Skip to content
Part 11 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Buhari be zo gidan ba se da ya kai Halima asibiti ya bar Saleh a wajen sanna ya zo, da kukan shi yana fad’in “shikenan yaya ka ta fi ka bar ni wayyo na shiga uku na”, Ummar ne ya ri’ke shi don yanda ya ke yi kamar me shirin hauka ba su san duk shirin makirin mutum bane, hakuri aka yi ta ba shi, bayan an gama mai addu’a aka tafi aka kai shi gidan shi na asali, shikenan se dai muce Allah ya yi mai rahama, ameen.

Buhari har da shi ake ‘kar’bar gaisuwa kamar besan me aka yi ba, an watsa cigiyar Halimat kaf garin Adamawa shiru har yanzu ba wani labari yau kwana3 da rasuwar Abubakar Ummar da matan shi har yanzu su na nan sun bar yaran a wajen kakan su.

Yau bakwai d’in Abubakar har yau mutane zuwa su ke yi don mu su gaisuwa momin shi ma har yanzu ta na nan Ummar kuwa yau su ke shirin koma wa Kaduna, amma ran shi be yi dad’i ba da har yanzu ba’a ga Halima ba don amanar shi ce.

Buhari sun kai ta asibiti inda aka shaida mu su dogon su ma ta yi kuma cikin jikin ta ya kusa fita amma be fita ba hakan Buhari be ji dad’i ba don ya so cikin ya zu be in da aure kawai za su yi amma yanzu se ta haihu tukuna, kwanan ta uku a asibitin aka sallame su a ranar kuma yabar jahar Adamawa da ita ya kaita wani gida da ya ke ginawa a Jigawa.

Yau kwana Arba’in 40 da rasuwar Abubakar Momin shi ta koma an raba gadon shi an bawa momin shi nata an bawa Buhari don su kad’ai su ka rage se na Halima an bawa Dad ta ya ajiye mata, ana ta neman ta har sun gaji shiru har yanzu, Ummar ma yana cikin tashin hankali sosai don yana ganin be ri’ke amanar da Abubakar ya bar mai ba na ya ri’ke mai iyalen shi.

Halima duniya ta canza mata Lokaci guda, kullum ku ka ta ke wuni yi, ga shi ba dama ta runtsa, don da ta rufe ido ta ke ganin kisan da aka yi wa Abubakar a gaban ta kamar ta yi hauka, ta na addu’a Allah ya sa ya kasance mafarki ne, Kamar kullum ta na zaune ta na aikin da ya zame mata jiki, Buhari ne ya bud’e kofar ya shigo cikin sauri ta mi’ke tsaye don tun da aka d’auko ta bata ta’ba ganin shi ba se yau da sauri ta je wajen shi tare da cewa “Buhari ka ji abun da ya faru ko sun kashe mana Ya Abubakar kuma Allah ze sa ka mai Allah ya to ni asirin su”, Alhaji Buhari kallon ta kawai ya ke yana aiyana wani abu a ran shi, “Buhari me mu ke yi anan ka mayar da ni gida wajen momi don Allah!” “ke malama kin dame ni da surutu ko, ki wuce ki zauna na le’ko ne kawai amma yanzu ma tafiya zanyi” “Buhari kai ka kawo ni nan da ma?”, “Ehh”, “to saboda me?”, Saboda ina so na maye gurbin yana!” Halimaa zaro idanun ta yi tare da cewa “ban fahimci me ka ke nu fi ba” dariya Alhaji Buhari yayi sannan yace “ina nufin auren ki zan yi”, cikin tsantsan firgita da tashin hankali haɗe da mamaki tace “Buhari Kasan me ka ke faɗa, Ni zaka ce zaka aura, to wallahi idan mafarki ka ke to ka farka, don wallahi bayan taɓa yarda ba” dariya yayi sannan yace “dama yardar ki na ke nema?, to ki sani ko kin yarda ko ba ki yarda ba, Gara ma ki yarda”, yana fad’in haka ya juya ya fita tare da rufe d’akin kuka Halima ta sa mai tsuma zuciya, durkushewa ta yi a wajen ta na kuka ta rasa me ke mata dad’i, a haka har bacci ya d’ibe ta.

Alhaji Buhari be sa ke waiwayo ta ba don sun ma kama hanyar Zamfara ne wajen boka, se yamma li’kis sannan su ka isa, kamar kullum sun kwashi gaisuwa, Saleh ne yace “Allah ya taimaki boka mun aiwatar da aikin nan fa, Abubakar yanzu ya zama d’an gari a lahira”, dariya sosai bokan ya yi sannan yace “ai tun kafin ku zo an sanar da ni kun aikata yanzu ina matar ta ke ta na gida na a Jigawa to shikenan cikin jikin ta yanzu watan shi hud’u, nan da wata Biyar ana saka ran haihuwar ta to awannan lokacin ne zan d’aura mu ku aure da ita, bayan haihuwar ta da kwana 30, amma gidan nan da ka aje ta akwai matsala, ka mayar da ita gidan ka”, cikin firgici Alhaji Buhari yace “amma boka Ba ka ganin da matsala, kasan matata Jamila”, “ba wani matsala zan yi aiki guda biyu ne akan ta, na farko akan Halima ne don idan bakin ta na nan asirin ka ze yi saurin tonuwa, na don zata iya samun ko waya ne ta kira wani wanda ta sani, shiyasa zan mata asiri na rashin magana, na biyu akan matar ka ne za’a yi mata wanda za ta yarda Halima ta zauna a gidan.

dariya su ka yi sannan Alhaji saleh yace “aikin ka na kyau boka” “ba kyau ba ne aikin ku ze ja kud’i sosai” “boka kasan kud’i ba matsala ta ba ne akwai su aiki dai mu ke so mai kyau” dariya boka ya yi sannan yace “yanzu da kun koma gida ka mayar da ita gidan ka”, “to za’ayi hakan” cewar Alhaji Buhari tare da zu ba mai kud’i ma su yawan gaske, su ka ta shi su ka tafi.

Hotel su ka kama a garin Zamfara don dare yayi musu.

Washe gari jirgi su ka bi su ka zo Jigawa su na sauka kuwa gidan da Halima ta ke suka fara zuwa su ka d’auko ta sannan su ka nufi gidan shi, Su na isa kuwa Hajiya Jamila na zaune a falo ta ga shigowar su asirin da ya aka yiwa Halima har ya fara don bata magana yanzu Cikin sauri Jamila tace “a’ahh daga ina? haka waye wannan?” be amsa mata ba se kiran wata ‘yar aikin su ya yi Mai su na talatu, cikin sauri ta ‘karaso falo ta zube ta gaishe shi, kallon ta yayi yace “ga wannan ki kaita d’akin can ciki na kusa da na ku hakkin kulawar ta ya dawo kan ki cinta shan ta da komai nata” “to ranka ya dad’e” tace tare da jan hannun Halima da se kallo ta ke bin su dashi ta rasa me Buhari ke nufi da ita, wajen Hajiya Jamila ya jiyo sannan yace “zata zauna a gidan nan na wani lokaci” “ban gane ba me ka ke nufi da zaman ta agidan nan”, “auren ta zanyi to”, ai tsalle Hajiya Jamila ta yi ta dire tace “baka isa ba ka min kushiya, au dama ka kashe yayan na ka ne don ka auri matar shi to ba ze sa’bu ba wallahi tana kai nan ta wuce d’aki shi ma Alhaji Buhari d’akin shi ya nufa.

*****

Haka dai Hajiya Jamila ba don ta so ba da kuma taimakon boka da kuma ƙaddarawar Allah Hajiya Halima ta zauna a gidan, yau satin ta biyu a gidan, kuma yau ne watan Abubakar biyu da rasuwa, cikin ta kuma ya shiga wata biyar, gaba ɗaya bata cikin sukunin da walwala kullum kuka ga ciki ga shi ba ta cin abinci don cikin na ta ba mai son ci ba ne, ga wahala da ta ke sha, ga wani rama da ta yi sosai, idan ka ganta se ka tausaya mata, kullum kuka, Alhaji Buhari kullum se ya leƙo ta, ya yi ta rarrashin ta, yayin da Halima ko kallon shi ba ta son yi.

Yau ma kamar kullum Halima na kwance a makeken gadon ta ta na abun da ya zamar mata jiki wato kuka, Alhaji Buhari ne ya turo kofar ya shigo, tashi ta yi ta zauna ƙarasowa ya yi yace “iska na wahalar da mai kayan kara, wai ke ba ki da aikin yi ne, kullum kuka, addu’ar ki yaya yake buƙata yanzu ba wai ki zauna yi mai kuka ba”

Halima da ta ke jin kalaman shi kamar an zuba mata harsashi ne a ƙahon zuciya, don zuciyar ta ta fara zargin Buhari akan mutuwar Mijinta.

Kallon shi ta yi yayin da har yanzu kwalla ke bin idonta ta na son ta yi magana amma ta kasa, murmushi yayi yace “da ma kin daina wahalar da kan ki, don na san me zaki ce ma, ki bari wannan kuka da kikeyi da baƙin cikin rasuwar yaya za ki barshi ne da zarar na aure ki, kinji ko” Halima kan ta ta mayar kan gadon tare da sakin wani Marayan kuka, Alhaji Buhari juyawa yayi tare da kwala wa Talatu kira, da sauri ta ƙaraso tare da cewa “gani ranka shi daɗe” “Talatu yau Halima taci abinci kuwa?”, “wallahi bata ci ba da ƙyar na samu ta ci kaɗan kuma sai da ta yi aman shi”, “to ki shiga ta samu ta ƙara ci, ki fito da ita tsakar gida kuma ta ɗan ga ni, tunda ta zo ta na ɗaki” “to shikenan bari na shiga” tace tare da shiga, shi kuma ya wuce, yayi gaba.

Abinci Talatu ta kawo mata amma ta ƙi ci ta yi nacin amma ta ƙi,hakan yasa ta ƙyaleta tare da ce mata, “to ki zo mu je ki ga gida,tunda kika zo kina ɗaki”, ba mu su kuwa Halima ta tashi su ka fita.

A dai-dai babban falon ɗakin su ka samu Hajiya Jamila na zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ta kara waya kuma a kunne da alama waya take yi, kure ta da ido Halima ta yi sosai ta ke kallon ta, gaban ta ne yayi wani mummunan faɗuwa lokacin da idon ta ya sauka kan wuyan Hajiya Jamila,sa ke kallon Sarkar wuyan ta ta yi ko shakka ba bu, wannan Sarkar ce Abubakar ya siyo mata ta Gwal a lokacin da su ka je asibiti aka tabbatar mai, daga can ma su ka wuce, kusan 3million ya so ya mata ita, ko makawa babu wannan ita ce ta faɗa a zuciyar tare da sake kallon Sarkar, baza ta taɓa mantawa da shi ba don yanda take son Sarkar tun da ya siya mata tace baza ta saka ba se ranar sunan ɗan su, amma kusan kullum se ta ɗauko ta gwada shi kuma ta kalla,don son Sarkar ta ke yi sosai.

Tunani kala-kala su ka fara zuwa ranta, to me ya kawo Sarkar nan wajen Hajiya Jamila, bayan ko ranar da za a kashe Mijinta ta Ganshi a gidan, to ko Zargin ta gaskiya ne, Buhari na da sa hannu a kashe mijin ta, wata zuciyar tace kar kiyi mai mummunan zato don ko ƙiyayya be taɓa nu na mai ba, kuma ɗan uwan shi ne na jini, sannan kuma zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ne, amma to me ze sa Buhari ya kawo ni nan har da cewa ze aure ni bayan ni matar ya’yan shi ce, ko ma auren ne ai wajen iyaye na ya kamata ya je.

tunani take ta yi sosai a cikin zuciyar ta ba ta dawo ba se da ta ji an daka mata wata uwar tsawa, a firgice ta ɗago kan ta, Hajiya Jamila ne tsaye riƙe da kugu tace “maitan na ki ya ta shi ne cinye ni zakiyi ki ka kura min idanun”, Halima da idon ta har sun fara kawo ruwa ta tsaya kallon ta, ita ko Hajiya Jamila bata ga ji ba ta cigaba da masifar ta.

Talatu ne tace “Hajiya a mata hakuri don Allah” ita kuwa komawa ɗaki ta yi ta na kuka don hankalin ta tashi yake yi a duk lokacin da ta tuna Abubakar wai ya mutu, da ace ba a gaban ta aka kashe shi ba da bazata yarda Abubakar ya mutu ba, kuka ta cigaba da yi sosai ta na yi wa mijin nata addu’a.

A falo kuwa faɗan ya koma kan Talatu ne, hakuri ta dinga bayarwa kamar ta ari baki, se da Hajiya Jamila ta gama faɗan nata sannan ta wuce ɗakin ta.

Adamawa

Yau wata biyu2 da rasuwar Abubakar, Ahmad ya samu lafiya amma har yanzu hankalin shi a tashe yake na ɓatar ƴar sa, gudan jinin sa, anyi cigiyar har an gaji amma ba’a samu Halima ba, momi ma hankalin ta a tashe yake, sun biya malamai ana ta addu’a don yanzu, shiru har yanzu ba wani labari.

Momin Abubakar har yanzu hankalin ta be kwanta ba na mutuwar ɗan nata, ta na ta yiwa ɗan nata addu’a, kuma ta na yiwa surikar ta Halima addu’ar Allah ya bayyana ta.

Ummar ma tun bayan rasuwar Abubakar ya zo kusan sau biyar kenan don jin labarin Halima, amma shiru har yanzu ba labarin ta.

*****

Yau wata huɗu4 kenan da rasuwar Abubakar, Halima na zaune har yanzu a gidan Alhaji Buhari, ba abun da ya canza har yanzu, don yanzu cikin jikin ta watan shi takwas8 yayi girma sosai, har yanzu dai tashin hankali be bar rayuwar ta ba, gashi har yanzu bata magana, Talatu ke kula da ita har yanzu, Alhaji Buhari yace ko matar shi Jamila be yarda ta bata key ɗin ɗakin Halima ba, don yanzu rufe ta ake yi,se dai idan an kawo mata abinci, yanzu ba lefi ta na ɗan cin abincin ba kamar da ba.

Halima yanzu zargin da ta ke yi wa Alhaji Buhari ya kusa tabbata don bayan Sarkar nan da ta gani a wuyan Jamila, ta sake gani wa su duk nata ne na Gwal, da awawwaro su ma duk na Gwal ne, amma har yanzu wani sashi na zuciyar ta be gama yarda da hakan ba, ta san kuma a wajen waɗanda su ka shigo gidan su da dare ne kawai za’a samu waɗannan kayan to mai ya kawo su wajen Hajiya Jamila, cikin ɗayan biyu ko ita Hajiya Jamilan ne da saka hannun ta ko kuma shi ko ma dai waye Allah ya to ni asirin shi.

Alhaji Buhari ya ƙara tabbatar wa Hajiya Jamila cewa auren Halima ze yi don ya tsayar da rana ma nan da wata biyu2, hakan ya sa hankalin ta tashi sosai ta ƙudiri aniyar kuma auren ba ze ta ɓa yiwuwa ba, hakan ya sa ta nemo ƙawar ta Zubaida su ka nufi wajen Mallam don sun daɗe ma ba su je ba.

Malamin da su ke zuwa wajen shi ɗan kwara ne, kuma yau su ka shirya zuwa don ayi mu su aiki.

Bayan sati biyu da zuwan su Halima ta fara hauka, hakan ba ƙaramin tasar ma da Alhaji Buhari hankali yayi ba ya koma wajen na shi bokan ya faɗa mai ba ze iya ba,amma ya jira bayan haihuwar ta akwai abun da ze yi, haka ya dawo.

Halima ta koma abun tausayi yanzu don ga ciki ga hauka gashi kuma, bata magana, ka kewar ƴan gidan su da mijin ta, da kullum ta kwanta se tayi mafarkin shi.

Adamawa

Anyi neman Halima har an gaji ba labari yanzu ma har an de na cigiyar ta, don Daddyn Ahmad ya je wajen wani malamin addinin musulunci ya yi istihara ya tabbatar mai jikan shi yanzu ta na buƙatar addu’ar su, kuma za ta dawo gida amma ba nan kusa ba, su kwantar da hankalin su, ta kusa fita damuwa, hakan ba ƙaramin tasar ma Ahmad hankali yayi ba, da kowa ma na gida, hakan ya sa ma ya koma India da matar shi bayan suna, don ta haihu yaran ta biyu kyawawa suna nan, Khadijah   (Sukrah) da Ibrahim(Khalil) yaran gwanin sha’awa gashi son yaran ya shiga zuciyar Ahmad da momin shi.

Halima ce zaune a ɗakin da ya zama nata, hannun ta rike da qur’ani da alama karantawa take yi yayin da hawaye ke bin fuskar ta, ake qur’anin naga ta yi sannan ta jingina da jikin gadon idon ta a rufe amma hakan be hana hawaye fita ba, ta daɗe a haka kafin ta koma kan gadon wani bacci me nauyi ya ɗauke ta.

Abun mamaki ba kowa yasan cewa Halima na dawo dai-dai idan dare yayi ba don ko Hajiya Jamilan ma bata sani ba, har Talatu me kula da ita ma, duk ba su sani ba, yayin da dare ya zamo mata lokacin kai ƙarar ta wajen Ubangijin ta, da yiwa mijinta addu’a da kuma ƴan uwanta.

Cikin Halima ya shiga wata tara har da kwanaki ma, haihuwa ko yau ko gobe, Buhari baya garin ma ya tafi Sokoto don yaran shi sun kira shi, don sun matsa mai se yayi musu birthday, hakan yasa shi tafiya garin, har yanzu Hajiya Bilkisu bata sake haihuwa ba,yaran ta uku ne, Abbas wanda yanzu ya kai shekara12, amma idan ka Ganshi za ka ce ma ya wuce haka don yana da jikin girma, se kuma Asma’u, se Fatima. dukan su aka yiwa birthday an kashe kuɗi kamar ba neman su ake da wahala ba, abokan su, ƴan ajin su, su duk sun halarta da wa su ma, ƴan anguwan.

Kaduna

Umar har yanzu hankalin shi ya ƙi kwanciya, na rashin ganin Halima don yana yawan zuwa gidan su Ahmad amma ba labari har yanzu, yaran shi su na ta wayo, feddauseey ita ce Babba tana da shekara 10 yanzu se Muhammad wanda su ke cewa Amir yana da shekar8 se kuma A’isha mai shekar6 se kuma Ibrahim (Khalil) mai shekara4, se kuma jaririyar da ta haifa me wata ɗaya, sunan ta, Zulaihat (Nur) suna zaman su Lafiya da matar shi Bilkisu don halin su yazo ɗaya duk ba na yarwa.

<< Wata Rayuwa Ce 10Wata Rayuwa Ce 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×