Bismllahir Rahmanir Rahim
A ranar nayi kuka tamkar numfashi na zai bar gangar jiki na, nayi baƙin ciki mara musaltuwa a daren nan sai naji dama ban faɗa ma sa baki na ba, jingina nayi a jikin bangon ɗakin mu haɗi da kifa kaina tsakankanin cinyoyi na, ina sakin wani wani marayan kuka cikin sarƙewar murya nace" yaushe zan huta ne? yaushe zanyi farin ciki? me yasa Mama ta tafi ta barni? yanzu in Kawu bai yarda dani ba ina zan kama?"
A hankali naji a turo ƙofar ɗakin, cikin sanɗa ta shigo kamar ɓarauniya. . .