Wata ranar juma'a Halima ta fara naƙuda cikin dare lokacin da hankalin ta, gashi ba kowa a ɗakin, Alhaji Buhari ma be dawo ba daga Sokoto, tun wajen 10:00 na dare, har gabannin asuba, bata haihu ba, iya wahala tasha shi, gashi kuma ana yin Asuba haukan ya dawo, se buge-buge take yi a ɗakin, hakan ya sa ma su aikin da suka tashi yin Sallah nufar ɗakin nata amma a kulle yake, gashi baza su iya buɗewa ba, hakan yasa su ka koma su ka ta so Talatu don bacci ta ke yi ma. . .