Bismillahir Rahmanir Rahim
Washe gari da sasafe, sai ga Aysha ta shigo gidan mu fuskar ta cike murmushi, lokaci ina d'urk'ushe a gidin murho ina fama da itace yak'i kamawa, cikin murna na taso hannun ta na kama na jata zuwa bakin zauren gida mu, murya ta k'asa-k'asa nace" lafiya Aysha na ganki a irin wannan lokacin…?" na fad'a ina waigawa baya na tamkar b'arauniya.
Har yanzu murmushin ta bai gushe a kan fuskar ta ba, tace" matsoraciya kawai, zuwa nayi nayi miki albushir Monday in Allah ya kai mu tare zamu. . .