Tunda daga ranar da na bar gidan, shikenan komai nasu yayi sanyi, ANTY bata cika fitowa ba ko da yaushe tana cikin ɗ'akin ta a ƙwance, gaba ɗaya damuwa tayi mata yawa, kullum tunanin halin da nake ciki takeyi, Daddah tayi faɗan har ta gaji amma shiru babu sauyi...
Tabbas bari na gida tamkar rushewar wani reshe ne na gidan, MAN bai taɓa sanin san da yake min ya kai har haka ba, kullum bai da aiki sai tunani na komai yake baby! duk abinda yake duba sai baby! koyar wa ma ta gagare shi duk dan. . .