Skip to content
Part 18 of 26 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Gaskia mun sha yawo sosai, duk dan nayi farin ciki, Alhamdulillahi domin na fara murmushi in na ga abun dariya, shima duk irrin haɗuwar sa da izza sa haka ya mayar da kan shi a waje na tamkar wani sa’ana, sai jana yake da hira ga labarin abun dariya da yake bani,  har yanzu banyi dariya ba sai dai murmushi kawai da nake, muna cikin tafiya danja ta tsada mu, yayi shiru yana tunanin yanda akayi ya sakar min haka…

Ni kam tuni na fara kalle-kalle abu na, irin masu miƙo kayan siyar wanna ne, ya miƙo min sweet da yawa, banyi tunanin komai na na amshe su na zuba kan ciyya ta, AN’NUWAR sam bai kula ba har sai da yaron ya fara magana, gani an kusa bamu hannu, da sauri ya ɗauko kudi a gaban motar yana miƙo min haɗi da cewa” mika masa..”

Haka yayi dai-dai da zuwan Kawu na zai tallaka titin, karf idanun sa ya faɗ’a akai na, a lokaci  kuma na saki wani murmushi, kana na miƙa kud’in cak ya tsaya tsakiyar titi yana kallo na zuciyar sa na halbawa, take tunanin sa ya tafi shi yana nan kullum cikin damuwa da tunanin halin da nake ciki, ni ina can ina farin ciki haɗ’i da mantawa dashi…

Hon aka fara mai ta ko ina sabida an saki hannu, AN’NUWAR ma ya taka ka mota muka wuce, da wani mugun gudu Kawu ya fara bin mu shi bai ma damu da motocin dake masa baraza na ba, gudu yake yana ɗago mana hannu, faɗi yace” ka tsaya!!  MUNIIBAT!! MUNIBBAT!!..” yana gudu  yana haki amma bai fasa kiran suna na ba…

Kamar ance na kalle merro…

Ban gane shi ba amma da alama mu yake tsayar wa, cikin taushin murya nace” an’a maka magana a can!..” yanda nayi maganar ne ina juya hannu abu ya birge shi, kawai sai yayi mun murmushi bai kuma tsaya ba…

Kawu ya dafe kirjin sa da yake masa zafi, cikin haki da gajiyawa ya fara tari! tun yana tsaye har ya durƙusa, ya jima sosai a cikin wannan yanayi…

Cikin damuwa ya dawo dakin, jiki a sanyaye ya ƙwaɓe kayan, daga shi sai gajeran wando ya tsaya, a hankali ya faɗa kan bed dinsa yana me nutsewa cikin katifa, a baiyana yace” me yake damu na ne? ya rabbi!!..” yana me shafo sajan sa..

Daddah ta dubi Anty data haɗa kai da gwiwa, cike da tausayin ta tace” yarinya ta tunanin me kike haka?…”

Cikin basarwa ta ɗago tana yake, Daddah ta zauna kusa da ita sosai, cikin kulawa tace” kina tunanin sauyawar baby ne ko?  me yiwa lokacin baya bata saba da irin kulawar da kuke bata ba, duk yanda akayi tunanin ta yana san dawo mata ne, kuma haka nake fata..”

Da sauri Anty ta dubi daddah idanun ta suka kaɗa, cikin raunaneniyar murya tace” ba wai bana farin ciki ba ne da samun lafiyar ba ne, a’a kawai ina hango yanda zata tafi ta barni, domin zata ji tamkar tashi daga barci ne, Daddah ina ƙaunar baby sosai dan Allah ki taimake ni ta zama mallaki na!!….” tayi maganar hawaye na bin kuncin ta…

Cike da tausayin ta tace” haƙuri zakiyi nusaiba insha Allahu kema zaki samu naki, ni a yanzu bani da iko kan yarinyar nan, maganar da nake miki duk wannan jimawar da tayi damu, har yanzu mahaifin ta bai fitar da rai da ita ba, kullum kwanan duniya sai yaje neman ta, hakiƙa yafiki son ta da ƙaunar ta, da kin sa  irin soyayyar dake tsakanin ta da Kawun ta, da baza kiyi  sha’awar raba su ba, ki duba ki gani sabida shaƙuwa da amanar ƙauna sunan shi yaki fita a bakin ta kasancewar ta me taɓin hankali, hakan bai yana ta tunanin sa ba! a ta dalilin rashin ta a kusa dashi, ya mayar da kanshi tamkar wani zarare, ya ajiye aikin sa me mahimaci ya zauna zaman jiran ta, karki sake ki shiga tsakanin su, muddin MUNIBBAT TA dawo haiyyacin ta nayi alƙawari sa hannu ‘na zan ɗanƙamai yarinyar sa, kana ‘na saka an’nuwar ya durƙusa ya bashi haƙuri, alƙawari nayi wa kai na ki cire ta a ranki tun wuri!!…”

Cikin kuka tace” hajiya dama kin san wacece ita? me yasa kika boye min? meyasa zakice na cireta a raina? sanin kan ki ne soyayyar da nake mata daga Allah nee! zanyi ƙoƙari nayi biyayya a gareki, amma bana jin har abada zan iya manta ta a rayuwa ta, a lokacin da kika mayar da ita ga danginta nima zan sake neman alfarmar sa akan ya bani ita zanyi masa alƙawarin abunda zanyi, dan Allah Hajiya karki hanani wallahi nima ina mata son so!…” cikin kuka take maganar..

MAN da tun dazu yana tsaye kuma yana jin su, ya ƙaraso cikin falo fuskar shi cike da tausayin Anty, ya zaune can kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace” Anty!! ba laifin Daddah bane! nine na hana a faɗawa kowa ko ita wacece, ita din ɗaliba tace! na san ta na san iyayen ta… daga nan ya ƙwashe labarin ta da yasani kaf ya faɗa mata, saboda tsananin tausayin ta  Anty kasa cewa komai tayi, ga tsanar matar Kawu da take ji har cikin ranta, a hankali tace” kinyi gaskiya Hajiya, dama kince halan a rayuwa ta ta baya bata saba da irin kulawar da muke bata ba a yanzu,  ina neman alfarma a gare ku dan girman Allah ko da ace ta warke ku bar min ita na wani lokaci, ina so ta san cewa mu masoyan ta ne kafin ta barmu!?..” ta ƙarke maganar cikin rauni…

Daddah za tayi magana MAN yayi mata alama da ido kan tayi shiru, cikin girmamawa ya kamo hannun Anty muryasa a tausashe yace” akan wannan ne kike zubar da hawayen ki ANTY!? nayi miki alƙawari ni da kai na zan roƙa miki Kawu ya bar miki baby haka yayi miki?..”

Duk da jikin ta ya mutu  haka bai hana ta sakar mai murmushi ba, a hankula tace” Allah yayi maka albarka yaro na!, dako har abada bazan mata da wanna ba!..”

Shigowar mu ne ya k’atse musu zance, da murna ta na shigo AN’NUWAR na biye dani a baya kaya niƙi-niƙi, kai tsaye jikin Anty na tafi na zaune ina nuna mata sweet din na, kallo na take cike da tausayi na tana min murmushi dole..

Daddah ta ƙarewa AN’NUWAR kallo cike da jin haushin sa tace” da izzinin wa  ka fitar min da yarinya?..”

Sororo yayi yana duban ta zuciyar sa babu dadi a dame yace” au sai an nemin izzini sannan za’a fata ita? a taunani na taimaka ta nayi..”

” To marar kunya rasa kunya beran tanka, wanda yayi gadon wahala, wallahi ko kusa ku alama kar na sake ganin ka da ita, wani yace maka tana buƙatar taimako? Lokacin da take buƙatar taimako ya wuce ai, daka gudu a tunanin ka ai zaje ka dawo ka tarar ta mutu, wato yanzu kaga  taza ma mutun shine zaka lalaɓo ka sake gigita musu yarinyar ko? to hawainiyar ka ta kiyayye ramata wallahi ka fita a ido na tun wuri! tunda uwar ka ta daure maka gindi sai kaje kayi iskacin ka akan wasa ƴan amma ba wannan ba kaji ni ko?…” Cike da masifa take maganar..

AN’NUWAR ranshi ya soso sosai da maganar ta, ya dube ta ranshi a bace bashi da yanda zan iya dole yace” Allah ya huci zuciyar ki Daddah, insha Allah zan kiyayye Allah ya bata lafiya..”

yana rufe bakin sa yayi saurin juye wa zaifice a ɗ’akin..

Da sauri Daddah tace” ameen in da zuciya ɗaya ka faɗ’a magulmaci…”

Man har zuciyar sa baiji dadin abunda Daddah tayi ma ɗan uwan sa ba, haka ma Anty amma basu da ikon magana, tsinkayo muryata  sukayi ina cewa” Kawu na! yau ma na ganka!..” sai na saki dariya me sauti…

A wani hautsine suka mayar da duban su gareni, kawai sai suka ga ina nuno MAN da yatsa, ANTY ta sauke a jiyar zuciya, Daddah ta shafa min fuska game da cewa” Allah ya baki lafiya baby!..”

Ameen suka amsa dashi ni kuma na cigaba da bare sweet dinna ina tarawa…

Duk wani abu me saukin ɗauka, Kawu in yaci karo dashi a ɗakin watsi yake dashi, cikin mutuƙar tashin hankali da ruɗani yana hawaye da sumbato, yake watsu da kayan ɗakin,   Anty na, ta haukace ta firgice, cikin mutuƙar ruɗewa take cewa” dan girman Allah, Abban Hanna ka tsaya ka saurareni, kayi haƙ’uri ka sawa zuciyar ka salama, MUNIBBAT dinka zata dawo a ko wanne lokaci, wannan haukar da kake bazai amfana maka da komai sai tarin nadama…”

Cak ya tsaya yana duban ta zuciyar sa na tafasa, a mutuƙar harzuƙe ya shaƙe mata wuya kana ya buga ta a jikin bango ɗ’akin haɗin ya sake shake ta da kyau, idanun sa jawur yace” munafika ladama ta nawa kike so nayi? duk uban waye yajawo wanna wahalar? duk abinda ya faru kece sanadi! kin cuce ni SHAFA’ATU kin saka na aikata babban ƙuskure, yau da idanun na naga MUNIBBAT a cikin mota…” ya wugar da ita gefe guda ranshi babu dadi ya ɗaura.

 dace”  kullum bana iya barci  sabida ita! walwala ta farin ciki na, kullum cikin tunanin ta nake, dai² da sa’a ɗaya ban taɓa mantawa da ita a cikin gidanan ba, na ajiye komai domin ta, amma abun bakin cikin shine ita ta manta dani ta manta ko ni waye! bata tunanin na, naji na aikata ƙusƙure amma me yasa zatayi min haka? da idanuna nagan ta tana dariya a gaban mota, ni gani rabo na dana dara har na manta kuma duk sabida ita, Ashe wahalar bazan nake…!”

Ya juya wajen Anty dake yashe a ƙasa tana aikin tari da murza wuya, tana ganin shi ta shiga ja  da baya tana zare ido, cakumo ta yayi yana mata wani irin kallo a hautsine yace” duk kece kika kulla komai! me yasa ma nake zaune dake har yanzu?…”

Wanna furicin da yayi shi yasa Anty sakin wani fitsari me zafin gaske, jikin ta ya dauki rawa…

Tsananin firgici, da ruɗani shine ya baiyyana akan fuskar ta, jikin ta tamkar ana kaɗata da majajawa, hannun ta na rawa ta miƙe cikin tashin hankali tana mai wani irin kallo me cike da alamomin tambaya, cikin sauri Kawu ya juya mata baya haɗi da share ƙwallar sa, a hankali tazo ta bayan nasa ta rungume shi ramm, tana wani irin kuka kamar ranta zai fita a gangar jikin ta…

” Dan girman Allah kaji tausayi na! kar ka mayar dani bazawa! kayi haƙuri Abban Hanna…?”  cikin wani irin yanayi tayi maganar…

To kun dai sai halin maza, musamma Kawu da ya ɗauki watani ba tare da yaji shi a duniyar wata ba…

Shasheƙar da take mai a bayan kunne shi ya haifar mai da wata muguwar kasala, take wani baƙon lamari ya ratsashi, cikin dakewa ya fara ƙoƙari rabata da jikin sa nan fa suka hau kokawa, yana ɗagowa da nufi yi mata masifa tayi saurin cefke mai…

*******

Washe Gari…

Da sasafe MAN ya fito domin yau yake sa ran haɗu wa da Kawu na, waje daddah ya fara zuwa bayan tayi masa Addu’a, ya wuto nan shashin mu a sa ilin Anty ta gyara ni duk da ba wata ƙwalliya tayi mun ba amma nayi mutuƙar yin kyau a cikin wani pink din material ɗinki ya amshi jikina sosai, ta ɗauko blue din hide ta ɗaura min, gaskiya na haɗu iya haɗuwa ta sakani a gaba sai addu’a take tofa min wai maganin baki, ni kam ina zaune kamar an dasani sai wasa nake da teddy ban ma damu da miyan da take tofa min ba…

A hankali MAN ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama, sun gaisa da ANTY kamar yanda suka saba, daga bisani ya fara tsokana ta, har ya juya zai wuce nayi saurin bin bayan sa bai kula dani ba sai da ya kai ƙofar fita ya juyo, aiko mu kayi karo dashi…

A razane nayi baya zan faɗ’i, inda shi kuma ya dafe goshin sa da hannun sa, na gama sadaƙarwa na kai kasa ga mamaki na sai jina nayi a jikin mutun, aiko tsoro yasa na ƙan-ƙame shi…

MAN ya ɓata fuska cike da jin haushin ƙannasa yace” AN’NUWAR!! kana da hankali kuwa? kalle fa yanda ka anagizani!…”

A hankali ya gyara min tsewa ta cikin halin ko in kula yace” kai baka ganin baby na! zata sha kasa!!! salon ka sake ja mana zagi a wajen tsohowar can, ai gara kai ka faɗi akan ita…” tunda ya fara maganar bai kalle inda Man yake ba, ni din dai ni yake kallo…

Ina gama watsakewa nayi saurin koma inda man yake cikin turo baki nace” ni sai na bika!..”

Ɗauke idanun sa yayi akan AN’NU  yana sauke su akai na, zaiyi magana nayi saurin komawa ta gaban sa ina me ƙifƙiffta  zara-zaran idanuna, cike da shagwaɓa nace” ni dai zan bika!…”

AN’NUWAR yayi sauri zuwa inda nake cikin taushin murya yace” Baby ki kyale MAN yayi tafiyar sa, muma zuwa anjima sai muje yawo ko?…”

” _lallai ma yaron nan wato dan ƙwana biyu ina sakar mai shine har ya samu damar zuwa gaba na yana cewa wai ta kyale ni, kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi kenan tabdi…”_  Duk a zuci yayi maganar nan..

Cikin sauri ya kamo ƙuguna yana me jana ɗaya gefen yace” dama ai dake zai wuce..”

ko kallon inda ANNUWAR yake bai sake ba ya jani muka fice…

Anty dake zauna akan kujera tana kallon abunda ya faru, ta ɗanne dariyar ta a fili kuma tana  baiyyana murmushin ta har cikin zuciyar ta yau bata so taga nayi mata nisa amma sabida farin cikina shi yasa bata hanni ba…

Sai bayan mun fito kuma, ya fara tunanin inda zai ajiye ni, yaje ya dawo ba tare da ana samu matsala ba,  dabara ce ta faɗo mai kawai sai ya saki murmushi, bai zarce ko ina ba sai gidan mu…

Bamu ɗauki wani lokaci ba muka isa, shi kaɗai ya fita a bakin ƙofa ya tsaya, yayi sallama ta ciki aka amsa mai, kana ya dawo cikin mota ya zauna, kaffe ni yayi da idanu babu ko kifftawa a hankali ya kamo hannu ‘na cike da sha’uƙi yace” kina so ‘na!!??…” cikin taushi da ƙauna yayi maganar..

Murmushi nayi masa cikin alamon jin dadi nace” a… Fitowar kawu na ya dakatar dani…

Jim kaɗan sai ga Kawu na ya fito, cikin sakin fuska suka gaisa da MAN, gani maganar me mahimmaci ce yasa Kawu ya koma ciki, sai gashi da abun zama…

To kamar dai yanda suka tsara komai shi da daddah haka ya ƙwashe komai ya faɗawa Kawu na, inda a ƙarshe ya daurawa da cewa” yarinyar tana tsananin ƙaunar ka, duk da tana cikin wani hali hakan bai sa ta manta da sunan ka ba, likitoci sun sheda mana muddin muna so ta warke cikin sauki, lallai sai mun nuna mata abun da tafi so a rayuwar ta, shine Daddah ta aiko ni gareka akan ‘na faɗa maka komai ko zuciyarka zata samu salama,  tunda muke da ita bata taɓa nuna wata alama tajin sauƙiba har sai ranar dana zo da ita nan ta ganka, a ranar ‘na sheda kai na farin cikin ta…

Kawu a yanzu muna buƙatar taimakon ka ne, ba kuka ba, kayi haƙuri ba muzo maka da wuri ba hakan ya faru ne sabida wata matsala da aka samu, mun sha wuya sosai kafin mu gano nan din, amma da tare zamuyi jinyar ta, a madadin ɗan uwana da iyaye ‘na ina me baka haƙuri akan hakan!…”

Na gaji sosai da zaman  motar ganin har yanzu shiru bai dawo ba, sai na fata taɓe-tabe a cikin motar cikin sa’a ‘na bude murfin motar, a hankali na zuro ƙafa ta ɗaya na jima a haka ina kallon inda ya shiga….

 Har lokacin Kawu ‘na hawaye yake zubar, na tsananin tausayi ‘na tabbas yasan duk wuya duk rintsi bazan manta dashi cikin sauƙi haka ba, ya kasa cewa komai sai aikin share ƙwalla yake…

<< Waye Zabin Munibat? 17Waye Zabin Munibat? 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×