Skip to content
Part 12 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Wata ranar juma’a Halima ta fara naƙuda cikin dare lokacin da hankalin ta, gashi ba kowa a ɗakin, Alhaji Buhari ma be dawo ba daga Sokoto, tun wajen 10:00 na dare, har gabannin asuba, bata haihu ba, iya wahala tasha shi, gashi kuma ana yin Asuba haukan ya dawo, se buge-buge take yi a ɗakin, hakan ya sa ma su aikin da suka tashi yin Sallah nufar ɗakin nata amma a kulle yake, gashi baza su iya buɗewa ba, hakan yasa su ka koma su ka ta so Talatu don bacci ta ke yi ma a lokacin, key ta saka ta buɗe ɗakin, hankalin ta yayi matuƙar tashi da halin da ta ga Halima a ciki da sauri ta fita tare da rufe ƙofar don har ga Allah ta na jin tsoro kar ta shiga ta yi mata wani abun, hakan yasa ta ɗauki wayar ta ta kira, Alhaji Buhari ta shaida mi shi, cikin tashin hankali yace gashi nan zuwa Jigawa yanzu, Talatu har yanzu ta na ƙofar ɗakin ta kasa shiga kuma ta kasa tafiya ta barta.

Halima kuwa tana nan tsabar azaba yanzu ta suma ma ko motsi bata yi, ga ciwuka da ta jima kan ta sosai, jini ne kwance a ɗakin sosai.

Ƙarfe 10:00 Alhaji Buhari ya iso Jigawa don jirgi ya bi, cikin sauri aka kai Halima Asibiti.

Wajen ƙarfe 5:00 na yamma sannan Halima ta sauka ta samu ƴarta mace mai tsantsar kama da ita sosai, yayin da har yanzu bata farfaɗo ba.

An shirya jaririyar cikin kayan sanyi kasancewar garin akwai sanyin damina sosai, ta yi kyau abun ta kamar ka sace ka gudu gata ƙatuwa ce sosai.

Halima bata farfaɗo ba se washe gari ko da ta farfaɗo, haukan ta cigaba hakan yasa likitan yin mata allurar bacci.

Kwanan su biyar a asibitin aka Salleme su, su ka dawo gida, ƴar tana hannun Talatu, Alhaji Buhari siyayya sosai yayi ma yarinyar har da madara don shi ake bata.

Talatu ta gane Halima na dawowa dai-dai idan dare yayi hakan yasa take kawo mata ƴar ta, kamar kullum yau ma ta kawo mata yarinyar, se dai ta ta sa ƴar a gaba ta na kuka, da tuno wasiyyar da Abubakar ya bar mata ranar da ze mutu, cewa ” idan mace kika haifa kisa ka mata Khadijah idan kuma namiji ne kisa mai Al-amin” wani kuka ne ya kwace mata daga jin kukan zaka gane na tsantsar damuwa ne da rashin jin daɗin rayuwa, don a yanzu har Gara mata mutuwa idan za ta zamo mata Hutu a gare ta, don Alhaji Buhari ya tabbatar mata da cewa bikin su saura kwana ashirin 20, don yau kwanan ta goma da haihuwa kamar yadda boka yace se ta kwana talatin, ita kuma ta tabbatar mai indai ya aure ta a ranar zata kashe kanta, don baza ta iya jure kallon shi a matsayin mijin ta ba.

Yau kwanan Halima ashirin da Haihuwa, yayin da Alhaji Buhari ke ta shirin bikin amma ba wanda ya sani ko a bokan shi don bikin na sirri ne, Hajiya Jamila kuma ta yi iya yin ta don a tunanin ta idan ya ga, ta haukace ze fasa amma abu yaci tura, ta koma gurin bokan ta ya shaida mata indai Halima na gidan to auren su ba makawa, hakan ya sa ta shirya, yadda zata ɗauke Halima tabar gidan.

Yau kwana Ashirin da biyu da haihuwar Halima yau kuma Alhaji Buhari ya shirya zuwa Sokoto daga nan ze biya Zamfara ya bar amanar Halima a wajen Talatu kamar yadda ya saba idan ze yi tafiya.

Washe garin tafiyar shi, Hajiya Jamila ta zo ma Talatu da barazanar kashe ta da ƴan’uwan ta duka indai bata bata mukullin ɗakin Halima ba, ita kuwa Talatu da tsoro ta bayar don tace gara ta bada akan ta shiga faɗar mata da miji, a kashe ta a banza su kuma su cigaba da rayuwar su cikin jin daɗi.

Washe gari ranar ne kuma Hajiya Jamila ta zo ita da yaran da za su mata aiki su ka fita da Halima da yarinyar ta, tace musu suyi nisa da Jigawa su yarda ita kawai, haka ayi kuwa sun bar gidan da ita inda suka nufi Kaduna da ita.

A Cigaba Da Labarin Mu

Kaduna

Baffa be dawo gona ba se wajen ƙarfe biyu12:00 sannan don yayi aiki ne sosai a gonar, su Garbati kuwa se yamma su ka dawo kiwo don dama idan su ka tafi suna kai la’asar wani lokacin har gabannin magriba, tun da da abincin su suke tafiya.

Sokoto

Kamar yadda Alhaji Buhari yayi cewa kwana huɗu ze yi a Sokoto, hakan ta kasance don har ya koma Jigawa ma ya bar yaran shi cike da kewar shi, don su na son Daddyn na su sosai, shima yana son su.

Jigawa

Alhaji Buhari ya dawo kamar yanda yace sun haɗu da abokin na shi, inda su ka sake neman mazaa don gobe zasu wuce Zamfara, Mazaa ya shaida mu su har yanzu neman Alamz yake be same shi ba, sun ƙara bashi makudan kuɗi, yayi mu su alƙawarin nemo Alamz don shi ze kai shi garin da su ka kai Halima.

Washe gari Alhaji Buhari da aminin shi su ka shirya zuwa Zamfara, sun fita da wuri don Ƙarfe12:00 ma anan ta yi mu su.

Zamfara

A durƙushe na hango su gaban bokan ya dage se masifa yake sirfa musu, Alhaji Saleh ne ya gyara zama tare da cewa “Boka mun san munyi lefi mun saɓa alƙawari,amma a gafarce mu” cikin tsawa Bokan yace” ba wannan maganar kuma,yanzu auren ka da Halima ma ba shi gaba ɗaya se dai wata hanyar kuma”, cikin firgici Alhaji Buhari yace “Boka ayi hakuri, a taimaka min da wata hanyar”

dariya bokan yayi na rabin minti sannan kuma ya ɗaure fuska, sannan yace, “zan duba na gani amma dai ku tafi zuwa jibi ku dawo” cikin haɗa baki su ka ce “Mun gode boka” tare da miƙewa su ka kama hanyar garin su.

Alhaji Saleh yasa an saki Talatu bayan dawowar su don ta faɗa mu su gaskiya bata yi mu su ba, amma ta ji jiki sosai hakan ya sa ma tabar aiki a gidan gaba ɗaya don ta na tsoron Hajiya Jamila, don haɗuwar su ba ze yi kyau ba, shiyasa bata koma Kano ba ma don zata iya nemo ta, ta nufi Abuja wajen anty ta.

Yau da gobe ba wuya har ranar da boka ya saka ma su Alhaji Buhari yayi don suna hanyar Zamfara ne ma yanzu.

Ƙarfe10:00 na safe a can yayi mu su don sun ƙosa su ji wani abu ne Boka ya yanke, don har kasa bacci su ke yi ma.

Kamar yadda su ka saba su na gurfane a gaban Boka, Alhaji Buhari ne yace” Allah ya taimaki boka gamu mun dawo, mu na sauraren abun da za ka aiwatar” dariya boka yayi sannan yace “kun samo ta ne?” “a’a” “to dama kamar yadda nace maka maganar auren ka da Sadiya ba shi, to yanzu ya dawo kan ɗan ka” Cikin rashin ganewa da fahimta Alhaji Buhari yace, “Boka ban fahimta ba”, “ina nufin ɗanka Abbas ka haɗa shi aure da ƴar Halima da ta haifa!” Mamaki ne ya kama Alhaji Buhari wai ɗan shi Abbas, “to Abbas har guda nawa yake, ita kuma yarinyar da take cikin tsumma wanda ko lissafin shekarun ta ba’a fara ba” tunanin da Alhaji Buhari yake yi kenan a cikin zuciyar shi, boka ne ya katse shi da cewa “Buhari kenan kana tunanin ba ze yiwu ba ko?, to tabbas abu ne mai yiwuwa, se dai jiran Lokaci” Alhaji Saleh da abun ya ɗaure mai kai shima, kallon bokan yayi yace “Haba boka yanzu se mun jira a ƙalla nan da wa su shekaru kafin ayi mana aikin, da da yadda za’ayi ai se mu nemo Halima kamar yarda kace tun farko” dariya Boka yayi sannan yace “yaro man kaza!, ai batun auren ku da Halima yanzu ku de na maganar ma, ba ku fahimci ni bane gaba ɗaya, yanzu zan muku aiki amma ze ci kuɗi sosai domin neman kuɗi se da kuɗi, shi kuma maganar auren ɗan ka wannan shine ɗorewa da tabbatuwar aikin ka da kuma tabbatuwar rufin asirin ka” Dariya su ka yi gaba ɗayan su sannan Alhaji Buhari yace ” ai baka yi mana bayani ba ne tun farko amma kaga yanzu mun gane, kuma za’a aiwatar da hakan” dariya Bokan ma yayi, sannan yace ” to yanzu maganar ɗauko Halima ma bashi, kawai ƴar zaka ɗauko, ka raine ta da hannun ka, ita kuma Halima ka bar ta a wannan waje”

Alhaji Buhari ne yace “boka amma ka na ganin Barin Halima a wani waje asirina baze tonu ba, Halima ta san ni na ɗauketa, kuma tana zargin ni na kashe yaya, ka ga barin ta a wani waje ze iya zama min matsala, don duk lokacin da ta dawo dai-dai zata iya komawa Adamawa kuma asirina ze tonu” dariya Bokan yayi sannan yace” ka bar wannan a hannu na akwai aikin da zan mata zata manta komai da ya shafi rayuwar ta ta baya, don haka ita kan ta bazata san waye ita ba bare ta bada labarin ka”, dariya Alhaji Buhari yayi tare da cewa” kai aikin ka na kyau, mun gode”.

Haka su ka cigaba da shirin su, har su ka gama su ka nufi gida.

Kaduna

Yau satin Halima uku3 a Kaduna gidan Baffa har yanzu Mallam na mata magani don yanzu ma ta daina hauka ta dawo dai-dai se dai har yanzu bata magana.

Yau ma kamar kullum su na tsakar gida su na aiki, Inna ta na yanka alayyahu, Halima kuma tana daka, su kaɗai ne a gidan, don Baffa da Bashir su na gona, Garbati kuma yana gidan mai gari, su Hassana kuma sun shiga maƙota gidan wata ƙawar su, Maryam su da Ilham.

Inna yanzu ta huta sosai don tare su ke aiki da Halima komai, Inna ta gama yankan Alayyahu ta zuba a miyar, da yake tuwon shinkafa su ke yi miyar taushe, Halima ma ta gama daka gyaɗan su na zaune, don sun gama aikin, miya ne kawai ya rage mu su.

Su Hassana ne su ka shigo da Ilham don ta fara Kuka, Inna ce ta ƙarɓe ta da sauri, ta na faɗin” ta gaji ko?, kawo ta a kaita wajen mamanta”, miƙawa Halima ta yi, Halima murmushi ta yi tare da ƙarban ta, Inna ta koma ta sauke miyar ma don ya nuna.

Sokoto
Alhaji Buhari da abokin shi ne zaune a wani katafaren gidan su da suke kan gina wa don yanzu gidajen su ma baza su irgu ba, Alhaji Buhari ne ya kalli Mazaa da ke zaune ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yana ɗaga lemo yace” wai Mazaa ya ake ciki ne ba wani Labari ne, kasan kai muke jira da a wannan aiki ko” dariya Mazaa yayi tare da cewa “haba Alhaji daɗi na da kai gaggawa, ka kwantar da hankalin ka, tunda ka ga nace mu haɗu yau Kasan ai akwai labari ko?” dariya Alhaji Buhari yayi sannan yace “yanzu naji magana amma ka zauna ka yi shiru ai se na ɗauka ba wani labari ne” “kwarai kuwa” cewar Alhaji Saleh.

Mazaa ne ya gyara zama bayan ya a jiye lemon da yake sha sannan yace “Dama na faɗa muku Alamz na ke jira don shi ne kawai ya san garin da mu ka kai ta ko?”, cikin haɗa baki su ka ce “Ehh” “to na gano inda yake, yana Lagos don an kama su ne da laifin fashi da makami a gidan wani babban ɗan siyasa an kama su yanzu haka yana hannu” “to miye abun yi yanzu” cewar Alhaji Saleh “Ehh da yiwuwar fitowar shi indai Naira na aiki a Nigeria, abun buƙata kawai shine Kuɗi, indai kun bani, gobe-gobe zan je Lagos ɗin da yardar Allah jibi ma Alamz yana hannu”,

Alhaji Buhari ne yace “Kasan kuɗi ba matsala na bane indai aiki je cika”, dariya Mazaa yayi sannan yace “yanzu kuɗin ze samu ko baza samu ba?”

“Kuɗi ze samu Mazaa amma ka sani idan aiki be yiwu ba, Kasan Ni waye Nima na san ka, Kasan da wannan?”

Dariya Mazaa yayi yace “Alhaji kenan ai muna tare hakan ma baza ta faru ba”

“to shikenan Zaka ji alert anjima kaɗan”

“Ko kaifa” cewar Mazaa tare da miƙewa yace “se na ji ku”.

Bayan fitan Mazaa su ka zauna su ka cigaba da tattaunawa har gabannin magriba sannan su ka watse kowa ya koma gida.

Sokoto

Bayan tafiyar Daddyn su sun cigaba da rayuwar su kamar yadda su ka saba sun koma makaranta sun cigaba da karatun su, sun mai da hankali kamar yadda su ka saba, don momin su na ƙoƙari sosai akan karatun su, don yaran ta su ne farin cikin ta yanzu, bata da wani buri da ya wuce mata ta ga sun samu Ilimi sosai.

Jigawa

Mazaa ya ji alert ɗin shi kamar yadda su ka ce, inda ya shiga ya fita har aka saki Alamz yanzu sun dawo Jigawa ma tare sun shirya tafiya Kaduna sati me zuwa.

Alhaji Buhari sun ƙara faɗawa Mazaa cewa yarinyar kawai za su ɗauko ban da uwar, don ranar Laraba su ka shirya za su je Kaduna yau Litinin, rana kawai suke jira.

Kaduna

Bayan Sallar magrib kowa na zaune ana ta fira tun daga kan Baffa da kowa na gidan har da Halima ana ta hira, Inna na riƙe da Ilham a hannun ta Halima kuma ta na kusa da ita, Inna ce ta kalli Halima tace “Halima kin sha maganin da Mallam ya baki?” Murmushi Halima ta yi tare da ɗaga kai alamar Ehh “to kar ki yi wasa da shan maganin, tunda munga amfanin sa ga ki kin fara samun sauƙi” cewar Inna, Ita dai Halima se dai ta yi Murmushi kawai, haka su ka cigaba da hirar su har zuwa lokacin da su ke kwanciya yayi kowa ya nufi ɗakin shi.

Washe gari Kamar yadda su ka saba, kowa ya tashi Baffa, Garbati da Bashir duk sun tafi Masallaci, Inna kuma ta nufi ɗakin Halima domin tashin ta, ta tarar da ita ma har ta tashi ta na Sallah, Inna bata yi mamaki ba don tasan Halima da son ibada kullum idan taje tashin ta se dai ta ganta ta tashi, abun da Inna bata sani Bama Halima tun da ta samu Lafiya tun tsakar dare take tashi ta yi alwala, ta dinga yin Sallar ta na kaiwa Allah kukan ta, da yiwa mijin ta Addu’a har zuwa asuba.

Bayan Inna ta fita ta je ta tashi su Hassana su ka yi Sallah, Sannan ta fito domin yin aiki, ruwan wanka ta fara sakawa Yaran kamar yadda ta saba.

Bayan ruwan yayi zafi ne ta ɗiba a baho ta nufi ɗakin Halima don yi ma Ilham wanka, kasancewar ita ta ke yi mata kullum.

Bayan ta mata wankan ne, ta fito don barin Halima ta shirya ta, ta fito don yai ma su Hassana wankan.

Bayan ta gama mu su Wankan ne ta mayar mu su da abin kari, ta na cikin aikin ne Halima ta fito wajen ta ta nufa da Ilham goye a bayan ta.

“Sannu da aiki Inna” Cewar Halima, Inna da take Juye ruwa a flas juyowa tayi don ganin me maganar, ƙure Halima ta yi da ido ganin ita kaɗai ce tsaye, to waye yayi mata magana, Murmushi Halima ta yi tare ƙara cewa “Inna ni nayi miki magana fa, tun jiya da dare magana ta ta dawo ina cikin karatun Qur’ani ina yi a zuciya, ban san lokacin da na fara yi ba, na yi ta gwada yin magana ma” Inna da farin ciki sosai ya kama ta, rungume Halima ta yi ta na faɗin “Allah mun gode maka, da ka buɗewa wannan baiwa taka baki”

Dai-dai lokacin kuma su Baffa su ka shigo gidan da Sallamar su, Inna ce ta taje gurin Baffa da saurin ta tana faɗin “Baban Bashir ka ga wani ikon Allah, Halima ta dawo dai-dai tana magana yanzu”

Murmushi Baffa yayi sannan yace “Alhamdulillah, naji daɗin haka sosai”

Halima zuwa wajen Baffa ta yi tare da cewa “Barka da safiya Baffan!”

“Yawwa sannu ya kwanan Mamana?”,

“Lafiya lau” cewar Halima Sannan ta juya inda su Garbati su ke tace “Sanun ku ƴan samari” Murmushi su ka yi sannan su ka gaisa, ƴan biyu ma sun fito sun gaishe ta tare da ƙarɓar Ilham don suna da son yara sosai shiyasa kullum Ilham na hannun su.

Aikin su ka cigaba da yi tare su na ɗan taɓa hira har su ka gama aka zubawa kowa nashi abin karin.

*****

Yau talata kuma yau ne su Mazaa su ka shigo Kaduna shi da Alamz shi yake tuƙin ma don shi yasan garin, aiko har wajen da su ka yar da Halima ya kawo su, sauka su kayi su ka gangaro zuwa cikin gari don su na son su san komai ne da gidan da Halima take, idan mutanen garin ne su ka ɗauke ta idan kuma ba su bane shikenan sai su koma.

Wani teburin me shayi su ka samu su ka zauna a zuwan sun zo siya ne, da ya ke sun canza shiga sun yi shiga ne irin na ƴan ƙauye idan ka gan su baza ka gane su ba, mutum biyu2 ne a wajen banda me sayar da shayin, su ma sun zo siya ne.

Bayan ya sallami mutum biyun ne da yake tafiya da shi za suyi ya juyo ya kalli su Mazaa yace “ƴan samari me za’a baku ne?, da alama ma ku ba ƴan gari bane” Alamz ne yayi Murmushi sannan yace “Baba shayi mu ke so da burodi” “to! banda taliya?”, “Ehh shayin kawai muke so” cewar Mazaa yana mamakin tsoho kamar wannan da sayar da shayi, shi a sanin shi matasa sun fi yi.

Juyawa yayi don haɗo musu shayin Alamz ne ya kalli Mazaa tare da cewa “kai Mallam ya za mu yi ne mu da muka zo neman labarin mun zauna anan” Murmushi yayi sannan yace “Matsalata da kai gaggawa!, shi yasa kake yawan shiga hannu kai dai ka zuba min idanu ka gani” “to shikenan zan gani dai” cewar Alamz yana kawar da kan shi gefe don ganin gari da masu wucewa.

Mazaa ne yayi gyaran murya sannan yace “Baba har taliyar ma a haɗa mana Saboda idan mun koma gona ba se mun nemi abinci ba”

Mai shayin ne wanda ake kira Mallam Sanda ya juyo tare da yin Murmushi sannan yace “ai kuwa kun yi dabara, kace aikin gona kuka zo?”, “Ehh Baba!, akwai gonar Baban mu ne can gaba mun zo aiki ne to kuma bamu ƙarya ba”

“to yayi kyau wani gari kuke?”

“Bamu da nisa da nan gaban ku muke kaɗan” “Ehh tabbas na gane garin” faɗin Mallam Sanda yana nufan su da kofuna biyu na shayin, ajiye mu su yayi a gaban su sannan ya juya don ƙarasa mu su taliyar, Alamz ne ya ɗauki shayin tare da kaiwa bakin shi, ba kamar yadda ya zata ba, don be zaci shayin ze yi daɗi ba, se kuma yaji shi saɓanin haka, hakan yasa ya dage yana ta sha yayin da Mazaa ko kallon shayin be yi ba hankalin shi na kan Mallam Sanda don yaga alamar shi ze iya faɗa mu su komai idan ya sani, gyara zama yayi sannan yace

“Baba ayi a gama mana don mu tafi mu fara aikin nan kar yamma ta yi mana a garin nan, don yanzu se a hankali, don naji ana bada labarin garin nan akwai ƴan garkuwa da kuma ma su sace mutane”, da sauri Baba ya juyo ya kalli Mazaa tare da cewa “kai ko yaro wa ya baka labarin nan?, ni ina garin ma amma ban sani ba”

“Nima naji ana faɗa ne kawai, ko ba haka bane Baba?”, “gaskiya bana ce ba, Ni baƙo ne a garin nan daga Niger nazo nan shekarata ɗaya da rabi anan amma ban taɓa ji ba”

“To shikenan Baba” cewar Mazaa

“Amma kwanan nan naji ana bada labarin an tsinta wata mata, amma ba’a kashe ta ba ita da ranta aka tsince ta” gyara zama Mazaa yayi don an zo wajen da yake so a zo, “to ya akayi da matar Baba?”, “Ehh to! gaskiya kar na muku ƙarya Nima naji ana faɗa ne wasu da suka zo nan shan shayi, to a yadda su ka ce Matar ma harda jaririyar ta, kuma yanzu haka ta na gidan wanda ya tsince ta, ana kiran shi Mallam Muhammad, tun daga nan ma ban sake jin labarin ba, ko an mayar da ita garin su ko tana nan”

“to Allah ya kyauta” Cewar Mazaa yana ƙarɓar ledar da Mallam Sanda ke miƙomai na taliyar, ƙarɓa yayi tare da cewa “Mun gode Baba” yace tare da nufar kofar fita.

Su na fitowa Alamz ya kalli Mazaa yace “kai mutumi na daɗi na da kai ka iya bugar ciki wallahi” dariya Mazaa yayi sannan yace “to tsaya wasa yanzu ba mun gano hanya ba, yanzu kawai gidan Mallam Muhammad za mu tambaya don tabbatarwa Ita ce ko ba ita ba” “Ehh haka ne” cewar Alamz yana ƙoƙarin kiran wani yaro.

Kiran yaron yayi suka tambaye shi gidan Mallam Muhammad, har kofar gida yaron ya kai su, ledar taliyar su ka miƙama yaron don da ganin shi kasan almajiri ne, sannan su ka samu wani waje suka zauna, don ganin masu shiga da fita a gidan.

Lokacin kuma su Hassana da Husaina suka fito bayan sun gama ƙaryata don zuwa gidan Mallam wajen ƙawar su Maryam don ba nisa kuma nan ne gidan wasan su, Su Mazaa suna kallon su kuma sun ga yarinyar da take goye a bayan su, kuma su na tunanin ita ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Rayuwa Ce 11

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×