba tare da yayi magana,daga ɗayan ɓangaren ne Deede ɗin ta fara magana.

“MUBARAK” ta ƙira sunanshi bayan tayi sallama.

Cikin sanyin murya kamar mai shirin kuka MUBARAK ɗin ya amsa mata.

“Na’am Deede”

“Lafiya kuwa maiyafaru naji muryanka yayi sanyi haka?” Cewar Deede ɗin.

Shiru yayi kamar bazai amsa ba amma kuma bazai iya ɓoyemata damuwar saba.

“Deede nazo gida na duba banga komai a CCTV camera ɗin duk wani abu da yake kai anyi formating” ya faɗa cikin rawar murya.

“Innalillahi wa’innailaihi rajiun bangane anyi formating ba MUBARAK daman akwai wanda yasan da CCTV camera a gidan naka ne?””” Deede ɗin ta faɗa cikin tsananin mamaki.

“Wallahi kuwa Deede nima abun ya matuƙar kullemun kai, kuma ni gaskiya babu wanda yasan na sanya wata CCTV camera a gidan, dan ko RAMLAT ban sanarwa ba.”

“To amma abun gaskiya da mamaki kuma wannan lamarin abun dubawane ya za’a yi haka ta faru na rasama abun da zancemaka wallahi” Deede ɗin ta faɗa tare da sanya hannunta ta dafe goshinta.

“Deede nifa inajin kamar ƙwaƙwalwa ta zatayi bindiga wallahi har wani zazzzaɓine ya rufe ni” Cewar MUBARAK ɗin yana lumshen idanunshi da sukayi masa jawur.

“A’a MUBARAK karka wani ɗaga hankalinka karka sanya damuwa a ranka dan Allah kaji, kabari zamu dage da addu’a zan sanya malamai suyi addu’a sosai akan abun kaima kuma inason ka dage da addu’ar, ni yanzu ga auren SALMAH da ya sakomu a gaba wallahi, amma inshAllah ana gama bikin zamu san matakin ɗauka.” Deede ɗin ta faɗa cikin son ta kwantarwa da ɗan nata hankali, sosai ta shiga masa nasiha basu bar wayar ba saida ta tabbatar da cewa hankalin shi ya kwanta ya zama stable kafin sukayi sallama.

*****

RAMLAT kuwa tana fita a gidan direct gidan su ta nufa a can wata unguwa da ban. Horn tayiwa mai gadi yazo ya buɗe mata gate ɗin,ciki ta shiga da motar inda taje tayi parking ɗinta a parking space,fitowa tayi a motar sannan ta kulleta, cikin gidan ta nufa,tun daga bakin ƙofar falon su ta tabbatar da cewa mahaifinta yanannan sakamakon surutu da taji yana tashi a cikin falon,ƙarasa shiga cikin falon tayi inda ta tarar da mahaifin nata zaune akan kujera ga mutane kuma sun kai goma a zaune a ƙasa da alamar yaranshi ne,sai kuma wani mutum da yake zaune a gefe,yana magana da mahaifin RAMLAT ɗin,waje ta nema ta zauna a can gefe tana sauraron abun da mutumin yake faɗa.

“Alhaji watau kamar yadda na sanar da kai shine nazo wajenkane ka taimakamun a bisa adalci da tausayi irin naka ka agazawa rayuwata badan nakai ba ba kuma dan na isa ba ka tausayamun ka sanya yaranka su maidamin kayana da jiya suka shiga kasuwarmu to tsautsayi yasa wannan abu ya ritsa harda shagona”

Mutumin ya faɗa yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa kamar zai yiwa mahaifin RAMLAT ɗin sujjadda.

Wani murmushi mahaifin RAMLAT ɗin ya sake mai cike da ma’anoni da yawa sannan ya ɗago ya kalli RAMLAT tare da mata hannu alamar tazota.

Tasowa RAMLAT ɗin tayi sannan ta dawo kujerar da mahaifin nata yake zaune ta zauna sannan tace.

“Dad mai yake faruwane? na shigo ma ko gaiswa ba muyi ba” ta faɗa tana kallon mutumin da yake tsugune a gaban mahaifin nata sannan ta kawar da kanta gefe.

“Watau wannan mutumin da kika gani yazo shine akan yana neman alfarma” shiru Alhaji ADAMU ɗin yayi kafin ya ɗago ya kalli RAMLAT ɗin sannan yacigaba da magana.

“Kinsan yanayin aikinmu to abun da ya faru shine daren jiya su DA’U sun shiga babbar kasuwa dan aiwatar da Business to sai Business ɗin nasu ya biya dasu ta shagon wannan bawan Allahn inda suka samomana riba mai yawa a shagon nashi domin ba ƙaramin kaya suka samu a shagon ba,to shine yanzu yazo yana buƙatar a mishi adalci a maida masa da kayanshi”

Ya ƙarashe maganar yana umartar ɗaya daga cikin yaran nashi da su ɗakko kayan da suka sato a daren jiyan a kasuwar.

Kayan suka shiga jidowa daga wani ɗaki suna kawo falon suna zubasu a gaban mahaifin RAMLAT ɗin sun ɗauki tsawon lokaci suna fitowa da kayan har saida na ɗan tsorata ganin irin yawan kayan da suka Sato a kasuwar. Saida suka gama fitowa da kayan kafin Alhaji ADAMUN ya kalli mutumin yace.

“Gaskiya kasuwarku akwai kaya sosai anyama kuwa kuna fitar da Zakka?”

“Alhaji wallahi muna fitarwa sosaima”

Mutumin ya faɗa yana ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa.

RAMLAT ce ta dakatar da mutumin ta hanyar fara magana.

“Dad yanzu ai adalci yace yana buƙatar a masa ko?”

RAMLAT ɗin ta jefawa mahaifin nata wannan tambayar.

“Eh yana buƙatar a masa adalci wai a maida mishi da kayanshi,yanzu ke a shawarar ki ya kika gani a mayar masa kayan nasa ko kuwa a ƙyaleshi kawai?”

Murmushi RAMLAT ɗin ta sake sannan ta dubi mutumin tace.

“Bawan Allah adalci kake so a maka ko?”

Ta jefawa mutumin wannan tambayar.

“Eh ranki ya daɗe a taimaka a duba lamarin””” cewar mutumin yana kallon RAMLAT ɗin.

Shiru RAMLAT ɗin tayi kamar mai nazarin wani abu kafin ta ɗago kai tace.

“To shikennan za’a maka adalci kamar yadda ka buƙata ɗin, amma kuma kasan da cewar anayin Business ne dan a samu riba ko?”

“Eh ranki ya daɗe.”

“Good to yanzu Dad abun da zai faru shine za’a raba wannan kayan nashi kashi uku zamu ɗauki kashi biyu zamu mayar mishi da kashi ɗayan tunda adalci yake buƙata kuma ni a ganina wannan shine adalcin da zamu iya mishi.”

“Shiyasa nake bala’in sonki RAMLAT domin kuwa akwai ki da hangen nesa.”

Cewar mahaifin RAMLAT ɗin yana sakin wata iriyar dariya ba daɗin ji.

Shiru mutumin yayi yana magana a cikin zuciyarshi tare da mamakin baƙin zalunci irin nasu RAMLAT ɗin shida kayanshi amma ƙarfi da yaji an mishi ƙwacen su,wannan wace kalar rayuwace gashi dai ana kallon su suna aikata wannan mummunar ɗabia’a ta Sata ɗin amma kuma hukuma ta kasa ɗaukar mataki a kansu kamar ma wadda hukumar tsoron su take,maganar RAMLAT ɗin ce ta dawo da mutumin daga duniyar tunanin da ya tafi tana cewa.

“Bawan Allah ina fatan hakan ya maka idan kuma bai maka ba ga hanya zaka iya kama gabanka.”

Ta faɗa tana mai zaro cingom a jakarta tare da jefawa a bakinta ta fara taunawa.

“A’a Wallahi ranki ya daɗe hakanma yayi sosai Allah ya saka muku da Alkhairi ya biyaku ya ƙara girma.”

Mutumin ya faɗa yana jin zuciyar shi kamar zata tarwatse saboda baƙin ciki.

Wani murmushin gefen baki RAMLAT ɗin ta sake kafin ta dubi yaran mahaifin nata tace su warewa mutumin kayanshi, aikuwa hakan akayi inda suka shiga ware kayan kamar daman sun san iya adadin kayan da suka ɗakko a shagon nashi,saida suka gama ware duk kayan mutumin kafin aka shiga rabashi kamar yadda RAMLAT ɗin ta faɗa haka aka raba kayan kashi uku inda aka ware kashi ɗaya aka bawa mutumin su kuma su RAMLAT da mahaifinta suka ɗauki kashi biyu.

*****

“Gudu gudu sauri sauri take shirin nata bata son Umman ta ta ƙara mata ƙira na biyu, aikuwa ta ɗauki hijab kennan zata sanya taji Umman ta ƙwala mata ƙira,da gudu ta fita daga cikin ɗakin har tana shirin faɗuwa uniform ne a jikin ta riga da wando Maroon colour sai hijab fari tas,ɗankwalin uniform ɗinne a hannunta kanta kuma anmata kitson kalaba wanda ya bayyana ainahin yawan gashinta domin kuwa har ya saƙƙo ƙasan kafaɗunta, kyakkyawa ce ajin farko saidai ba fara bace amma kuma tafi wasu fararen da yawa kyau domin kuwa kana mata kallon farko zaka tabbatar da zallar kyawun da Allah ya mata,ƙarasa fitowa tayi daga cikin ɗakinta inda ta tsinkayi Muryar Umman tana cewa.

“Ai wallahi ABDUL kai kake ƙara sangartar da SALMA, amma ace yarinya kullum tana girma tana ƙara shiga daji,kullum a gidannan in zaka kaita islamiyya sai ta ɓatama lokaci, kaikuma kamar dole sai ka kaita”

Umman ta faɗa tana watsawa SALMAN wani mugun kallo.

Baki SALMAN ta turo gaba tana cewa.

“To Umma dan Allah ya zanyi a hakanma fa ni ina ƙoƙarin ganin naje da wuri.”

“Dalla ni rufemin baki ki wuce ku tafi bana son dogon sharhi.”

“Yaya ABDUL kanajin abun da Umman take cewa ko kuma kaƙi magana” ta faɗa kamar zata fashe da kuka.

“Yi haƙuri ƙanwata karkiyi kuka,haba Umma ya kike ƙoƙarin sanya ƴar lele kuka dan Allah Umma ki bari haka,kuma fa ki kalla agogo ɗaya da rabi ma yanzu tayi to kinga bamuyi latti ba tunda sai ƙarfe biyu suke fara haddar,yanzu dai mu mun tafi Umma sai mun dawo” yaya ABDUL ɗin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye.

“To ABDUL ka dakeni mana saboda zansa ƴar lele kuka ko.” Ta faɗa tana hararar ABDUL ɗin.

Dariya sukayi gaba ɗaya sannan SALMA tace.

“Allah ya barmun ke Ummana ya ƙaramiki lafiya da nisan kwana,sai mun dawo byeeeee.”

SALMA ɗin ta faɗa tana mai nufar ƙofar barin ɗakin,shima yaya ABDUL ɗin bin bayanta yayi don zuwa ya kaita islamiyya.

Murmushi kawai Umman SALMA ɗin tayi tare da musu addu’ar dawowa lafiya,cikin jin ƙaunar tillon ƴartata da kuma godiya ga Allah daya bawa ƴartata masoyi kamar ABDUL ɗin.

Suna fita ƙofar gidan yaya ABDUL ya kalli SALMA sannan yace.

“Ƴar lelena hau mashin ɗin mu tafi karkiyi latti ko.” Cewar yaya ABDUL ɗin shima yana ƙoƙarin hawa mashin ɗin nashi.

Har ya hau mashin ɗin amma SALMA bata niyyar ko alamar motsawa daga inda take,juyowa yayi yana kallonta ganin bata hau mashin ɗin ba.

“Ya dai ƴar lele ki hau mana mu tafi.”

Noƙe kafaɗa SALMAN tayi sannan cikin shagwaɓe fuska da murya kaman zatayi kuka tace,

“Uhmmm Uhmmm nidai gaskiya yaya ABDUL mu tafi da ƙafa kawai ka tura mashin ɗin mu tafi.” Ta ƙarasa maganar tana wasa da bakin hijabi ɗinta.

Dariya yaya ABDUL ɗin yayi sannan yace.

“Kai ƴar lele rigima Allah dai ya nunamin ranar da zaki zama mallakina duk wannan rigimar taki sai na cireta.” Ya faɗi yana sanya hannu tare da jan leɓen bakinta da ta turo na ƙasa ita a dole tana shagwaɓa.

“Aucchhh wayyo Allah bakina yaya ABDUL wallahi da zafi.” Ta faɗa tana bubbuga ƙafa a ƙasa tare da yin narai narai da ido.

“To yi haƙuri SALMANA tauraruwata mai haske duniya ta mu tafi kinji amun afuwa”

Ya ƙarasa tare da haɗe hannayen shi waje guda alamar bada haƙuri.

Murmushi tayi wanda ya ƙara bayyanar da tsantsar kyawunta har sanda kumatunta ya lotsa.

“To shikennan yaya ABDUL ɗina na haƙura ai baka laifi idan kayima to an daɗe da yafema.”

“Masha Allah godiya nake gimbiyata, yawwa ina fatan dai kinyi haddar ki ko?”

“Eh yaya ABDUL nayi” Cewar SALMA ɗin bayan sun kama hanyar tafiya.

“Yawwa ƴar albarka Allah ya miki albarka ya kaimu nanda sati biyu inda za’a ɗauramana aure dan na matsu in ganki a gidana.”

“Ameen ya Allah yaya ABDUL ɗina nima na matsu wallahi.”ta faɗa tana rufe fuskarta alamar kunya.

Haka sukaci gaba da tafiya suna hira kana ganinsu kaga masoya na gaskiya, a haka har suka ƙarasa islamiyyar su SALMAN, har bakin ajin su ya rakata kafin suyi sallama dama kullum haka sukeyi shi yake kaita makarantar sannan in lokacin tashi yayi yaje ya ɗakkota.

Saida ya tabbatar ta shiga har cikin ajin nasu kafin ya juya ya hau mashin ɗin shi ya nufi hanyar komawa gida.

<< Wata Kaddara 1Wata Ƙaddara 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.