Cikin tsananin kuka nake maganar wanda ya karyar da zuciyar Kawu na, jikin sa yayi bala'in yin sanyi zuciyar sa tayi mai nauyi, sai yake gani kamar yanzu ne ƙanwar sa ke bashi amanar MUNIBBAT...
Gani yayi shiru baice mun komai, zuciya ta ta sake tsinkewa wajen kayana na nufa, a hankali na tsugona na ɗauka wasu irin hawaye masu zafin gaske suna zubo min, ban sake juyowa na kalle cikin gidan ba murya a sanyaye nace" na tafi Kawu! na gode sosai da soyayyar ka a gareni har abada bazan manta da kai ba, domin kai ne. . .