Skip to content
Part 4 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Magana ya cigaba da yi khadija ta kyaleshi batare da tace komai ba, kallon ta yayi sannan yace khadija d’ago kai tayi ta kalle shi tare da amsawa yace meyasa bakya so na khadija, sunkuyar da kai ta yi don bata san me zata ce mai ba, dai-dai lokacin Al-amin ya dawo, har ya wuce ze shiga gida se yaga kamar khadija dawowa yayi ya kalla da kyau, ya tabbatar ita ce sallama yayi wa Alhmad sannan yace khadija d’agowa ta yi ta kalli yayan ta murmushi ne ya su’buce mata wanda ba ‘karamin kyau yake ‘kara mata ba kuma bata cika yin murmushin ba, idan kaga murmushin ta to suna tare da yayan ta, Ahmad sa’kin baki yayi yana kollon ta wanda ya lura tun zuwan yayan nata fara’a ya fad’ad’a a fuskar ta wanda hakan ba ‘karamin dad’i yayi mai ba, Al-amin ne ya matsa setin kunnen ta Yace

“ki tasaya ki sallame shi kafin kizo kin ji dariya ta yi tace to yaya.

Sallama yayi ma Ahmad ya wuce gida a bakin kofa ya tarar da inna ta na le’ke , abun dariya ma ya so ba shi amma yasan idan ya sa’ke yayi dariyar nan to yasan sauran, shigewa d’aki yayi yana ta dariyar ledan da ya shigo da ita ya kwance Tsire ne yaji kuli aciki ya zauna ya fara ci.

Khadija ko da yayan ta ya shige gida se ta koma ta had’e rai Ahmad murmushi yayi yace “gimbiya ta kin ‘ki kimin magana, ki yi min magana zanji dad’i arai na har yanzu ko uffan bata ce mai ba” se ma cewa da tayi zata shiga gida, Ahmad be yi fushi ba, Hannu yasa a Aljihu ya d’ebo kud’i masu yawa ya mi’ka mata ‘kin kar’ba tayi tare da ce mai ma “seanjima ta juya ta nufi gida, murmushi ya yi sannan ya shiga motar shi ya wuce gida.

Khadija na shigowa inna ta jawo ta har zuwa cikin gidan tace ke baki da hankali ne a miko miki makudan kud’i ki taho ki bar su sabida mugun ta bazaki kawo min ba,duka inna ta yi wa khadija tare da cewa idan ta ‘kara fita aka bata kud’in bata ‘kar’bo ba se ta kusa kashe ta, hakuri khadija ta bata sannan ta shige d’akin su, rarrashin ta Al-amin yayi har tayi shiru sannan ya mi’ka mata raguwar tsiren da ya rage mata kar’ba tayi ta fara ci sannan yace “khadija waye na ganku tare a kofar gida”

ta’be fuska ta yi tace “yaya wani ne wai sona ya ke yi d’an cikin gari ne ni dai gaskiya ba na son shi” “to mi yasa bakya son shi khadija?”

shiru tayi yace “khadija nasan bakisan miye so ba , ki saurari zuciyar ki abun da ta gaya miki game da shi ki fad’a min, khadija in dai kin yarda da shi halin shi da kuma mu’amalar shi, kuma ya na son ki da gaskiya ki yarda dashi khadija, khadija awannan rayuwar da muke ciki ba ni da burin da ya wuce naga auren ki domin shine kwanciyar hankali na, ke ma kuma Ina sa ran ki samu hutu a auren da zakiyi domin idan kika yi aure yanzu kin huta da dukkan abun da inna maryam ta ke miki zaki samu yancin kan ki domin aure shine cikar buri da kuma kamala na ‘ya mace, ajiyar zuciya khadija ra yi, sosai kuma maganar yayan nata yayi tasirin sosai a zuciyar ta, tabbas gaskiya ya fad’a mata, don ita kan ta bata san dalilin da ya sa bata son Ahmad ba, “to nagode yaya insha Allah zan fad’a maka”

“To kanwata kin ga da kinyi aure nima se nayi aure na ko dariya ta yi tare da rufe fuskanta domin kunya taji sosai.

‘Yar ‘karamar wayan shi Tecno da ya saya ne ya fara ringing duba wa yayi sunan khadija ya gani yana wayo a kan wayan da yake ya siya mata waya ita ma soyayya sosai suke yi har Mallam Bashir ma ya sani kuma yayi mai alkawarin bashi khadija, d’aga wayan yayi suna ta fira na soyayya khadija na zaune tana jiran ya gama wayan amma ta ga bashi da alamar gamawa se mamakin yayan nata ta ke yi shine da soyayya haka ko kunyan ta baya yi ko ma dai ya manta ta na d’akim ne , mi’kewa ta yi ta shiga uwar d’akan d’akin da yake a can ta ke kwana shi kuma yana falo, katifar maman su akai take kwanciya, shi kuma yana falo a tabarma, har bacci ya d’auke ta bata dena juyo wayan shi ba.

Shiko Al-amin sun dad’e suna waya da khadijan shi kafin su ka yi sallama ya kwanta.

Gidan su Ahmad

Ahmad tun da ya bar kofar gidan su Khadija, ko gidan kakan shi be koma ba direct gida ya nufa don wani irin da zuciyar shi ke yi mai kamar an d’aura mai dutse tsabar nauyin ya rasa me ke yi mai dad’i arayuwa.

Horn ya danna dai-dai lokacin da ya zo kofar gidan na su gida ne had’ad’d’e, kai da ganin gidan kasan Naira ta zauna ma mai wannan gidan domin gida ya had’u na karshe, Idi mai gadi ne ya bud’e mai gate d’in tare da mi’ka mai gaisuwa, d’aga mai hannu kawai Ahmad ya yi, Idi tun da ya ga haka yasan mai gidan nashi yau ba lafiya ba don idan ya shigo gidan yana perking wajen shi ya ke zuwa su gaisa sannan su sha fira sosai kafin ya wuce cikin gida amma yau ko gaisuwa babu kawai hannu ya d’aga mai.

Ko da ya shiga ‘katoton falon na su ‘kanwar shi maimuna kawai ya gani zaune ta na kallo a ‘katon Tv nasu wanda ka ke ganin mutane kamar za su fito, kallon ta yayi yace “ina momi?” cikin fara’a tace “sannu da zuwa yaya, momi sun fita ita da dad, amma sun kusa dawowa”, 3siter da ke gefe ya hau tare da kwanciya ya rufe idanun shi da hannun shi, maimuna ce tace “yaya akawo maka abincin ne?” “na koshi!” yace mata a takaice, tun daga nan bata sake magana ba don da ganin yayan nata tasan yana cikin damuwa, kuma ko me za tayi baze fad’a mata damuwar shi ba domin shi haka yake akwai hakuri da zurfin ciki, mi’kewa ma ta yi ta shiga d’akin ta domin ta kwanta bata jima da tafiya ba mom da dad su ka dawo, yayin da Ahmad har yanzu ya ke kwance a kan 3 siter momi ne ta karasa wajen shi tana fad’in “lafiya dai my son”, bud’e fuskar shi yayi sannan ya bud’e idanun shi da su kayi ja-jur yace “momi ba komai kawai kai na ke ciwo kuma nasha magani ma”, ya fad’i haka ne domin kar ta cigaba da tambayar, “to Allah ya kawo sau’ki”, dad ne ya amsa da “Ameen”, sannan Ahmad ya mi’ke ya nufi d’akin shi.

Ko da safiya ta yi khadija ta tashi kamar kullum ta yi aikin da duk ta san ta nayi ta da ma kunun da take zuwa tallan shi, yayin da Al-amim tun asuba ya ke barin gidan , don daga sallar asuba yake wucewa wajen aiki anan ma yake ‘karyawa, inna kuwa har yanzu ma bata tashi baccin ba wajen ‘karfe 8:15, sauri-sauri khadija ta ke yi don ta kusa makara wajen tallar ta don wataran ma 7:45 ma ta fita, se da ta kimtsa komai sannan taje d’akin inna ta tashe ta fitowa tayi sannan ta zuba mata wanda zata sha a d’an kofi ko sugar ma babu, cikin sauri khadija ta shanye kunun da ba abun da ze mata ma aciki, azuciyar ta,tace “idan na fita na sayi ko kosai ne acikin kid’in da yaya ya bani”, mi’kewa ta yi ta d’auki kunun ta fita zuwa bakin kasuwa inda su ke zama, kamar kullum, ta karaso kusa da ‘kawar ta Abu da suke zama waje d’aya, ita kuma kosai take siyar wa, gefen zanin ta ta kwance ta ciro d’ari biyar ta mi’kawa Abu tace “ta bata kosai na d’ari da Hamsim 150”, ‘kar’ba abu tayi ta irgo mata kosan har da gyara ta mi’ka mata, sannan ta zauna ta fara ci, duk da bata iya cin abu awaje ba amma hakanan ba yan da ta iya.

Kamar yadda ya saba yau ma ya shigo ‘kauyen inda yake tsayawa daga can gefe yana kallon ta domin baya gajiya da kallon sahibar tasa, ita ko khadija bata san me ake ba ta na nan tana cin kosan ta, kamar baza taci ba don guda d’aya se ta mai gutsira uku3 ko hud’u4, shi ko se kallon ta ya ke gwanin burgewa wani yaro ne yazo wajen ta siyan kunu inda ta ajiye kosan ta bashi.

*****

Dabara ce ta zo wa Ahmad ya kira wani yaro yace “kaje kace wa mai kunu can a kawo na d’ari biyu”, “to” yaron yace tare da nufan wajen, yace mata ta kawo kunun d’ari biyu_ zubawa tayi ta mi’ka mai, yace “a’a yace ne ki kawo se ki kar’bi kudin ki”, kamar ba zata je ba se kuma wani zuciyar tace mata taje domin yau ta na so ta siyar da kunun ta da wuri don kanta da yake mata wani irin ciwo.

mi’kewa tayi tace wa Abu “ga kunu na nan Don Allah”, “to ba damuwa” Abu tace sannan tabi yaron suka tafi har gurin mota, Ahmad bud’e motar yayi saura kad’an khadija ta zubar da kunun nan tsabar tsoro da mamakin ganin Ahmad, tace a zuciyar ta lallai wannan mutumin kamar maye da sanyin safiyar nan, muryar shi ta tsinta yana cewa “barka da safiya gimbiyata”, kallon shi ta yi ba tare da tace komai ba ta mi’ka mai kunu , Ahmad bud’e motar yayi ya fito kad’an yasa hannu ya ‘karbi kunun ya ajiye yace “nagode masoyiya” khadija badon bai bata kud’in kunun ba da ta juya ta tafi domin bata son kallon da Ahmad yake mata, “khadija!” ya kira sunan ta cikin sanyin murya yace “meyasa bakya sona khadija, kinsan yadda sonki yake wahalar da zuciyata, kinsan yadda nake kasa bacci da tunanin ki kuwa, kinsan yadda kunne na ke mararin son jin muryar ki amma baki min magana khadija , ko fad’a min kalma d’aya kiyi raina ze yi dad’i ko da zagi na ne ma kiyi”, khadija murmushi ne ya subuce mata,wai ko zagi na ne kiyi shine ya bata dariya amma ta dake tayi murmushi, dad’i Ahmad yaji sodai aran shi. Yace wannan ma kad’ai ya ishe ni yau zan wuni cikin farin cikin aduk sanda na tuna wannan murmushim naki, hannu yasa a aljihun shi, ya ciro dubu d’aya ya mi’ka mata kar’ba ta yi tace “ba ni da canji”, “ki ri’ke duka na baki” “a’a, bana so!, zan nemo canjin na baka”, “ki barshi kawai” “aa, ban yarda ba”, “to ki bani kunun na sauran canjin” “to” tace sannan ta nufi wajen kunun ta karo, kunun na ta ya rage saura na d’ari biyu dama duka na dubu d’aya da d’ari biyu ne 1200,

Ahmad ya kar’bi kunun yayi wa almajirai sadaqa, sannan yayi mata sallama ya wuce ita ma raguwar na d’ari biyun da ya rage ta yi sadaqa sannan ta kar’bi canjin ta na wajen abu ta saka d’ari biyu a cikin kud’in inna ta aje raguwar ta nufo gida don zuwa yanzu kan ta kamar ze tsage tsabar ciwo,

Da kyar ta ‘karasa gida, ta na zuwa ta yi sa’a ba inna agidan ta shige d’akin su ta kwanta, abu kamar wasa zazza’bi sosai ya rufe khadija yayin da har 1:30 inna bata shigo gidan ba, khadija ko sallah ta kasa mi’kewa tayi gashi ita kad’ai ne agidan, inna bata dawo gidan ba se 2:30, khadija ta shiga kwala wa kira khadija ta ke kwance ta juyo muryar inna na kira ta kasa amsawa, inna da ta gaji da kira se ta mi’ke ta nufo d’akin nasu salati tayi ganin khadija kwance zuwa tayi ta maka mata duka tace kina jin ina kiran ki tsabar iskan ci baza ki amsa ba kuma baza kizo ba, dakyar khadija ta bud’e baki tace “kiyi hakuri inna!, Wlh bani da lafiya ne”, “ko asibiti ne ma akan ki bani kud’i na”, ciro mata kud’in tayi ta bata inna ta mi’ke ta yi gaba abun ta, ba tayi maganar samo mata magani ba, yayin da khadija ke jin dad’i aranta ganin inna batayi mata maganar tallar rana ba.

Har akayi sallar magriba khadija na kwance tana fama da jiki yayin da inna tunda ta fita d’azu bata sake shigowa ba, a lokacin ne Al-amin ya shigo gidan ya tarar da khadija kwance sosai hankalin shi ya tashi ganin gudan jinin nashi ba lafiya, fita yayi da niyyar ya siyo mata magani, Ahmad ya gani tsaye a jukin motar shi a’kofar gidan Ahmad na ganin shi ya ‘karasa ya mi’ka mai hannu su kayi musabaha, cikin fara’a Ahmad yace “yayan mu ina zuwa haka?” ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “zanje cemist d’in can ne”, “Subnallahi!,waye ba lafiya”, Al-amin yace “wlh Khadija ce bata jin dad’i”, cikin tashin hankali Ahmad yace “me yake damun ta?, mamaki sosai ya kama Al-amin ganin tashin hankalin da ya gani ‘karara a idon Ahmad, ya tabbata Ahmad yana son ‘kanwar shi, domin ya kwanta ma Al-amin arai kuma yayi bincike akan shi ya tabbatar mutumin kirki ne, yasan khadija ma tana son shi kawai dai bata san so ba ne shiyasa, muryar Ahmad ne ya dawo da shi daga tunanin da yake yi yace “muje na rakaka asiyo mata maganin”, tafiya sukayi tare har zuwa chemist suka had’o mata magani yayin da su kayi sallama Ahmad ya nufi gida cike da tunanin masoyiyar tashi, da addu’ar Allah ya bata lafiya.

Ahmad Kan shine ya fara sara wa sosai, koda ya isa gida, momin shi ya tarar zaune a falo ita da maimunatu, gaisheta kawai yayi ya wuce d’akin shi, momi ta na lura da d’an nata yana cikin damuwa amma kuma tasan halin shi baze fad’a ba, mi’kewa tayi ta nufi d’akin nashi samun shi tayi ya kwanta agadon shi ko takalmi be cire ba, “Ahmad!” Ta kira sunan shi d’agowa yayi da sauri don jin muryar momin shi tare da zaunawa, momi ma waje ta samu ta zauna ta fuskan ce shi sannan tace “Ahmad me yake damun ka ne?” “ba komai momi” ya fad’a mata, “Ahmad kasan nafi kowa sanin waye kai, se yaushe zaka canja, baza ka ta’ba fad’a ma wani damuwar ka ba ko da nice, so kake na rasa ka ko, Ahmad,?, ka gaji da rayuwa dani ne ko?,”, momi na gaman fad’i haka ta mi’ke zata fita, cikin sauri yace “kiyi hakuri momi zan fad’a miki” dawowa tayi ta zauna sannan yace, “dama momi na samu yarinyar da nake so ne” murmushi momi ta yi na jin dad’i, tace “Alhamduliilah!, sannan yace “se dai momi wlh bata sona yarinyar se wahalar dani take”, murmushi momi ta yi sannan tace “wannan wacce yarinya ce wannan ta ke wahalar min da kai, a ina take?” ta’be fuska yayi sannan yace “‘yar garin su kaka ne”, dariya sosai momi tayi sannan tace “kace ‘yar garin mu ce ka samo, ba dai bata son ka ba ne kawai jan aji ne na yammata, don ba macen da zaka ce kana sonta tace bata son ka ba”,

Dariyar jin dad’i yayi yace “kai momi kina fasa min kai da yawa fa”, dariya momi tayi tace “bari dad ka yazo zan fad’a mai”, “momi kuma bata da lafiya wlh yanzu na baro gidan mun dawo siyo mata magani”‘ “subhanallahi!, me yake damun ta?”, “momi yace dai zazza’bi ne”, “to Allah ya bata lafiya” “Ameen” yace sannan momi ta fita zuwa d’akin ta.

Bayan Al-amin sunyi sallama da Ahmad ya shigo gida ya ba wa khadija maganin ya tambayeta taci abinci, “a’a” tace mai, komawa yayi ya siyo mata ya dawo taci ta sha maganin sannan ta koma ta yi kwanciyar ta, ita kad’ai tasan me take ji ajikin ta,

Koda safiya ta yi Al-amin yau beje wajen aiki fa don halin da take ciki, Ko mi’kewa ma ta kasa yi yayin da inna ke baccin ta batasan me akeyi ba, fita yayi ya siyo mata abun kari, ta d’an ci tasha magani,inna bata fito ba se 8:30, sannan ta fito mamaki ya kamata ganin ba abun da akayi a gidan, khadija ta shiga kwala wa kira, Al-amin ne ya fito yace mata “batajin dad’i”, “to sannu munafiki!, zaka ce batajin dad’i don kar taje talla ko?, to se taje”, shigewa d’akin nasu tayi ta tarar da khadija kwance se yanzu ma ta tuna da jiya tace mata bata da lafiya fito wa tayi ta hura wuta don samun abun da zata sa ka abaki domin ma yunwa ya ta so ta, se yau ta ga ranar khadija da yanzu ci kawai zata yi amma yanzu se ta d’aura.

<< Wata Rayuwa Ce 3Wata Rayuwa Ce 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×