Ina ƙwance sai k'unk'uni nake ni kad'ai, gaba d'aya haushin wanda yayi min tsawa d'azu ya cika min raina, Anti ta shigo d'akin yafi sau biyar tana min magana akan na tashi nak'i, gajiya tayi ta rabu dani ta kama sabgar gaban ta...
Haka kawai na fashe da wani irin kuka me ƙ'arfin gaske, duk wani mahaluki dake cikin gidan nan sai da yaji kururuwa ta, Anti dake bayi a gigice ta hau saka kayan ta ko kumfar jikin ta bata dauraye ba, Daddah da Big man suma da gudu suka. . .