Skip to content
Part 6 of 12 in the Series Wata Rayuwa Ce by Khadijah Ishaq

Bayan sun gama cin abinci su ka zauna su ka d’an ta’ba hira sannan su Ahmad suka mi’ke domin za su je gidan su Al-amin domin su fad’a wa inna halin da ake ciki, ko za ta zo ta kwana awajen ta, fita sukayi su ka bar su khadijan, bayan fitan su khadija tace wa Maimuna ta taimaka mata tayi sallah, taimaka mata ta yi don har yanzu ba ‘karfi a jikin ta, tayo alwala, maimuna ta shimfid’a mata d’ankwalin ta don ba Dadduma. A zaune ta samu tayi sallolin da ake binta da’kyar har magrib ta yi domin ta ji an fara kira.

Bayan ta idar ne kuma ta fara jin sanyi sosai domin ruwan da ta ta’ba gashi ba bargo se zanin asibitin, sallah ta idar itama sannan ta Kira yayan nata, tace mai su taho wa da khadija kaya da kuma bargo don yanzu har rawan sanyi ma take yi, to yace sannan ya fad’a wa Al-amin, lokacin ma sun iso gidan su Al-amim d’in, Ahmad ne ya tsaya a waje yayin da Al-amin ya shiga cikin gidan taradda d’akin inna yayi a rufe har da kwad’o ma, mamaki yayi wannan matar kuma in ta je , yayi tambayar da ba shi da amsar ta fitowa yayi yace wa Ahmad “bata nan ga kofar ta ma arufe, amma bari na tambaya ma’kota ko ta na can”, gidan ‘kawar ta Ladidi ya nufa wanda ba nisa da gidan nasu shiga yayi da sallamar shi ya gaishe ta sannan yace “inna bata zo nan ba?” kallon shi ta yi cikin mamaki sannan tace “Dama bakusan da tafiyar ta ba, ai d’azu ta zo tayi min sallama za ta garin su ana bikin ‘kanin ta tace min ma zata yi kwana4”, mamaki ne sosai ya kama Al-amin, sallama yayi ma Ladidi ya fito zuciyar shi se tafasa ya ke yi, “a duniyar nan yanzu idan aka ce ba ka da uwa ka rasa rabi da kwata na farin ciki, tun bayan rasuwar Mahaifiyar su su ke fama da ‘kalu-bale kala-kala na rayuwa ko se yaushe za su ji dad’in rayuwar su, inna maryam da ace ‘yar ta ce bata da lafiya, ko makawa babu baza ta tsalleke ta ta tafi wani biki ba, amma tsabar rashin imani amma ba komai zamu cigaba da hakuri, Allah ya duba mu.”

Maganar da Al-amin ya ke yi kenan acikin zuciyar shi har ya ‘karaso wajen Ahmad, Ahmad kallo d’aya yayi mai yasan akwai damuwa domin yanda fuskar shi ta canza lokaci d’ay, fad’awa Ahmad duk abun da Ladidi tace yayi, shi kan shi Ahmad, abun ya ta’ba mai rai sosai, Al-amin ne yace “bara na kwaso mata kayan” sannan ya fita ya nufi cikin gidan, d’akin nasu ya shiga ya bud’e kayan khadija duk bana arzi’ki sosai se wasu guda uku, wanda duka ma shi ya d’in ka mata da sallah, d’aya atamfa roba ne amma sabo ne, se kuma wata shadda da ya musu tare shine ma mai d’an tsadan, se kuma atamfa Abc guda ukun ya d’ebo mata ya zuba a leda sannan ya fito ya d’auki bargon shi da yake rufa dashi da yake sabo ne be dad’e da siyan shi ba saboda sanyi ya kusa yana da niyyar ma itama khadijan ya siya mata, tunda wanda suke rufa tun na maman su ne da ta bari.

Fitowa yayi da kayan suka shiga mota su kayi asibitin suna shiga seda suka tsaya su kayi sallah a masallacin da ke asibitin sannan su ka shiga ciki har zuwa d’akin da khadijan ke ciki, tana kwance se rawar sanyi take yi bargo Al-amin ya ciro ya rufa mata sannan ya fita domin kiran likita, minti3 bayan fitan shi su ka shigo tare da likitan ya dubata sannan ya sa mata ruwan sannan yace “kar ta ‘kara ta’ba ruwan sanyi”,. “to” su ka ce sannan ya fita yace “nan da 11:00 ze dawo domin ya cire mata lokacin ya ‘kare”, har bayan isha’i su maimuna su na asibitin, maimuna ce ta fita waje ta kira momin ta, bayan ta gaishe ta sannan tace “momi zan kwana a asibitin don Allah”, momi ce tace “su ‘yan uwan ta da ko tsabar karere ne maimuna” “a’a momi wallahi yarinyar marainiya ce bata da kowa se yatan a hannun kishiyar maman su suke to wallahi bata son su, tasan ba ta da lafiya amma wallahi momi ta tafi biki bata ma a garin ga baban su ma baya garin”, sosai momi ta tausaya musu, sannan tace “maimuna kinsan dad ki baze bari ki kwana a wani waje ba ko?,ki dawo gida idan yaso gobe se nayi masa magana yarda ze fahimta se ki kwana awajen ta” “to momi” tace sanna su kayi sallama, ta koma d’akin.

Mom ta kira Ahmad ta shaida mishi su dawo gida, don haka wajen ‘karfe 9:00 su ka shirya barin asibitin maimuna ce ta had’a komai data zo dashi amma tabar snak d’in da kuma drinks sannan su kayi sallama su ka nufi gida akan gobe za su dawo, sosai Al-amin yayi musu godiya don ba abun da ze biya su dashi,

Yaji dad’in had’uwa da su, kuma yana ji a jikin shi Allah ne ya turo musu Su Ahmad a rayuwar su domin su taimaka musu, yau da basu da be san ya ze yi ba tun daga kawo khadija asibiti, duk da yana da kud’in da ze yi komai, amma kuma duk abun da yaje ze biya se ace Ahmad ya biya sosai Ahmad ya kwanta mai arai, domin yana ganin tsantsar kaunar ‘kanwar shi a kwayan idon Ahmad.

Yana cikin wannan tunanin Har bacci ya d’auke shi domin Yau ya gaji sosai.

Su Ahmad ko da su ka koma gida a falo su ka samu su momi da dadi, su na hira, gaishe su su kayi sannan su ka musu sannu da zuwa, dad ne yace babana ya mai jiki, sosa kai yayi, yace “da sau’ki dad”, “yaushe Baban nasu ze dawo se muje nema maka auren ta” murmushi Ahmad yayi na jin dad’i sannan yace “dad ban sani ba amma zan tambayi yayan nata gobe”, “to” yace sannan yace “Allah ya dawo dashi lafiya”, dukan su suka amsa da “Ameen”, maimuna ce ta ce “mom baki ganta ba wallahi ‘yar kyakykyawa da ita gata ‘yar dai-dai ce”, murmushi momi ta yi tace “gobe zan je na gaishe ta Insha Allah, ku tashi kuje ku kwanta don nasan kun gaji sosai” “to” suka ce sannan kowa ya mi’ke ya nufi d’akin shi, Ahmad yana shiga ruwa ya watsa sannan ya sa ka kayan baccin shi, ya kwanta amma baccin be zo ba se tunane-tunane, yake yi.

Maimuna kuwa ta na shiga d’aki kaya kawai ta canza ta kwanta don ta gaji, Ko minti10, batayi da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita.

Washe gari tun da asuba Al-amin ya tashi ya nufi masallaci bayan ya dawo ne ya zauna, khadija har yanzu bata ta shi ba tana bacci, tunani yake me zai siyo musu ku karya ga ruwan wankan da khadija zata yi be san a ina ze samo ba, ko ya je gida ne ya dafa ruwan ya kawo, to idan ya dafa ma a me ze zuba yayi tunani, bashi da wata mafita mi’kewa yayi ya nufi waje domin samo musu abun da za su karya domin yanzu kusan ‘karfe 8:15, ne yana fitowa wayan shi ta fara ringing yana dubawa ya ga Ahmad ne,ɗaukan watan yayi su ka gaisa ya tambaye shi mai jiki yace “da sau’ki, sannan yace “kana ina ne?” “Gani na fito waje ne zan siyo abu”, “mai zaka siyo?”, “abun kari” yace mai, Ahmad ne yace “Don Allah kar ka siyo kome ga munan a hanya da maimuna, ka ji “to” yace sannan ya koma cikin d’akin ya ga khadija ma ta tashi, gaishe shi tayi ya mata sannu da jiki sannan ya zauna, ba’a fi minti 15, se ga Ahmad da maimuna sun shigo, Ahmad rike da flas, da leda ahannun shi, Maimuna ma flas ne a hannun ta da kuma kula Babba, gaisawa su kayi sannan, maimuna ta ‘kara so wajen khadija tace “anty ta shi ki wanke baki ki karya”, taimaka mata tayi ta tashi ta shiga bayin ta wanke baki sannan ta fito ta zauna kofuna biyu maimuna ta d’au ko ta had’a musu tea sannan da d’auko flet da zuba musu chips d’in dankalin turawa da kwai da buredi ta ajiyewa wa khadija d’aya Al-amin d’aya godiya su kayi, sannan maimuna ta ce “anty mu yau ina da lecture za ni makaran ta ne ma yanzu nace se na biyo da duba ki sannan, 9:00 zamu shiga karatu, amma anjima zan dawo”, “to” khadija tace sannan ta ƙara cewa “ga ruwa nan a Flash se ki yi wanka” kallon Ahmad ta yi tace “yaya muje ka ajiye ni”, “to je ki gani nan zuwa”, “to” tace sannan ta yi hanyar fita waje, Ahmad yace wa Al-amin “Bari na ajiye ta a school na dawo”, “to adawo lafiya”, yace sannan Ahmad ya fita, a wajen motar ya samu Maimuna na jiran shi ya shiga kai tsaye su ka wuce makarantar ya ajiye ta sannan ya wuce ya ce idan kin tashi ki kira momi ta turo mai gadi ya d’auke ki, “to” tace sannan ta wuce ciki.

Shi kuma direct asibitin ya dawo shima lokacin da ya zo Likitan na saka mata ruwa, ya gama ya fita, su ka zauna su na fira yayin da Ahmad ke tambayar shi yaushe Baban su ze dawo, yana so ya turo ne Al-amin yaji dad’i sosai aran shi se de besan yaushe baban su ze dawo ba don har ya dawo ya koma wani lolacin baya sani, Kallon Ahmad yayi sannan yace “gaskiya bansan ranar da ze dawo ba amma da zarar ya dawo zan fad’a maka” “to nagode sosai” Ahmad yace, wayar Ahmad ne ya fara ringing ko da ya du ba momin shi ne d’aga wa yayi su ka gaisa sannan ta tambaye shi wani asbiti ne ya mata kwatance bayan sun gama wayar ne Ahmad ya kalli Al-amin yace “ga momin mu nan zuwa ta gaishe da khadija” sosai Al-amin ya ke mamaki momi da kanta, minti15, momi ta kira shi ta fad’a mai ta iso fitowa yayi ya shigo da ita kujera ya matso mata da shi ta zauna, Al-amin ne ya du’ka har ‘kasa ya gaida ita ta amsa cike da fara’a tace “ya mai jiki?”, “da sau’ki” yace, sannan yace “momi mun gode sosai da d’awainiya”, murmushi ta yi tace “kar ka ‘kara min godiya don yanzu mun zama ɗaya kuma kaman yara na na ɗauke ku”, “to” yace sannan ta juya ta kalli khadija da ke bacci lokaci d’aya yarinyar ta shiga ranta, momi ta d’an dad’e a asibitin sannan ta tafi gida yayin da khadija tana jin su kawai bacci ‘karya ta ke don kunyar momim take.

Sosai ta ke mamakin Ahmad daga had’uwa har kowa na gidan su yasan ta har sun zo gaishe ta, gaskiya a gaishe shi, tace acikin ranta.

Maimuna bata dawo ba se karfe hud’u 4:00, ta zo asibitin yayin da yau ita ta kwana da ita.

Kwanan su uku a asibitin aka sallame su, sun dawo gida aranar kuma khadija budurwar Al-amin ta zo gaishe ta, so biyu kenan ta zo, ta je asibiti ma ta gaishe ta, ranar ne kuma inna maryam ta dawo ita ma, le’kowa d’akin ta yi tace “to munafukai wato kun gama yad’a ni a gari bata da lafiya na tafi biki ko?, to naje ko asibiti ne akanta ba abun da ya shafeni bane”, sannan ta fice a d’akin, Al-amin ne ya fito waje don ya siyo musu abinci turus yayi da mamaki ganin baban su wanda rabon da ya ganshi ma ya manta ya fito daga d’akin inna gaba d’aya ya lalace yayi ba’ki shida yasan baban su fari ne, cikin sauri ya ‘karasa wajen baban nasu ya gaishe shi, ga mamakin shi se ya wuce bai amsa ba, bin shi yayi yana magiya “don Allah Baba kayi hakuri ka saurare ni Don Allah akwai maganar da zan fad’a maka ne don Allah ka saurareni” bin shi yake yana magiya yayin da baban nasu yake ta tafiya seda ya isa kofar gidan sannan ya tsaya ba tare da ya juyo ba Yace fad’i maganar ka, Al-amon cikin sauri yace “Baba dama akwai wani ne da yake neman auren khadija, shine yace yana so ya turo, asatin nan shine nace zan fad’a maka”, shiru Baban yayi be yi magana ba har tsawon lokaci Al-amin ne ya d’ago ya le’ka fuskar baban nasu ga mamakin shi hawaye ya gani yana bin fuskar shi, Yace “Kace su zo ranar Juma’a, amma ka tura su wajen Abokina mallam Bashir domin ze iya aurar da ita bayan amintar da ke tsakanin mu d’an uwa na ne jini, ni gobe ma zan koma lagos ina muku fatan Alkhairi ‘ya’yana”, sannan ya fice daga gidan , tsayawa Al-amin yayi ko mi’kewa ma ya kasa yi yana du’ke a wajen wasu zazzafan hawaye na ba’kin ciki su ka wanke mai fuskar shi ya dad’e a wajen yana hawaye sannan ya fita ya siyo musu abincin da zasu ci ya koma gida , koda ya shiga d’akin khadija na sallah ajiye mata abincin yayi sannan ya fita, ta na idarwa ta d’auka ta fara ci, har ta gama be shigo gidan ba.

Bashi ya shigo gidan ba se bayan la’asar, zama yayi ya d’auki abincin na shi ya fara ci, “khadija!” Ya kira sunan ta, khadija dake uwar d’aka tana kwance ta fito jin kiran yayan nata, ta zo ta zauna kusa da shi, yace “khadija kina son Ahmad?”, tambayar ta zo mata a bazata, rasa amsar da zata ba shi ta yi se ta sunkuyar da kanta, ya ‘kara cewa, “Khadija Ahmad ze zo neman auren ki a cikin satin nan”, d’ago kai ta yi cikin sauri tace “yaya da wuri haka, ba mu gama sanin wa ye shi ba”, Al-amin ne yace, “khadija wani irin sani kike so kiyi mai, ina so ki gane Ahmad na yi bincike akan shi mutumin kirki ne, bayan nan kinga lokacin da ki ka kwanta asibiti fa har momin shi fa ta zo gaishe shi ga ‘kanwar shi har kwana ta yi awajen ki, khadi na na fahimci wa ni abu d’aya Ahmad yana son ki kuma indai kika aure shi na tabbatar miki baza ki sake kuka ba, da yardar Allah”, “to yaya Allah yayi mana za’bin alkhairi, ko da ace ba Ahmad ba ko waye ka za’ba min zan yarda da shi yaya domin yanzu kai ne min uwa, sannan uba, dole nabi za’bin ka” “khadija idan baki son shi ki fad’a min”, “ina son shi yaya ta fad’a tare da rufe fuskarta” murmushi yayi dai-dai nan kuma ya gama cin abinci, ya mi’ke domin yana so yaje gidan mallam yayi mai magana.

Kai tsaye gidan mallam Bashir ya nufa a kofar gidan ya tsaya domin gidan surukan shi ne, yana jiran ya fito, aiko ba’a jima ba ya fito daga gidan gaishe shi yayi sanna su ka zauna a wani dakali dake ‘kofar gidan, Al-amin ne ya zayya ne mai komi ya ‘kara da cewa jibi ne zasu zo, “to Allah yasa ayi damu” mallam yace Al’amin yace “Ameen” sannan yace “mallam se kuma maganar kud’in da nake tarawa awajen ka ina so na ‘kar’ba domin nayi hidimar bikin khadija”, “to ba damuwa duk san da kake bu’katar kuɗin ka ka yi min magana zan baka ai hakkin ka ne” godiya Al-amin yayi sosai sannan ya mi’ke ya nufi gida.

Bayan sallar magrib aka aiko kiran khadija inji Ahmad Lokacin Al-amin yana gida shi ya fara fita domin su gaisa daga nan ya wuce masallaci, inna ku wa da har ta le’ka ta gan shi gargad’i tayi wa khadija tace “saura yauma ya baki kud’in ki ‘ki ‘kar’ba wlh ni da ke ne”, fita khadija ta yi ba tare da tace wa inna komai ba, direct wajen motar shi ta nufa inda yake atsaye, tun farkon had’uwar su bata ta’ba ganin shi da ‘kananan kaya ba, se yau sun bala’in masa kyau, ‘karasawa tayi ta gaishe shi sanna tace “ya maimuna?”, sosai ya ji dad’in yadda ta tambayi ‘kanwar na shi, yace “tana lafiya, tana gaishe ki ma”, “to ina amsawa”, tace fira kad’an su ka ta’ba inda ya ‘kara fad’a mata magabar ze turo magabatan shi jibi, tace “ai yaya ya fad’a min ma”, yace “ba wannan nake son ji ba, kin amince zaki aure ni?” rufe fuskar ta ta yi da hijabin ta, murmushi yayi yace “ban gane hakan me yake nufi ba”, “to ka tambayi yaya na ze fad’a maka” “to shikenan Allah yasa na ji Alkhairi, bara na zo na koma gida” wani leda ya ciro daga motar shi ya mi’ka mata ‘kin ‘kar’ba ta yi tace “seda safe”, sannan ta wuce zuwa gida, Ahmad wani yaro ya kira acikin yaran da su ke wucewa ya bashi ledar yace ya shiga gidan nan ya bawa wanda ta shigo yanzu kar’ba yayi ya nufi gidan, Khadija na shiga inna ta fara sababin nata kenan ta jiyo sallamar yaro ledan ya mi’ka yace “gashi wai abawa wanda ta shigo yanzu”, da sauri inna ta ‘kar’ba tace “kaje kace an gode”, “to” yace sannan ya juya ya fita, inna ce ta kalli khadija tace “to mai ba’kin hali baza ki ‘kar’bo ba don karki ba ni ko, tsabar mugunta”, bud’e ledar inna tayi kayan kwalliya ne kala-kala aciki da mayuka da sabulai Harda kwalin waya, gefe kuma kud’i ne wanda da gani za su haura dubu ashirin kud’in kawai inna ta d’auka tare da dungurewa khadija sauran tace “ga shi kici gantalin ki da su”, ta wuce d’aki ta na washe baki,khadija ma d’akin ta wuce ta zazzage kayan, kayan kwalliya ne sosai se kwalin coculate irin Babba nan se kwalin waya, ‘kirar iphone, aje kayan ta yi ta mi’ke domin yin sallar isha’i don tun tana waje taji an fara kira.

******

Al-amin se da yayi sallar isha’i sannan ya nufo gida yana zuwa d’akin su ya shiga khadija ce ta nuna mai kayan da Ahmad ya kawo mata, sosai Al-amin ya sa ma kayan albarka.

Washe gari gidan su Ahmad se shirin zuwa gidan su khadija suke inda Ahmad ke murna kanan an saka shi a aljanna.

Kamar yadda aka yi ranar juma’an su ka je gidan su khadija in da aka tsaida maganar aure wata uku masu zuwa, Al-amin ya samu inna ya fad’a mata domin fita hakkin ta, yayi mamakin ganin inna ta yi murna da hakan, abun da ya kawo kawai yasan inna da son kud’i ko don kud’in Ahmad ne yasa.

Bayan saka ranar khadija inna ta dawo da d’aura mata talla acewar ta da kud’in za ta yi mata kayan d’aki, hakan be yi wa Al-amin dad’i ba, amma yayi hakuri don a Gangara kwana nawa ne zata bar mata gidan, wata rana khadija taje talla su ka had’u da Ahmad sosai ya nuna ‘bacin ran shi akan tallar ko da can baya so ya gan ta tana talla, har wajen inna ya je ya fad’a mata ba ya son tallar nan ba kunya inna tace mai to idan batayi tallan nan ba dame kake so nayi mata kayan d’aki, Ahmad ya shaida mata shi matar shi yake so a kawo mai ko ba ko da tsintsiya ce, ba inda innan ta iya don dole ta dena d’aura ma khadija tallan, Ahmad ya samu Al-amin ya shaida mishi kar ya wahalar da kan shi wajen kayan d’aki da komai kawai matar shi yake so don d’akin ta yana cikin gidan su tuni ma an zuba komai, don ko an siyo ma ba wajen zubawa, sosai Al-amin yayi godiya.

Al-amin ya kar’bi kuɗin shi na wajen mallam sunyi yawa sosai dubu d’ari ne kawai babu a millon d’aya, fili ya siya ya fara gini agarin na su amma can da nisa sosai daga gidan su sosai aikin ginin shi ya kankama, yau saura sati uku bikin khadija ba wani shiri da suke yi, inda kuma yau ne aka saka ranar khadija da Al-amin wata3 su ma domin saura kad’an Al-amin ya gama ginin shi..abu kamar wasa yau bikin khadija saura kwana biyar inda agidan su Ahmad ake shiri sosai kasancewar ba’a ta’ba biki agidan ba sosai yan uwa su ka cika gidan, yau ne kuma za’a kawo lefe inda su ka shirya za’a kai gidan mallam Bashir, da yamma ƴan kawo lefe su ka kawo akwatina goma sha biyu ne 12 ko wanne cike yake da kaya mutane se zuwa su ke kallon lefen khadija su na san barka domin se makiyi ze ce kayan basu yi ba, ana biki saura kwana uku kuma aka kawo sadakin khadija dubu d’ari biyar Al-amin ya damƙawa khadija a hannun ta, yayin da tace ta bashi du ka da wasu kud’i ma da Ahmad yake bata duk ta had’a ta bashi, tace ya ‘kara a hidiman auren shi, sosai Al-amin yaji d’ad’in abun yayi ta saka mata Albarka don shi kan shi yasan yana bu’katar kud’i.

Rana bata ‘karya sede uwar d’iya ta ji kunya yau ce aka d’aura auren khadija muhammad sani da angon ta Ahmad Ibrahim wanda aka d’aura a masallacin juma’a na garin Adamawa sodai jama’a su ka halarci d’aurin auren, gidan su khadija Al-amin ya bawa inna kud’i da za’a yi abincin biki inda akayi girki mai rai da lafiya mutane kuma duk sun shigo yan’uwa da abokan arziqi khadija tun da akace an d’aura auren ta ke kuka sosai anyi lallashin amma ta ‘ki yin shiru haka su ka gaji su ka barta.

Ba’ayi wani abu ba se walima da aka shirya a gidan su Ahmad bayan an kai amarya ‘karfe 4:00, motar d’aukan amarya su ka zo motoci ne guda takwas ai ko an kwashi mutane duk maƙota ne da ‘yan uwa da abokan arziƙi da’kyar aka raba khadija da yayan nata don yadda ta rike shi ta na ihu, duk dauriya irin ta Al-amin se da ya zubar da kwalla daƙyar dai aka saka khadija a motar se gidan suAhmad.

Gida ne babba sosai had’add’e sannan part uku ne agida kuma ko wanne sama da ‘kasa ne, d’aya shine na khadija wanda cike yake dakaya sosai se d’aya shine na su momin shi d’ayan kawai anyi shi ne shima akwai komi acikin shi, nan aka sauki ya d’aukan amarya duk yawan su suna shiga tsab ya d’auke su kowa ya samu wajen kwanciya, sun sha walima sosai anci ansha an koshi ba wanda ze ce yaje wajen be ‘koshi ba Bayan an tashi Su ka koma masaukin su duk zaton su ma nan ne d’akin khadija se yaba kyau d’akin su ke yi, abinci aka ‘kara kawo musu a ‘katon kula masu mugun ci su ka ‘kara, wa su kuma sun ‘koshi, khadija nacan wani d’aki ita da khadija budurwar Al-amin har yanzu kuka ta ke se lallashin ta takeyi amma ta’ki, maimuna ce ta shigo part d’in bayan ta gaishe su ta tambayi amarya aka nuna mata d’akin da ta ke, d’akin ta nufa ta na zuwa ta rungume khadija, ta ce “antyn mu nazo taya ki kwana ne” murmushi khadija ta yi ta goge hawayen dake fuskan ta, tare su ka kwana da mainunat.

Washe gari, Bayan la’asar duk wad’an da su ka ka wo amarya su ka yi shirin watsewa, an cika musu ciki da aljihun su don Mom se da taba ko wa turmin zani, dad kuma ya bi kowa da dubu biyar-biyar, sosai su ka yi farin ciki, kowa yana addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya aka kawo mota ta mayar da su gida, aka bar khadija ita kad’ai ta na d’akin momi ma ita da Maimunat su na kallo, ta na jin kunyar momi sosai amma yanzu kunyar ya fara raguwa Don momi ta na jan ta ajiki sosai, ta na nuna mata so.

Haka dai rayuwa ta ci ga ba tafiya wa khadija cikin jin dad’i don yanzu ta manta wani rayuwar wahala, domin so sosai ake nuna mata agidan, tun daga kan Ahmad, maimunat, Momi da dad, ga sauran ‘yan uwa ko wa na son ta, hakan yasa ita ma ta da ge wajen kyautata musu, acikin wata biyu da auren khadija ba za ka ta’ba ga ne ita ba ce idan ba farin sani ka yi ma ta ba, ta canza ta yi haske sosai da ma fara ce, fatar ta tayi kyau se she’ki ta ke yi, gashi ba aikin da take yi domin momi ma ta hana ta sede masu aiki su yi wataran momin da kan ta ta ke shiga kicin ta yi girki da yawa ta aiko musu part d’in su, koda yaushe ta na part d’in momi don yanzu ma ta dai na jin kunyar momi don ganin ta ta ke kanar uwar ta, momin ma tamkar ‘ya ta d’auke ta bata banbance tsakanin su da maimunat dad ma haka, za su zauna su yi fira sosai kafin su koma part d’in su.

Yau saura sati d’aya1, bikin Al-amin da khadija, se shirye-shirye ake yi, khadija ma ba’a barta abaya ba don shiri ta ke wa yayan nata sosai, momi da dad sun bata kud’i masu yawa gudunmawar bikin, ga wasu ‘yan uwa ma duk sun bata, Ahmad kuma yace ze bawa Al-amin da kan shi.

Yau takama Laraba bikin saura kwana3 khadija ta shirya za ta je gidan nasu maimuna zatayi mata rakiya, Direban gidan ne ya kai su don Ahmad ya tafi wajen aiki, ta zo ta samu yayan nata yana had’a kud’in siyo kayan lefa ta bashi wanda ke hannun ta sosai yaji dad’in hakan yayi farin ciki ganin ‘kanwar nashi cikin kwanciyar Hankali, rakata gidan na shi yayi, gidan ya had’u sosai plat ne yayi mai d’an girma, yayi kyau sosai yayin da yau za’a zo ayi jere, sosai khadija ta yi murna ganin d’an uwan nata ya dage yayi irin wannan gida haka, gida su ka dawo ta shiga d’akin Inna ta gaishe ta, ta amsa ba yabo ba fallasa, ta juya zata fita inna ce tace ke haka ake zuwa ganin gidan ba komai ko dai bakin halin ne ya tashi baza abani komai, khadija ta rasa me zata ce gashi duka kud’in hannun ta ta bawa yayan ta, ta ce inna ya na d’akin mu bari na ‘karbo, washe baki ta yi tace ko kefa, wajen maimuna ta je tace ta ara mata kud’i ko 20k ne tace “wlh ba kud’i cash a hannun ta sede su je pos su ciro” “to” tace don baza ta iya komawa wajen yayan ta tace ya bata kud’,in ba pos su ka je ta ciro 25k su ka dawo ta bawa inna washe baki tayi ta na murna ta ce “ko ke fa zauna bara na zubo muku abinci kuci” ba musu khadija su ka zauna taliya ce ta zu bo muzu mai da yaji, khadija akoshe ta ke amma don karta bata kunya se ta juya ta fara ci loma d’aya ma da’kyar ta had’iye don ta taliyar ta nuna sosai harta fara narke wa gashi salam kamar ba komi aciki se uwar ya ji, gashi yayi mata jagwal abaki, maimuna ko duk yanda ta so ta ci taliyar ta kasa don da ta kalle shi ma take jin tashin zuciya da’kyar khadija ta yi loma uku ta ce “inna mungode mun koshi, bari mu wuce” “to a gaida gida” su ka fita, su na fita inna ta d’auki kayan ta ta juya ta fara saka loma dama bata so su ci ba shikenan ta gama dafawa yanzu za ta ci da sun ciye se ta kara kashe kud’i ta fad’a aran ta tace ai ya ‘kara auki.

Se da yamma su khadija su ka tafi gida don seda su ka tsaya su ka ga lefe, se son barka kaya sunyi kyau sosai Al-amin ya dage ya zu ba mata kaya akwati Shida ne ko wanne kuma akwai kaya sosai.

Yau juma’a, yau aka d’aura auren Al-amin da amaryar shi khadija akan sadaakin dubu d’ari da Hamsin, amarya ta tare a sabon gidan ta.

Bayan wata shida, zaman lafiya sosai khadija da Al-amin suke yi haka ma Ahmad da Khadija, khadijan Al-amin ta na da ciki ma yanzu.

Bayan shekara2 khadija ta haifi yaron ta namiji wanda yanzu ma har yayi wayo su na kiran shi da Abubakar, inna yanzu bata da aiki se yawan zuwa gidan Al-amin don kwad’ayi, ta na gani irin jin dad’in da su ke ciki don Al-amin yanzu kud’i sun zauna mai sosai don Ahmad ya bashi jari yayin da mallam ma yace ya bud’e wajen kan shi ya barshi da yaran, ya bud’e wajen aikin nashi yayin da ya zuba yara don shi yanzu sana’ar sai da atamfofi yake yi yana zaman shago ne yabar yara acen wajen don kwararru ya d’auka.

Ganin irin jin dad’in da khadija ke ciki yasa ladidi ta zowa da inna maganar a had’a auren Al-amin da ‘yar ta safiyya, domin yanda za su rin’ka samun kud’i inna ta aminta yayin da ta fad’a wa Baban su Al-amin d’in don tasan idan shi yayi wa Al-amin magana ze iya yarda ya aure ta.

Haka dai da suka. Rufa tare da taimakon bokan nasu da kuma Baban su ya auri safiyya, safiyya ta kasance yarinya mara kunya da kamun kai, kowa yasan ta a’kauyen da rashin kunya, tana da kayau dai-dai gwargwado kasancewar ta bafulatana gaba da baya, amma khadija ta fi ta kyau sosai, khadija bata nuna wa Al-amin kishinta amma abun ya mata zafi, ganin shekarar su uku da aure ya ‘kara aure kuma, haka ta daure ta na hakuri da halin safiyya, bayan shekara d’aya da auren su da safiyya ita ma ta haifi yaron ta namiji, yayin aka saka masa sunan mahaifin Al-amin muhammad sani, yayin da safiyya kuma tace lallai se dai asa sunan mahaifin ta shima muhammad ne amma Buhari ake kiran shi, haka Al-amin yayi hakuri ya maida shi Muhammad Buhari.

Yaron khadija lokacin yana da shekara hud’u sosai yayi wayo, gashi ya biyo kyau iyayen shi.

Bayan shekara uku, ba wanda ya sake haihuwa acikin matan Al-amin yaran shi se wayo su keyi sosai yayin da ya ke yawan kai su gidan khadija domin su gaishe ta khadija har yanzu bata haihu ba, yau shekara shida kenan da auren su, Hakan bai damu kowa a familyn ba Hasalima har yanzu tsantsar so su ke nuna wa khadija, acewar momi ko khadija bata haihuba, ai ta samu ‘ya tunda tamkara ‘ya ta d’auke ta.

Abubakar yana da shekara shida, yayin da Buhari yake da shekara 3 alokacin ne kuma aka saka su makarantar boko sosai Abubakar ya ke karatu yayin da Buhari wasa ke cin ranshi.

Bayan shekara4, Abubakar yanzu yana primary4, shi kuma Buhari yana primary2 amma ba abun da yake ganewa sede wasa yana da wani aboki mai suna iliya shi ma yaro ne mara ji sosai, Abubakar sosai ya dage yake karatu don duk jarabawa shike zuwa na d’aya idan ya dawo makaran ta kuma se yaje shagon baban shi ya taya shi zama, yayin da buhari kuma sede ya tafi wasa wajen abokai, shi Abunakar abokin shi d’aya Ummar shi ɗan Kaduna ne an kawo shi wajen anty shi ne Adamawa yana karatu wanda halin su ya zo d’aya ajin su ma d’aya ne sosai su ke karatu d’aya na taimakon d’aya.

Bayan sheka 2 Abubakar ya gama primary yayin da sunan shi da na abokin shi su fito a wad’an da gwannati ke d’iba su biya musu makaran mai tsada ko da Abubakar ya fad’a wa Baban shi sosai ya ji dad’i.

Bayan wata d’aya za su wuce kano don yi karatu don bording school ne mai tsada wanda se ka cika d’an masu kud’i za a gan ka awannan makarantar, sosai su ka dage suna karatu, yayin da Buhari tun da Abubakar ya bar makarantar se abun nashi yaci gaba don yanzu ma se yayi wata d’aya be je ba idan an tura su sede su tafi yawo shi da iliya ba inda basu sani ba a garin su ne zuwa rafi wanka da dai sauran su, ko da aka kawo wa Al-amin ‘karar Buhari baya zuwa makaranta sosai yaji haushi ya yi ma buhari dukan tsiya, amma se safiyya ta fara kuka ta na fad’in ai dama ba son ta ake a gidan ba, amma shi Abubakar da ya ke uwar shi ‘yar gwal ne ba’a ta’ba dukan shi ba se nata.

<< Wata Rayuwa Ce 5Wata Rayuwa Ce 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×