Ko da nazo bakin ƙofar sai na tsaya, ina leƙwa a hankali kuma ‘na sako ƙafata ɗaya, tunanin ‘na fara amma ba wai can ba, tun daga ranar da Kawu na yayi fushi dani har zuwa ranar da ya koreni har lokacin sa mota ta makeni, bana iya tunawa sosai ɗishi-ɗishi nake gani a haka ‘na shigo zauren gaba ɗaya ina dafe bango…
Gaba ɗayan su miƙewa sukayi tsaye, MAN yana tsakanin mamakin yanda akayi ‘na iya buɗe motar, inda Kawu ‘na! yake mun wani irin kallo nayi ƙewarki jikin sa ‘narawa hawaye ba gudu akan ƙuncin sa, ganin zan faɗi suka tahu a tare da nufin taroni, kafin MAN ya kawo hannu Kawu ‘na! yayi saurin ture shi na faɗo jikin sa, idanuna akan sa face din sa…
So nake na tuna shi, amma na gaza gani sosai, cikin rawar baki yace” MUNIBBATU NA!!! kece? dama zan muke haɗuwa? ashe da gaske yake? kece ? Ke kalle ni nan nine nan Kawunki? kin gane ni? ki kalle ni nace karki rufe idanunki sanyin idaniyyata dube ni nace Kawun ki ne kin tunani ? ko zaki manta kowa a’i na san bazaki manta ni ba ki kalle ni nace!!…” ya faɗa da ƙarfi…
Tunda ‘na faɗo jikin sa nara iya gane komai nawa, tun farkon rayuwa ta na fara har zuwa lokacin sa mota ta makeni, cikin ƙaraji nace” Kawu na!!!!….” Take kuma na saki gaba ɗaya ‘na tafi duniyar suma…
Hayaniyyar mu ne ya jawo hankalin Anty ‘na dake ɗaki jin kamar da gaske murya tace ba gizo nake mata ba, zuciyar TA ta buga da karfin gaske, cikin kiɗima tafito zuwa zauren a ruɗe kwance TA same ni shame-shame a jikin Kawu ba na tafi duniyar suma, itama suman tsaye tayi dafe da kirji…
Wani irin tausayin mu ne ya ratsa zuciyar Man dake tsaye akan mu, cikin daure yace” Kawu tana buƙatar ganin likita a yanzu…
*****
Gaba ɗaya a halin gidan suna tsaye bakin ƙofa, ko wanne da kalar tashin hankalin dake kan fuskar sa, Hajiya Nusaiba ta dube MAN cikin alamun karaya tace” me yasa? ya zakayi mun haka? shikenan fa ɗaga yau zata barni!…” sharrr wasu zafaffan hawaye suka biyo kuncin ta…
Daddah tayi saurin dafa ta baya cikin taushin murya tace” bashi da laifi Nusaiba! nice ‘na aika shi! amma bamuyi dashi zai tafi da ita ba…”
AN’NUWAR dake tsaye shima yayi jigum, yana tausayin a halin sa ganin sun shiga damu sabida baby! gaban su yaje ya tsaya cikin nutsuwa yace” kuyi haƙuri na san duk nine silar komai, amma ina da hanyar da baby zata cigaba da zama daku, zama na har abada amincewar ki nake nema Daddah, ya kamo hannun ta ya daura dacewa _a gaban ku zan nemi auren ta a wajen mahaifin ta! fatana ta tashi lafiya…”_
A mutuƙar razane kowa yake duban sa, MAN ya dafe bango da sauri yana fitar da wani nishi marar sauti, Kawu ya kura mai ido zuciyar sa cike da zilumi, ANTY dake sauraron komai take wani bakin ciki ya mamaye mata zuciya cike da tsiwa tace” uban wa ma zai baka auren ta ɗ’aga ganin ka haka sama ta kai! tun ba yau ba mun riga da muyi mata miji, sai dai ka nema a gaba…”
Gaba ɗaya kuma sai kallo ya koma kan ta, shi dai Kawu na bai ce komai ba…
A haka doctor ya fito ya same su kowa yayi jigum-jigum, cikin farin ciki ya mikawa MAN hannu haɗe da cewa” congratulations Aboki na, a yanzu komai ya dawo normal kamar yanda na sha gaya maka, sai mu jira tashin ta mu gani kuma, Allah ya kara lafiya …” jikin MAN a sabule ya amsa da amin…
Dadi kamar ya kashe Kawu na, ai bai jira cewar kowa ba ya faɗ’a ɗakin zuciyar sa kamar zata faso ƙirjin sa saboda dadi, MAN ya rintse idanun sa shikenan ta kubuce mai a karo na farko…
Daddah ta dafo shi cikin muryar ta na manyan taka tace” bana so ka karaya Haidar, har yanzu muna da sauran lokaci…”
” No Daddah komai ya ƙare min yanzu! shikenan ta tafi kenan!…”
Wani kallon tara saura ƙwata ANTY na tayi musu sannan ta biyo bayan Kawu na cikin ɗ’akin da nake, yana zaune jikin gadon da nake ƙwance sai aikin kallo na yake hannu shi cikin nawa, na jima sosai ina barci sabida allurar da akayi min, su MAN ko da wasa babu wanda yayi gigin shigowa ɗakin, suna ɗaga waje amma suna iya gano komai a haka…
Kawu na, ya fito jikin sa sanyayye yace” kuyi haƙ’uri zan so kuzo kuma…” yayi maganar yana nuna musu cikin d’akin kana ya daura da cewa” tana buƙatar ku ita ma…” a hankali ya kamo hannun MAN tunda shi ya fara sani, har gaban gadon ya kawo shi sannan ya juya wajen su Daddah cikin girmamawa yace” Hajiya ban san da wannan irin baki zanyi miki godiya ba na riƙe min marainiyar Allah da kikayi, kin tallafe ta a lokacin da take buƙ’atar taimako, ki mayar da ita mutun a lokacin da take shirin yanke tsammani, kin gatata ki ɗaga darajar ta, a lokacin da take zaton baza ta sake samun wani gata ba, na biyewa sharin zuciya dana shedan na aika babban ƙuskure, na kore ta ɗaga gidana a lokacin da take mutuƙar buƙatar taimako na, na ci amanar yar uwa ta da ta bani amanar ta, nine gatan ta Amma na manta wannan, nafi kowa sanin me zata iya aika tawa amma rashin bincike yasa na rufe idanuna na aika ta babban kusƙure, yanzu da ba dan Allah yasa ta faɗa hannu na gari ba, da ya rayuwar ta zata ƙasance? tun daga ranar da ta bar gabana ƙwanciyar hankalin tayi ƙaura a waje na, kullum burina shine na ganta, kullum zuciya tana begen ta, sai gashi ina zaune an kawo mini ita cikin mutunci har gida, wannan shine karamci kun ƙauna CE ta duk da baku san ko ita WACECE ba, kun nuna mata gata wanda bata taɓa samu a wajen mu ba, niko da me zan saka muku kuji dadi?…”
Cikin sauri Hajiya Nusaiba tace” bama buƙatar komai ɗ’aga gare ka face ka bar mana baby ta zauna wajen mu. ta zab’e a gaban sa muryar ta a rauna ne tace” ka dube girman Allah, kamar yanda Allah ya taimaka ya baka zuri’a lafiya, ilimi, kaji tausayin mu nida yara na ka bar mana baby nayi maka alƙ’awari zan kula maka ita har ƙ’arshe numfashin na!! tabbas na san abu ne me wuya ƙyautar da suƙutunda guda haka, musammma irin baby, na san irin soyayya dake tsakani ka ita na San irin shaƙ’uwar dake tsakanin ku, ba dan ni ba badan halina ba da soyayyar da fiyyen halitta, karka rabani da ita…”” cikin hawaye yanzu take maganar…
Cikin sauri MAN ya ɗago ta ransa a bace yace” me kikeyi haka ne ANTY!!? kina tunanin zai iya baki kyautar MUNIBBAT cikin sauki haka? Daddah ki faɗa mata ta cire ta a ranta, ba gamu ba? mu bamu isheki ba ne ANTY? muma muna ƙaunar ki ko duk wannan bai miki ba? ki ɗaina in da rabon MUNIBBAT ta sake zama tare da ke zata dawo SON…!” a hankali ta rungume MAN cikin kuka tace” zanyi ƙewar ta sosai MAN! Ina jin ta tamkar yar ciki na!!..”
Shima hannun sa ya saka yana share ƙwallar idanun sa cikin juriya yace” nima ina ƙaunar ta ANTY amma ba yanda za muyi, yanzu zata ga abun da mu kayi mata tamkar a mafarki ne, gaba ɗaya mu zamuyi ƙewar ta ne!…” ji yake kamar ya kurma ihu amma sabida ANTY ta ɗai na kuka sai ya daure!!…
Daddah ta kamo hannun AN’NUWAR har gaban Kawu, cikin taushi tace” ka gafarce mu aka abinda jikana yayi muku na bige muku yarinyar cikin gaganci?..” ta faɗa tana haɗ’e hannuwan ta waje guda…
AN’NUWAR yace” kayi haƙuri tsutsayi na da ƙaddara amma nima ba haka na so ba, ka gafarce ni!!..” ya faɗa cikin ladabi…”
Gaba ɗ’aya ji yayi kan shi yayi mai girma, ganin manya mutane suna neman yafiyar sa akan MUNIBBAT ga tsananin soyayyar ta da yake hango wa a cikin tsakiyar idanun su, cikin tausayawa ya ɗago AN’NUWAR fuskar sa a sake yace” Allah ya yafe mana baki ɗaya, ni ya kama ta nayi godiya ba ku ba, na gode sosai Allah ya bar zumunci…”
A hankali suka amsa da ameen…
To abunda basu kula dashi ba, shine tun farkon shigowar su na farka, duk wannan koke-koken da suke akan idanuna su kayi sa, naji komai da ya faru dani kallo ɗaya nayi ma AN’NUWAR da Hajiya na tuno inda na san su, malan Haidar kuma bai juyo ba bare na sheda shi, amma naji murya sa inta kokon to…
Cikin sanyin jiki Daddah ta saka su a gaba akan su tafi gida, har sun kai ƙofa jiki na na rawa nace” Hajiya!!!…”
Gaba ɗayan su juyo wa sukayi kamar ance su rugo inda nake, musamma hajiya nusaiba cikin soyayya ta sunbaci goshi na idanun ta cike da hawaye tana wani shafa min fuska, tace” BABY NA!!! kin gane ni? Nice nice!!..” kuka kan da take ya hana abunda take son faɗa fitowa.
A hankali Dadda ta ɗago ta zuwa jikin ta, cikin nutsuwa tace” shitt!! ya isa haka!!..”
Ƙare musu kallo nayi tass, sannan ‘na kalle Kawu na, haɗi da sakar mai tausasan murmushi, a hankali nace” ina san ka sanyin idaniyata!..”
Shi ma martanin murmushi ya mayar min, daga bisa ni yace” Hajiya ‘in babu damuwa ina son magana dake?..”
” BISMILLAH!..” cewar Daddah.. Waje suka fita ni kuma aka barni da jama’a ta har yanzu MAN bai waigo ba, tunda na kalle ANNUWAR sau ɗaya ban sake gigin kallon sa ba, hankali na gaba d’aya yana wajen Hajiya Nusaiba, da take ta ƙoƙari ganin na tuna su…
(Kun dai san manta komai nata tayi, ba wai haukacewa tayi ba, duk abinda kayi mata zata iya rikewa, haka zata iya tunawa ko da memory dinta ya samu lafiya, musamma ita tunda tana da kayefin tunanin, zata na ganine tamkar a mafarki tayi wata rayuwar daban…)
Cikin gajiyawa nace” Kiyi haƙuri Hajiya, nima yau na fara ganin ku!..”
Maganar ce ta daki zuciyar ANTY cikin sauri tayi baya, MAN yayi saurin tare ta, haushi ya kama ANNUWAR…
” HAJIYA zan so na bar muku ita a hannun ku, ni kai na sai zuciyata sai tafi nutsuwa da hakan, amma ina jin tsoro sosai da yanayi da take ciki, ki ƙwantar musu da hankali insha Allah nan ba da jimawa ba zan dawo muku da ita, zanyi ƙoƙari sosai na ganin bata manta da ku ba, kuyi haƙ’uri dan Allah ku bar min ita nima na samu nutsuwa, zata dawo muku cikin sauki…”
Kallo mutuntawa Hajiya Daddah tayi masa cikin jin dadi da tausayi sa tace” haƙiƙa naji dadi furicin ka sosai, Allah ya saka da alhairi, amma abinda nake so da kai shine, karka taƙura kan ka abinda bakayi niyya ba, na san yanda kake ƙaunar ƴarka, ita ma tana ƙ’aunar mahaifin ta, muna san muga MUNIBBAT a cikin farin ciki, me ɗaurewa kullum ƙwanan duniya addu’ar da muke mata kenan, Allah ya amsa kuma mun gode masa, duk cikin mu babu wanda zai so ya raba ta da abinda take so, a yanzu babu wanda tafi ƙaunar gani da san zama dashi sama da kai! kana tunanin zamu so wannan farin cikin nata ya rushe? a’a baza mu zama masu san kan mu ba gaskiya, zan so ka bar ta a wajen ka duk lokacin da ta bukaci ganin mu, insha Allah zata gan mu, kamar yanda muke kula da ita a wajen mu, baza mu canza ba insha Allah mun gode sosai Allah ya bar zumuci, ka ci gaba da riƙe amana tabbas zakaga ribar hakan, Allah ya tsare gaba mun gode…”
Jikin sa yayi mutukar yin sanyi, ko magana ma ya gagara…
Har yanzu ban ga fuskar mal Haidar ba, a haka ya fice da Anty tana kallo na hawaye na bin kuncin ta, ANNUWAR na bin bayan su, a waje suka tarar da Daddah daga nan su kayi sallama da Kawu suka fice a asibitin gaba ɗaya…
Gaskiya na yarda ni ƴar gata ce a wajen Kawu na, duk inda na motsa sai ya tambaye lafiya ta, abun gwanin ban sha’awa zuwa dare aka sallame mu muka dawo gida, babu wanda baiyi mamaki ba gani a gyara gidan fas dashi, musamma ɗaki na a zuba mun wasa manya kayan ɗaki masu bala’in kyau da tsari, tamkar ba gidan mu ba, gaskiya ana ƙawata abun sosai, dadi ya kamani sai tsalle nake ina murna, cikin jin dadi nace” Kawu duk wannan nawa ne ni kaɗ’ai?..”
Shima murmushi ƙarfin hali yayi min haɗi da cewa” eh mana yar gidan Kawu, duk dan kiyi farin ciki ne ai…”
Ko da na bude cikin siff din kaya ne masu yawan gaske da tsada, komai ana zuba min a ciki ina can ina shirme na na jin dadi, Kawu na ya ɗauki wata farar takarda da aka ɗ’anne ta da ƙwalin wata danƙ’areriyar waya, bai bari na gani ba yayi saurin ficewa a ɗ’akin…
To kamar yanda aka saka min wannan kayan a ɗaki na, haka ma ɗakin matar Kawu na ya kasance, amma fa bai kai nawa kyau ba gaskiya, sai murna take ganin ta samu gani ma…
Can zaure ya tsaya, sosai ya fahimci me ake nufi da saƙon, ya jima sosai yana tunanin aciki su waye yayi wannan aikin, amma ya kasa fahimta, a ƙ’arshe rubutun ana rubuta (A&M) me ya hakan yake nufi to? iya tunanin sa yayi amma ya gaza ganewa dole ya haƙuri ya dawo cikin gida jikin sa a sanyaye…
Kimanin sati biyu kenan yanzu da dawo ta cikin ahali na, bana fuskar wata damuwa a ko wanne ɓangare, rayuwa ta nake kamar yanda na faro ta tun farko, har yanzu Kawu na bai koma wajen aikin sa, gashi kusan kullum yana bani labarin rayuwar da nayi a wani gida, da irin soyayyar da ake min, amma fa har yau baice min ni bace, abinda yake ɗaure min kai ma shine a duk lokacin da muka zaune hira dashi, da ya fara bani labari naji ya faɗ’i abinda babu shi, zance ba haka bane kaza ne, na kayi mamaki ina zauna ni kaɗai na fara tuna rayuwar da nayi a baya, sai nake gani tamkar mafarki nakeyi…